Warin Baki (Mouth Odour)

1
237

Warin baki, abu ne me wuyar faɗi ga aboki ko wani da ake jin nauyinsa, to sai dai dole a kwana a tashi mutum zai san yana da shi. Akwai lokutan da dole akan ɗan ji baki ya canza wanda canjin ka iya zama normal musamman in ana azumi ko an jima ba a sa komai a baki ba.

Toh sai dai in warin ya zamto kodayaushe a kai-a kai da har ya kai yana hana mutum sakewa, toh mahimmin abu shi ne a yi ƙokarin gano abinda ke haddasa hakan sai a magance shi domin ta haka ne za a iya rabuwa da matsalar.

Wasu lokutan ba rashin brush ba ne ko rashin tsafta ba ne kurum kamar yadda mutane kan ɗauka.

Abubuwan Da Suke Kawo Warin Baki

(1) Daɗaɗɗiyar cutar ulcer, in mutum ya jima ɗauke da ulcer ba tare da magance ta ba, hakan na sa warin baki ko numfashi wanda ke tasowa daga can cikin uwar hanji tunda gyambo ne dama, shi yasa akan kira ta da gyambon ciki tunda ko gyambon da ke waje yakan yi wari ballantana na can ciki,  wurin da iska ba ta ratsawa.

Domin sanin menene Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo Danna nan

(2) Haka nan toshewar ƙofofin salivary gland wato bututun sashin da ke samar da miyau a baki sakamakon tsakuwa da ta toshe (salivary stones) hakan yana sa warin baki sosai.

(3) Haka ma samuwar tsakuwoyin tonsils wato tonsils stones da ke faruwa sanadiyyar abincin dakan maƙale a baki da haƙoran mu bayan gama cin abinci, inda a hankali yakan haɗu da ƙwayoyin cutar bacteria a bakin ya haddasa wannan tsakuwar da ke haddasa warin bakin mara daɗi wanda har numfashi haka za a ji yana ɗoyi.

(4) Haka ma matsalar shigar ƙwayoyin cuta ramuka ko kogunan ƙashin fuska (sinuses) da ke ƙasan hanci suna haddasa (sinusitis) wato rauni a gun, ka ji hatta hancin mutum wari yake gami da ciwon kai ko ciwon fuska. 

(5) Haka yanayin abincin da mutum ke ci a kai a kai irinsu albasa ko tafarnuwa ba tare da tsaftar baki me kyau ba. 

(6) Ɗabi’ar shan ababen zaƙi kamar tea empty ko yaushe, chocolates, candy, coke da lemukan gwangwani da na roba. In ba a tsaftace baki da kyau tare da amfani da “tongue scraper” ana karce saman harshen wanke shi bayan an yi brush to ana iya wayar gari da warin baki a kwana a tashi.

Domin karanta matsala da maganin Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

(7) Ko kuma idan mutum na da kogon haƙori sakamakon abincin da ke shiga ciki ya maƙale nan ma yana iya haddasa warin baki

(8) Haka zalika rashin iya wanke baki koda ana yi kullum, shi ma brush ɗin iyawa ne, don haka in ba a sakuce ko ina da kyau ana iya wayar gari da matsalar.

(9) Haka ma idan mutum na kwanciya bacci ba tare da wanke baki ba bayan ya ci wani abu komai ƙanƙantarsa koda kuwa biscuits ne kada a raina, wannan bama warin baki ba hatta miyawun bacci na daga abinda ke kawo shi  wato kwanciya batare da cikakken tsaftar baki ba.

Matakan  Ɗauka

(1) Idan tsakuwoyin stones ne dole sai an huda an cire su, sai dai wannan aikin likita ne domin ba ganinsu ake ido da ido ba likita ne ya san mazauninsu a bakin, warin bakinsu ya fi hamami in su ne kamar an buɗe irin tukunyar gas ɗin nan haka za ka ji bakin mutum.

(2) Idan rashin yin brush da kyau ne toh ya dace a gyara.

(3) Idan haƙori me kogo mutum garehia ya je a wanke a cike kogon ko a cire haƙorin in ba zai ciku ba, shikenan an rabu.

(4) In wani abu mutum yake ci toh sai ya ƙaurace masa musamman lokacin kwanciya bacci, kar ka ci komi awa 2 kafin yin bacci in ba ruwa ba. 

(5) Wanke baki da ruwan sinadarin hydrogen peroxide irin wanda ake sayarwa don wankin ciwo, bayan an tsiyaya an ɗan ƙara masa ruwa kaɗan an kashe zafinsa sai ai amfani da shi ya zamto ana kurkure baki da shi sau 2 ko 3 a yini, yakan taimaka wajen rage matsalar idan har dalilin ƙwayoyin cuta ne.

(6) Tauna kanumfari kamar kwaya 3 yana sa a ji saukin abin musamman wanda hakan ke hana su sukuni.

(7)  Ko kuma tafasa kanumfarin ƙwaya 7 zusa sama a wadace da ruwa daidai misali a riƙa kurkure baki da ruwan ana zubarwa a hankali, ake yi safe da yamma zuwa wani ɗan lokaci, musamman a ce ana ƙarawa da gishiri a cikin ruwan, ya danganta da tsananin warin da ake ji. 

(8) In ulcer ce ai maganinta ita ma, sannan ake brush kullum kafin a kwanta.

(9) Haka in “SINUSITIS” ne da hatta mutum shi kansa yana jin inya buso iskar hancinsa ya shaƙa tana warin ga ciwon kai toh shi ma ya je ga likita a ba shi magani a warkar da abin.

(10) Ko amfani da apple cider vinegar wajen kurkure baki safe da yamma in ba kanumfari duk yakan taimaka.

(11) Haka ma amfani man olive a zuba a riƙa kurkurawa tsawon minti 20 a baki kafin a zubar, hakan a jere a kai-a kai zai tallafa .

(12) Haka ma amfani da baking soda wajen wanke baki safe da yamma ko duk bayan sanda aka gama cin abinci a madadin amfani da man goge baki.

(13) Sai canza brush a kai a kai kada ya ke wuce wata 3 ana amfani da brush guda.

(14) Koyon halayyar zuwa a riƙa wankin haƙora a clinics na dentist duk bayan wata 6 kimanin sau 2 a shekara zai taimaka, har lafiyar idanu da kunne sai ta ƙaru, ba sai me ciwon haƙori ba wannan zuwa flossing abu ne da ake so ga kowa.

Domin karanta Menene Amfanin Motsa Jiki Danna nan 

labarin da ya wuceMenene Amfanin Motsa Jiki?
Labarin na GabaYadda Zaka Bada Agajin Gaggawa Ga Wanda Ya Sha Kananzir (Kerosene)

SHARHI ƊAYA