Waɗanda Allah Ke Gaggauta Karɓar Addu’ar Su

0
426

WAƊANDA ALLAH KE GAGGAUTA AMSA ADDU’ARSU

1. Addu’ar Annabawan Allah.
2. Addu’ar mala’ikun Allah
3. Addu’ar wanda aka zalunta.
4. Addu’ar mai ƙarfin imani da tsoron Allah.
5. Addu’ar ɗa mai biyayya ga iyayensa.

6. Addu’ar mai Azumi.

7. Addu’ar shugaba adali.

8. Addu’ar iyaye (nagartattu) ga ‘ya’yansu.
9. Addu’a ga ɗan uwa a bayan idonsa.
10. Addu’ar mai jihadi.
11. Addu’ar mai Hajji ko Umrah.
12. Addu’ar mai dauwama cikin zikirin Allah.
13. Addu’a ga mai karatun AlQur’ani.

14. Addu’ar matafiyi (tafiya ta halal).
15. Addu’ar mai taka tsantsan wajen haram; abincinsa, abin shansa, tufafinsa da mazauninsa.

ABUBUWAN DA SUKE KAWO JINKIRIN AMSA ADDU’A

1. Shirka ƙarama da babba.
2. Ta’amuli da haram ci, sha ko tufafi.
3. Nauyin zunubai da ƙeƙashewar zuciya.
4. Barin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.
5. Tafseel (Dalla-dalla) a cikin addu’a

6. Wasa da wargi a cikin addu’a.
7. Addu’a da zuciya gafalalliya mai shagala.

8. Rashin ladabi a gaban Allah Jalla wa’ala.
9. Ta’allaqa addu’a ga mashi’ah (In ka so)

10. Gaggawa a cikin addu’a.
11. Al-Istihsaar( Shi ne mutum ya bar addu’a saboda gajiya da ƙosawa)

12. Rokon abin da hukuncin Allah ya gama da shi.
13.Saja’i a cikin addu’a (shi ne mutum ya tilasta wa kansa daidaita harafin ƙarshen jumlolin addu’a )
14. Bidi’o’I a cikin addu’a.

15. Roƙon wani abu da ya shafi saɓon Allah ko yanke zumunta.

Duba:
1. TAS’HIHUD DU’A na Dr.BAKR
2 ARRIYADUN NAZIRAH na Shk.Abdur Rahman Nasir Sa’adiy
labarin da ya wuceYadda Ake Pizza
Labarin na GabaLadubban Addu’a A Musulunci
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.