Yadda Ɗabi’un Annabi (S.A.W) Suke

0
1248

 Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai yawan murmushi da sakin fuska. Wani lokaci yakan yi dariya, har haqoransa na gaba ko wushiryasa ta bayyana.

Idan ya yi fushi jijiyar fuskarsa takan kumbura da jini. Amma fa baya yin fushi domin an cuce shi, sai domin an saɓa wa Allah. Ya kasance mai nutsuwa da yawan zurfafa tunani. Ba shi da yawan wasa da kakaci koda dai yakan yi barkwanci (ko abin da ake kira zolaya), a wasu lokutan. Idan zai yi Magana yakan yi ta filla-filla, yadda kowa zai gane abin da yake nufi. Kalmominsa ‘yan kaɗan sukan ƙunshi bayani masu yawa. Wannan shi ake kira (kalmomi ‘yan kaɗan, waɗanda suka ƙunshi abubuwa masu yawa).

Ya kasance yana da son ƙamshi, ba ya son wari ko kaɗan. Yana da son yin abubuwa da dama. Kamar taje kai da sanya takallmi da yayin yin wanka da dukkanin al’amuransa5. Yakan yi tafiya da takalmi, wani lokaci ba sai da takalmi ba. Yana yin tafiya cikin sauri, tare da ɗaga kan tudu. Idan zai yi waiwaye yakan juya da jikinnsa gabaɗaya.

Annabi Muhammad (S.A.W) ya kasance yakan yi zaman haɗe jiki. Watau yakan zauna cinyarsa a haɗe da cikinsa, alhali ya sa hannayensa ya haɗo qafafuwansa. A wasu lokutan akan ga ya yi rigingine, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya. Ya kasance idan zai ci abinci yakan ci a durqushe. Yana ci da ‘yan yatsu uku. Musamman abincin da zai ciwu a haka. Kamar dabino da gurasa da sauransu.

Idan zai sha ruwa ba ya yin numfashi a cikin mazubin, kuma yana sha a zaune. Kodayake a wasu lokuta a kan ga sha ruwa a tsaye. Ya zo a cikin As Shama’lun Nabawiyya cewa, Annabi Muhammad (S.A.W) yana da son koren abu. Kuma ya fi son na ƙafafuwan ƙaramar dabba.

Bai taɓa yin kwana uku yana ƙoshi da gurasar alkama ba. Ya fi cin gurasar sha’ir. Mu sani cewa shi sha’ir kamar alkama ya ke. Bai taɓa cin gurasar da romo ba har ya bar duniya. Watau sai dai da mai. Idan ya isa gidan mutane yakan tsaya a gefen dama na ƙorar gidan, ya yi sallama. Ya kasance idan zai kwanta yakan ɗora kansa a kan hannunnsa na dama, ya ambaci Allah, sannan ya yi bacci.

Daga ka’abun bin Malik (RA) ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance fuskarsa takan zama kamar wani yanki ne na farin wata, idan yana farin ciki” (Bukhari ne ya ruwaito).

“Daga Aliyyu (RA) ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan yana tafiya, yakan yi ta cikin sauri da ɗaga ƙafa, kamar yana gangarowa daga tudu”, (Tirmizi ne ya ruwaito).

Amma idan yana yin tafiya tare da sahabbansa yakan sa su a gaba. Yakan ce: “Ku bar bayana domin mala’iku”.

Idan Annabi Muhammad (S.A.W) ya isa wurin taron jama’a, yakan zauna a ƙarshen duk inda ya iske da wuri. Ba ya tashin wani ya zauna a wurinsa. Idan mutum yana Magana da shi yakan saurare shi, ya bashi hankalinsa, sai ya gama. Ba ya yin mugun baki (watau Magana marar kyau). Ba ya la’ana. Ba ya ɗaga murya a kasuwa (S.A.W).

Ya kasance yana da kau da kai. Ba ya saka mummuna da mummuna. Kamar yadda muka faɗa a baya, ba ya yarda mutane su rufe masa baya idan yana tafiya. Ba ya nuna fifiko a kan bayinsa da masu yi masa hidima. Bai taɓa zargin wanda yake yi masa hidima ba.

Yana rama hidima ga wanda ya yi masa. Wata rana yana halin tafiya tare da mutane, sai aka buƙaci  yanka akuya da gyara ta.. Sai wani daga cikinsu y ace: “Ni zan yanka”, wani ya ce,Nizan feɗe, wani ya ce: “Ni zan dafa” “Sai shi kuma ya ce:”Ni zan debo ƙirare” “Sai suka ce: “Ka bari mu za muyi”. Sai ya ce: “Ba na son na fifita a tsakaninku. Allah yana ƙin bawansa idan ya ga yana fifituwa a tsakanin mutanensa”. Sai ya je ya yiwo ƙiraren.

Majalisin Annabi Muhammad (S.A.W), majalisi ne na nutsuwa da ladabi da aminci da girmama juna. Annabi Muhammad (S.A.W) yana da mutuƙar nutsuwa da kwarjini a majalisin sa. Bay a yin Magana saida buƙata.. Idan yana yin Magana duk sahabbansa sukan yi tsit, su sunkuyar da kawunansu, kai ka ce tsuntsaye  ne a kawunan nasu. Ba sa yin  musu ko jayayya a tsakaninsu. Duk wanda ya zo ya tambaye shi wata buƙata ba ya barinsa ya tafi sai ya biya masa ita, ko ya yi masa Magana mai daɗi, ta haƙurƙurtarwa.

Ya kasance ya na haɗa kan sahabbansa. Ba ya barin duk abinda zai raba tsakaninsu. Yana tambayar lafiyar duk wanda bai gani ba daga cikinsu. Idan wani ya yi abu mai kyau yana yaba masa, kamar yaddaa idan wani ya yi abu marar kyau yakan kwaɓe shi. Wani lokaci kuma yakan kawar da kansa idan ya ji wata Magana marar kyau ko wani abu marar kyau, domin su gane sun yi ba daidai ba.

Yana tambayar sahabbansa halin da jama’ar gari suke ciki. Yana girmama shugaban kowace ƙabila ko dangi. Idan ya fara Magana daga ciki sahabbansa sukan dakata, sai ya gama, sannan wani ya fara tasa6.

Annabi Muhammad (S.A.W) yana zuwa duba marar lafiya,, ba tare da duban matsayinsa ba. Shi yake sallatar jana’iza ya bi ta har ƙabarinta. Ba ya raina gayyata ga duk wanda ya gayyace shi gidansa, ko da kuwa mace ce ko yaro.

Domin samun cikkakken bayani akan Yadda Siffar Jikin Annabi (S.A.W) Take: danna koren rubutu

labarin da ya wuceYadda Siffar Jikin Annabi (S.A.W) Take:
Labarin na GabaYadda Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya Suke
Dr. Yahaya Tanko
A yanzu Dr. Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar Dukawuya FCE. A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki. Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.