Barkanmu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa; A yau za mu koyi yadda ake farfesun ganda. Tare da ni Hafsat Shettima.
Abubuwan da ake buƙata:
- Ganda
- Jajjagaggiyar albasa matsakaita 2
- Tumatir Jajjagaggen matsakaita 2
- Jajjagaggen Attaruhu (to taste)
- Tattasai Jajjagaggen madaidaita 2
- Sinadarin ɗanɗano (Maggi, Knorr, onga, etc.)
- Sinadarin ƙamshi (Garlic, gyadar miya, curry, etc)
- Ruwa kofi 3 da rabi
Yadda ake haɗawa:
- Asa ganda cikin pressure cooker a dafa, har sai ta yi laushi.
- Cikin tukunya mai zurfi, a sa ganda da kayan ƙamshi, da markaɗaɗɗen kayan miya da saura kayan ɗanɗano kofi biyu ruwa.
- Idan ya dahu sai a saka, a ɗan bar shi kamar minti 4-5 sai a sauke.
- Za a iya ci da French bread ko kuma as starter. Wannan shi ne yadda ake farfesun ganda.
Domin koyan Yadda ake danderun nama sabon salo danna wannan koren rubutun