Tambaya
Assalamu Alaikum warahmatullah. Malam don Allah ina neman fatawa.
Wata ce take neman miji, kasancewar duk masu zuwa wajen ta ba da gaske suke yi ba, to shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake ba ta rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya a nan shi ne? shin me ne makomar abin da ta aikata shin malam ta yi shirka ne ko kuwa ta yi ba daidai ba? Na gode.
Amsa
Da farko game da shan rubutu muddin ayar Alkur’ani tsantsa babu wasu zane zanen hatimi- to ya halatta yayya IBN TAIMIYYA yatabbatar a MAJMU’UL FATAWA, hakama WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya ba tabbarda hakan a SARIMUL BATTAR,
Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,
Faɗin cewa Malamin zaurene na gargajiya to galibi irin na shirkar suke yi, don haka ki tuba tsakaninki da ALLAH da alkawarin ba za ki sake zuwa wurinsu ba don kare addininki da mutuncinki,
Don samun biyan buƙatunki, sai ki dage da addu’a da kiyamunllaili da Azumi da istigfari, kuma kina iya lazimtar wannan addu’ar domin shi ANNABI MUSA ya yi ya sami akin yi da matar aure a ranar, ga addu’ar👉🏼
رب إني لما أنزلت إلي من خير فقير
ALLAH yayafe mana kuma yabaki miji nagari,
ALLAHU A’ALAM.
Amsawa Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
05/10/2019
Daga : ZAUREN ISLAMIC SUNNAH