Tambayoyin Azumi Da Amsoshi

0
40

SALMANU FARISS ADAMU

Tambaya :- Idan mutum ya fara yin azumin kaffara zai iya hutawa ?

Amsa :- Idan mutum  ya fara yin azumin kaffara ba zai iya tsayawa hutawa ba, sai idan yana da wata cuta, misali mace mai jinin haila ko wani mutum mai cutar gyambon ciki (ulcer) ko wata cuta ko hatsari ya samu mutum, wanda kuma  ba zai iya yin azumin ba, to wannan ya halatta a wannan yanayin mutum ya ajiye azumi har izuwa lokacin da mutum ya samu lafiya.

Misali idan mace tana yin azumin kaffara, sai kuma hailarta ta zo mata, sai ta ajiye azuminta, bayan ta ɗauke mata, sai ta ci gaba da azuminta daga inda ta tsaya, haka ma mutum mai ciwon gyambon ciki zai aikata ko wanda wata cuta  rashin lafiya ta same shi zai aikata.

Amma idan mutum lafiyarsa ƙalau, sannan  kuma babu wani dalili da shari`ar musulunci ta amince da shi na jingine ko ajiye azimi, har sai ya gama azuminsa a jere, idan kuma ya ajiye azuminsa a wannan halin, to dukkanin azumin da ya yi a baya sun rushe, sai ya sake tun daga farko.

Misali idan mutum ya yi azumi guda hamsin da tara, sai yace bari ya huta,  idan Allah ya kai mu jibi ya ƙarasa cikon azumin guda ɗaya, to azumin da ya yi a baya sun ruguje, dole ne sai ya sake lissafi tun daga farko. Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci a kanmu mu yi la`akari sosai a kan irin waɗannan matsaloli da sauran su.

Tambaya: Idan mutum yana saduwa da matarsa a cikin watan azumin Ramadan sai alfijir ya fito, to yaya hukuncin azuminsa yake ?

Amsa : Idan wani mutm yana cikin ganawa da matarsa sai kuma alfijir ya fito, azuminsa ya karyer matuƙar ya yi Inzali, sannan kuma akwai kaffaran azumi a kan su guda sittin (60).

Tambaya: Mutum ne yake kwance bayan alfijir ya fito  ko bayan an yi sallar Asubah, sai matarsa ta zakke masa ,to yaya matsayin azumin su yake ?

Amsa: Azuminsu ya ruguje ko ya rushe, sannan kuma akwai kaffaran azumin guda sittin a kansu. Bugu da ƙari kuma malamai sun ce ” mace ba za ta iya zakkewa ɗa namiji ba kai tsaye kuma ta yi Inzali ba tare da shi namijin yana so ba, Allahu a`alamu.

Tambaya : mace ce take yin azumi, to kuma ya rage saura kamar mintuna biyu a sha ruwa, sai hailarta ta zo mata, ko lokacin haihuwarta ya yi, to yaya matsayin azuminta yake?

Amsa:  Duk wacce haka ta faru da ita, to azuminta na wannan ranar ya rushe, sai ta sake wani azimin bayan an sha ruwa, amma kuma babu kaffara a kan ta.

Tambaya: Menene hukuncin mutumin da ya aikata wani abu wanda yake karya azumi, amma kuma shi a lokacin da yake aikata wannan abun, shi bai san hukuncin aikata haka ba?

Amsa:- Duk wanda ya aikata wani abu, saannan kuma a lokacin da yake aikata abin shi kansa bai san hukunci aikata haka ba, babu laifi a kansa, saboda Allah (S.W.A) ba zai kama mu ba da abin da muka aikata bisa ga rashin sanin hukuncinsa ba. Sai ya roƙi Allah gafara a kan abin da ya aikata, sannan kuma yana da matuƙar mahimmanci a kan musulmi duk abin da zai aikata a rayuwarsa ya san hukuncinsa, Allah yasa mu dace.

Domin karanta Azumin Watan Ramadan danna nan

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAzumin Watan Ramadan
Labarin na GabaAzumin Watan Ramadan 2