Ko kun san:- Groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin ɗan adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Soyayyar gyaɗa ¼ cup
- Dankalin hausa matsakaita
- Albasa a yanka ƙanana ko a jajjaga
- Curry ½ tablespoon
- Markaɗaɗɗen nama
- Sinadarin ɗanɗano
- Attaruhu guda biyar jajjagge
- Tafarnuwa
- Breadcrumbs 1 cup
- Ƙwai 3 (a fasa a kaɗashi)
- Man gyaɗa na suya
Yadda Ake Haɗawa
- A cikin kwano mai ƙyau a zuba dafaffiyar dankali sai a farfasata su fasu da kyau.
- Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin ɗanɗano, curry, thyme da nama a juya a hankali.
- A samu ɗan faranti a ringa ɗiban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye.
A tsoma wannan ball cikin ƙwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe.
Domin sanin Yadda Ake Donut danna nan