Danbun masara wani abinci ne na Hausawa wanda ake yi da masara. Kuma masara tana daga cikin nau’in abincin da yake ƙara ƙarfi a jiki.
Kayan Haɗin Danbun Masara
Tsakin masara
Mai
Alayyahu ko Cabbage da karas
Abin ɗanɗano
Albasa da Attaruhu
Yadda za a Haɗa Danbun Masara
A samu madambaci (steamer) a zuba ruwa a ƙasansa, sai a ɗora ruwan a wuta, sai a wanke tsakin masarar sosai, a tsane a mararraki, a sa buhu a saman madambacin, a juye tsakin masara a ciki, a bar shi ya turara kamar awa 1. A kwashe tsakin a faranti a kawo ruwa a yayyafa masa, a saka yankakkiyar albasa da attaruhu da abin ɗanɗano. A sa alayyahu ko carbbage da karas yankakku daidai misali, a mayar da shi wuta, a dinga yayyafa masa ruwa a kai a kai, har sai ya turara sosai, sannan a sauke. Za a iya ci da V.I.P ko da Farfesun kifi da muka yi a baya.
Domin karanta cikakken bayani a kan yadda Ake Burabusko danna nan