Yadda Za Mu Sabar Wa Kanmu Yawan Tuba

0
2118

Tuba daga zunubi shi ne yin nadama, barin zunubin, da neman gafarar Allah.

Ya zama dole ne mu tilasta wa kanmu yawan tuba. Domin samun yardar Allah maɗaukaki. Kuma Idan muna kwaɗayin samun amsawa ibadunmu, da addu’o’inmu , da arziƙi, da lafiya, da dukkanin biyan buƙatunmu.

Allah Ya fada cikin suratu Nuh: 10-11.
:Ku nemi gafarar Ubangijinku, lallai shi mai gafartawa ne. Sai ya aiko muku da ruwa mai kwarara daga Sama .

Kuma mu sani, saɓon Allah yana zama masifa a kan kowane abu. Yakan shafi rayuwar mutum, iyalansa har ma da dabbobinsa.

HANYOYIN DA ZA MU BI, DOMIN SABAR WA KANMU YAWAN TUBA

1 – Yawan karantawa da yin nazari wannan hadisin da Annabi ( S.AW) ya ce: Ya ku Mutane, ku tuba zuwa ga Allah, cewa ni ina tuba a cikin yini sau ɗari”. ( Muslim)

2 – Duk lokacin da muka aikata laifi. To mu yi amfani da damar da muka samu. Duba abin da Annabi (S.A.W) ya faɗa a wannan hadisi :

Babu wani musulmi da zai aikata laifi, sai mala’ika ya tsayar da shi har sa’a uku, wato ko zai tuba. In har ya tuba to..kuma ba za a yi masa azaba ba, a ranar alkiyama…

3 – Kwaɗayin rahamar Allah, a koda yaushe. Domin mu kasance cikin waɗanda Allah Yake farin ciki da mu. Duba wannan hadisi: Allah yana tsananin farin ciki da tubar bawansa, ..fiye da ɗayanku da yake kan dabbarsa sararin daji sai ta tsere masa, alhali abincinsa da
ruwan shansa yana tare da ita. Har ma ya fidda rai da ita. Sai ya zo jikin bishiya ya kwanta a inuwarta yana fidda rai da ita…sai kawai ya gan ta a gabansa tsaye. sai ya kama
ragamarta, sannan ya ce saboda tsananin farin ciki Ya Ubangiji Kai ne bawana,  ni kuma ubangijinka. YA YI KUSKURE SABODA TSANANIN FARIN CIKI (Mslm)

4 – A Koda yaushe muka yi azkaar ɗin safiya ko na maraice ka da mu manta da yin waɗannan:

Sayyidil Istighfar

5 – Sanya wa kanmu adadin yi a kullum. Kamar yadda Annabi (S.A.W) yai 100 / 70.

6 – Yin ayyuka na alkhairi , wanda Allah zai yafe mana da su. Misali. Kamar yadda karuwa ta shayar da kare ruwa, kuma Allah ya yafe mata, ya ba ta aljanna.

7 – Kauracewa saɓo domin gudun mummunar shaida daga mutane. Saboda tasirin shaida bayan mutuwar mutum. Ya tabbata cewa: Muminai su ne shaidun Allah a ƙasa.

tuba daga zunubai
Acikin wannan hadisin

An wuce da gawa, sai sahabbai suka yaba ta, sai Annabi (S.A.W) ya ce:” Aljanna ta tabbata a gare shi. Sannan aka sake wucewa da wata gawar, sai suka faɗi sharrinta, sai ya ce:” Wuta ta tabbata a gare shi. Sai Umar (R.A) ya ce me ya tabbata a gare su? Sai ya ce: Wannan kun yi masa kyakkyawan yabo, sai aljanna ta tabbata a gare shi. Wannan kuwa kun ambaci sharrinsa, sai wuta ta tabbata a gare shi. Domin ku ne shaidun Allah a doron ƙasa.

A ƙarshe jama’a mu duba mu gani. Idan har wanda Allah Yai masa gafara duk abin da yai a baya, da wanda zai a gaba. Annabinmu dan gatan Allah. Shugaban Manzanni. Wanda yake mafi kyawun halaye. Mai yawan ibada har kafafunsa na kumbura. A kullum yana yawaita Istighfari. To yaya mu za mu dinga sakaci? Allah Ya sa mu cikin bayinsa masu yawan tuba.

Litattafai da aka duba
Qur’an
Riyadu Salihin

labarin da ya wuceYadda Ake Wankan Soyayya
Labarin na GabaYadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.