Abubuwan da ake buƙata:
- Kaza ko Nama
- Shinkafa
- Kayan ƙamshi
- Mai ɗanɗano
- Masara
- Tafarnuwa
- Citta
- Albasa
- Cinammon
- Persley
- kayan miya
- Koren tattasai
Yadda ake haɗawa
- Za a sami nama ko kifi, idan nama ne, yana buƙatar a dafa shi kamar awa ɗaya yadda zai yi laushi sosai.
- Idan kifi ne, za a wanke, a sa masa sinadarai sai a sa shi a tukunya, a ba shi wuta kaɗan, dan su shiga jikinsa, amman kar a sa ruwa.
- Sai a zuba markaɗaɗɗen kayan miya, amman ba da yawa ba.
- A kawo ɗan mai kaɗan shima a zuba, a soya sama-sama, kar ya soyu sosai.
- Sannan a kawo ruwa da ɗan dama a zuba, da sinadaran ƙamshi, amman ba masu yawa ba.
- A wanke shinkafa a zuba, idan ya tafasa a zuba nama da ruwan naman, ana son aƙalla shinkafar ta yi awa ɗaya dan ta samu ta farfashe tunda romonta ake so. Idan anga ta yi kauri, sai a kawo kayan mai ɗanɗano da cinnamon a zuba, a rage wuta, idan kuma da kifi ake yi to sai a zuba.
- Sannan a yanka koren tattasai da parsley da albasa a zuba a bar shi ya yi kamar minti 2 sai ki sauke.
Domin sanin yadda ake pancake danna nan