Mu halitta ce ta jinsin mutane, kuma muna daga cikin waɗanda Allah bai halicce su domin komai ba, sai domin su bauta masa kawai. Saboda haka, Ya ba mu hankali domin mu yi ilmi, da shi ne za mu san dai-dai kuma mu san abin da ba dai-dai ba, mu bambance tsakanin gaskiya da ƙarya, mu gane bambanci shiriya da ɓata. Da haka za mu iya yin aiki nagari, mu kuma nesanci miyagun ayyuka.
Mutum cikakke shi ne wanda ya yi imani da Allah da Manzo Sa, kuma ba ya rabuwa da yin managarcin aiki, idan a ka samu saɓani, ya yi tuntuɓe, ya aikata kuskure, sai ya yi sauri ya tuba ya koma ga Allah Mahalicci , saboda shi mai imani ne da Allah, kuma mai yin koyi da Manzon Allah (S.A.W).
Wannan ita ce siffa ta cikikken mutum, a mahangar Musulunci. Ba kawai kasancewar sa mai ɗauke da kai da ƙafa da iya magana, da dariya ba, ya zama tilas sai ya haɗa waɗannan siffofi sannan zai amsa sunansa Ɗan’Adam. Daga nan ne idan an yi tambaya: “Mu Ɗin Su Wane Ne?” Za mu cancanci bayar da amsar: “Mu mutane ne”.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ɗan’Adam Kamar Yadda Allah Yake Son Sa wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa domin karanta cikekken littafin nan DANNA KOREN RUBUTUN NAN