Dashishi abincin ne da ake yin sa daga alkama. Dashishi abincin gargajiya ne a Arewacin Nijeriya, yana da matuƙar lafiya a jiki, musamman ma a wajen masu ciwon siga kasancewar alkama na ɗaya daga cikin abincin masu ciwon siga.
Abubuwan da ake buƙata:
- Alkama
- Gishiri
- Mai
- Albasa
Yadda ake haɗawa
- A wanke alkama sosai, a fitar da dukkan harkakinta.
- Sai a surfa ta, watau a cire dusar alkamar, sai a bakace a wanke a sake shanyawa.
- Idan ta bushe sai a ɓarza ta, sai a ɗaura tukunya da madambaci sai a shimfiɗa buhu mai kyau, wanda aka wanke shi, amma fa buhun mai shara-shara.
- Wanke alkamar a tsane ta sosai, a zuba a cikin wannan buhun da aka shimfiɗa a cikin tukunyar.
- Sai a rufe da faifai a bar shi ya yi kamar 20mnts.
- Sai a sauke a wanke shi bayan an wanke, sai a yi mashi hadi a sa gishiri da albasa da mai idan dashishi da miya ce, sai a maida a tukunya ya ƙarasa dahuwa, za a iya ƙara masa 15-20mnts za a ji ma yana ƙamshi, sai a sauke ya yi, sai ci.
Domin karanta Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal danna nan.