fbpx
Gida Ilimin Addini Sallar Kisfewar Rana Da Wata (Zazzaɓin Rana Da Wata)

Sallar Kisfewar Rana Da Wata (Zazzaɓin Rana Da Wata)

0
888

Sallar kisfewar(kusufi) rana da wata sunna ce mai Ƙarfin gaske. Ana yin sallar kisfewar rana a cikin jam’i tun daga lokacin da haskenta ya dusashe har zuwa dawowar hasken.

Ga yadda ake yin wannan sallah:

1- Ana yin kabbarar harama, a karanta addu’ar buɗar sallah (Istifah) ayi a’uzu billahi, a karanta Fatiha sannan a yi dogon karatu kimanin Suratul Baƙara.
2- Sai a yi dogon ruku’u kwatankwacin wannan tsayuwar.
3- Sai a ɗago daga ruku’u a ce: Sami allaahu li hamidahu, rabbana walakal hamdu.
4- Maimakon, a tafi sujjada sai a karanta Fatiha da doguwar sura kwatankwanci Ahli-Imran.
5- Sai a sake dogon ruku’u kwatankwacin tsayuwar ta biyu
6- Sai a ɗago daga ruku’u a ce: Sami allaahu li hamidahu rabbana walakal hamdu”.
7- Sai sujjada, sai zama, sai sujjada ta biyu.
8- Sannan sai a tashi zuwa raka’a ta biyu, a yi kamar yadda aka yi a raka’a ta farko sai dai ana rage yawan tsayuwa da tsawon ruku’u.

Idan aka gama hasken ranar bai dawo ba, sai a sake yi har dai hasken rana ya dawo; kuma a bayyane ake yin karantun ta. Amma kisfewar wata waɗansu malamai suna cewa ana yin irin wannan Salla in ya faru, waɗansu kuma suka ce a’a raka’a biyu ko fiye kawai za a yi kuma ba a jam’i ba.
Amma babu inda aka ce a fita ana ihu da kururuwa da kade-kade da raye-raye da waƙe-waƙe wai don wata ko rana suna zazzaɓi wannan bidi’a ce mummuna.

Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Roƙon Ruwa danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

×

Maraba!

Yi magana da mu kai tsayi ta WhatApps ko a shiga group din mu.

×