Al’adun Bahaushe suna kamancecceniya da na Larabawa da Habashawa da Kanuri wajen suturta jiki, wataqila saboda alaqa uwar harshe da suka haxa (a tunanina).
Tun kafin zuwan addinin Musulunci, Bahaushe yana qoqarin suturta al’aurarsa, da bantai, taguwa (riga ‘yar ciki da babbar riga), wando tsala, takalmi fele, hula kube, zanin mata, gyale/mayafi da kallabi (Lawi, 2017).
Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan
Bahaushe ya sami baqin sutura daga Larabawa da Turawa da sauran qabilun da ke kewaye da shi. Bahaushe ya xauko jallabiyya, abaya daga Larabawa, sai kwat, siket, nek tayal, gown daga Turawa. Sai hulunan Kanuri, damanga, zanna bukar da sauransu.
Bahaushe mutum ne mai gyaran jiki da tsafta, yana wanka a kogi, ko gulbi, ko makewayi, yana aski, da gyaran fuska da yanke farce. Mata kuma na qunshi da lalle, kitso.