A yau za mu koyi yadda ake gas meat.
Abubuwan Da Ake Buƙata:
- Jan nama
- Albasa ko lawashi
- Markaɗaɗɗiyar gyaɗa
- Kori
- Thyme
- Tattara
- Attaruhu
- Tumatur kaɗan
- Maggi
- Kabeji
- Tafarnuwa
- Foil paper ko takardan cementi
- Da leda baƙi
Yadda Ake Haɗawa
- A wanke nama.
- A yanka albasa ko lawashi.
- A jajjaga tattara da attaruhu.
- A yayyanka tumatur.
- A haɗa nama, albasa, da kayan miya, da gyaɗa, kori, thyme, maggi da sauran kayan ƙamshi a gauraya, idan ana so a sa tumatur ko kuma a bar shi sai bayan kori ya nuna a zuba shi ɗanye a kan naman a ci.
- A juye haɗin baki ɗaya a cikin foil paper a kunshe ko kuma a leda, sai a sa ledar a cikin takarda, takardan kuwa a cikin wani leda.
- A ɗora tukunya da ruwa, idan ya yi zafi ko ya tafasa a dora matsami kamar za a yi dahuwar dambu, a dora ƙunshi a kai a rufe da marfin tukunya a bari ya nuna.
- Idan ya nuna za a iya garnishing da cabbage, tumatur, koren tatttasai a ci.
- Za a iya kuma amfani da oven in da hali ba dole sai tukunya ba.
Domin sanin Yadda Ake Stuffed Meat danna nan