Tag: Falalar

  • Falalar Sallatut Tasbihi

    Falalar Sallatut Tasbihi

    Duk wanda ya yi wannan salla, Allah zai gafarta masa dukkan zunubansa na farko da na ƙarshe, tsoho da sabo, na kuskure da na ganganci, babba da ƙarami,na fili da na ɓoye.

    Kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ƙarfafa a yi wannan sallah kullum in da hali ko sati ko duk wata ko duk shekara kai ko da sau ɗaya ne a rayuwar mutum. Wannan bayani ya zo a hadisin da Abu Dawud (1279, Ibn Mjah 1387, Hakim 1/318, 319, Ɗabarani 161/11, da Abu Nu’aim 1/25- 26 suka ruwaito ta hanyoyi daban-daban daga Ibn Abbas.

    Matsayin Wannan Hadisi

    An daɗe ana saɓani kan inganci ko raunin wannan hadisin.
    Daga ciki masu raunana shi akwai (1) Imam Ahmad (2) Tirmizi (3)Ibnul arabi (4) Ibnul Jauzi (5) Ibn Taimiyya da sauransu.
    Masu ƙarfafa hadisin kuwa sun haɗa da Muslim, Abu Dawud, Hakim, Baihaƙi, Iban Hajar, Ahmad Muhammad Shakir da Albani. Allah ya yi rahama a gare su.
    Amma malamai irin su ibn Huzaimah da Zahabi sun yi gum da bakinsu, ba su faɗi komai ba kan matsayin hadisin.
    Saboda wannan saɓani ne, a kan sami saɓani kan hukuncin yin ita sallar, waɗansu suka ce ana so a yi, su ne wanɗanda suka inganta hadisin, waɗanda suka ce ba laifi in an yi, amma waɗanda suka raunana hadisin suna ganin sam bai halatta a yi ba. To wannan al’amari dai mai sauƙi ne, wanda zai yi ya yi, wanda ba zai yi ba ya bari. Allah ya ganar da mu amin.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Tahiyyatul Masjid danna nan .

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Sallar Walaha

    Falalar Sallar Walaha

    a) An karɓo daga Buraidah (R.A) Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam)Ya ce: “A jikin ɗan Adam akwai gaɓoɓi ɗari uku da sittin (360) wajibi ya yi sadaka a kan kowace gaɓa” sai suka ce wane ne zai iya wannan ya Manzon Allah? (sallallahu alaihi wasallam) Sai ya ce: Binne majina a masallaci (Wato in ka ga wani ya yi kaki ya kwamɓala ta a masallaci ka binne ta) ko ka kawar da abu mai cutarwa daga hanya, in ba ka sami iko ba, raka’a biyu ta walaha ta wadatar”. (Abu Dawud 2/524).

    b) An karɓo daga Abu zarr (R.A) ya ce: ” Sadaka tana hawa kan kowace gaɓa ta ɗayanku kowace safiya, kowane tasbihi daidai yake da sadaka, kowace hamdala (Alhmdulillahi) daidai take da sadaka, kowace hailala daidai take da sadaka, kowacce kabbara daidai take da sadaka, umarni da kyakkywan aiki daidai yake da sadaka, hani ga mummunan aiki daidai yake da sadaka, raka’a biyu ta walaha tana wadatarwa ga wannan.” (Muslim 720)
    Wannan hadisi yana nuna mana cewar Sallar walaha raka’a biyu daidai take da sadaka ɗari uku da sittin (360).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Istahara danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Wutiri.

    Falalar Wutiri.

    1- Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:

    “Haƙika Allah Ta’ala ya ƙara muku wata sallah, ita ce sallar wutiri; ku sallace ta tsakanin sallar Isha da fitowar alfijir”. (Ahmad 6/397).

    2- Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Wanda ba ya yin wutiri ba ya daga cikinmu”.(Ahmad 2/433/ Hadisin Da’ if).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Yin Wutiri danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafashi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Raka’ Atil Fajr.

    Falalar Raka’ Atil Fajr.

    Raka’atul Fajri su ne raka’o’i biyu da ake yi kafin Sallar Asuba. Ana taƙaita su wato ba a tsawaita karatunsu da ruku’insu da sujjadarsu, kuma ana son yi su a gida kafin a fito masallaci. Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:

    “Raka’atul fajri ta fi duniya da abin da yake cikinta”.( Muslim 728, Tirmizi 416).

    Domin karanta cikakken bayani akan Raka’a Biyu Kafin Magariba danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.