Nau’o’in Sujjadar Rafkanuwa

0
23

Sujjadar rafkanuwa iri biyu (2) ce, akwai 

  1. Qabli: ita ce wacce ake yi kafin a yi sallama (bayan an karanta tahiya da salatin ;kuma akwai ,(صلى هللا عليه وسلم Annabi 
  2. Ba’adi: ita ce wacce ake yin ta bayan an yi sallamar sallah. 

DALILAN SUJJADAR RAFKANUWA 

Ana yin sujjadu guda biyu (2) qabli ko ba’adi ne idan aka samu:

  1. Qari, ko 
  2. Ragi, ko kuma 
  3. Qari da Ragi a lokaci guda, ko 
  4. Shakka a cikin sallah. 

SIFFOFIN SUJJADAR RAFKANUWA 

  1. Wanda ya yi ragin wani aiki a cikin sallah zai yi qabli (sujjadu guda biyu kafin sallama). 
  2. Wanda ya yi ƙari a cikin sallah, zai yi ba’adi (sujjadu guda biyu bayan sallama). 
  3. Wanda ya yi shakka a cikin sallah, zai yi gini a kan abin da zuciyarsa ta kwanta a kai na ƙari ko ragi (yaqini). Akwai bayaninsu a gaba insha Allah. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

ABIN LURA: 

Kafin mai sallah ya fahimci yadda zai gyara sallarsa da “sujudus sahwi” yana da kyau ya san sharuɗa, rukunai, farillai, sunnoni da mustahaban sallah, saboda: 

  1. Akwai ayyukan da rage su ko ƙara su yana sa a yi “sujudus sahwi”. 2. Cikin aiyukan da rage su ko ƙara ke sa a yi “sujudus sahwi”, wasu ana yi musu ƙabli, wasu aiyukan kuma ana yi musu ba’adi. 
  2. Akwai aiyukan da barin su ba ya sa a yi sujjada. 
  3. Akwai kuma ayyukan da sai sun kai wani adadi za a musu sujjada. 5. Akwai ayyukan da barin su (kaɗai) ɓata sallah suke baki ɗaya. 6. Akwai ayyukan da barin su yana bata raka’a kaɗai, sai a zare ta, a jefar, a sake ta, sannan a yi sujjada. 

Domin Karanta Bayani akan Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce Danna Nan

3Sahih Muslim, hadisi na 573. 

4Sahih Muslim, hadisi na 572.

RAFKANUWAR DA AKE YI WA ƘABLI 

  1. Ɓoye karatun sallah a idan ake bayyanawa. 

Wanda ya tuna ya ɓoye karatun sallah kafin ya yi ruku’u, zai dawo ya sake karatun a bayyane. 

Idan iya karatun surah ne ya ɓoye, idan ya dawo ya sake karatun a bayyane; babu sujjada a kansa. Idan kuma har ya ƙulla raka’a (ya yi ruku’u) zai yi sujjada ƙabli. 

Idan kuma karatun Fatiha ne ya ɓoye a wurin bayyanawa, zai dawo ya sake a bayyane, sai kuma ya yi sujjada ba’adi. 

  1. Wanda ya tsallake aya ɗaya cikin karatun Fatiha zai yi qabli. Idan kuma ya wuce aya ɗaya, sallah ta ɓaci. 

Idan kuma a karatun surah ne, mai sallah ya cije, zai tsallake aya da ya cije, ya je ta gabanta. Idan babu mai tuna masa, zai wuce ya yi ruku’u, babu komai a kansa. 

  1. Rage sunnoni biyu zuwa sama. 
  2. Ba za a yi sujjada ƙabli saboda rage ruku’u’, ko karatun Fatiha’, ko ‘sujjada’ ba saboda su rukunai ne. 

Wanda ya manta karatun Fatiha, ruku’u, ko sujjada a cikin sallah, zai dawo ya rama su, sannan ya yi sujjada ba’adi, idan kuma ya ƙulla raka’a, raka’ar ta ɓaci.5 

  1. Wanda ya manta tahiyar farko, zai yi ƙabli. 

RAFKANUWAR DA AKE YI WA BA’ADI 

  1. Ƙara raka’a. 

Misali, wanda ya tashi ƙarin raka’a ta uku (3) a sallar Asubah, ko raka’a ta huxu (4) a sallar Magriba, ko raka’a ta biyar (5) a sallolin Azahar, la’asar ko Isha’i, idan ya tuna bayan ya tashi, zai dawo ya zauna, sai ya yi sujjadu biyu bayan sallama (ba’adi). 

  1. Wanda ya bayyana karatun sallah a wajen ɓoyewa, zai yi sujjada ba’adi.

QABLI DA BA’ADI 11 

  1. Wanda ya yi shakkar ya rage raka’a, zai zo da ita, sannan ya yi ba’adi. 4. Wanda ya karanta wani harafi da ba na cikin Alqur’ani ba, ko canja harufan Alqur’ani, zai yi sujjada ba’adi. 
  2. Rage rukuni. 

Misali, wanda ya manta karatun Fatiha, ko ruku’u, ko sujjada, zai jefar da raka’ar da ya yi mantuwa a cikinta, ya gina wata, sannan ya yi sujjada ba’adi. 6. Wanda ya manta sujjada ta biyu (2) a raka’ar farko, bayan ya tashi daga ruku’un raka’a ta biyu, sai ya tuna bai yi sujjada ta biyu ba a raka’a ta farko, to, zai koma ya zauna, sai ya yi sujjadar, sannan ya cika sallarsa, sai ya yi sujjada ba’adi (ita kuma waccar raka’a ta biyun an jefar da ita). 

Domin Karanta Bayani akan Yin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce Danna Nan

  1. Wanda ya maimaita karatun Fatiha da rafkanuwa zai yi sujjada ba’adi. Idan kuma da ganganci ne, sallah ta ɓaci. 

RAFKANUWAR DA BA A YI WA SUJUDUS SAHWI 

  1. Tauye sunnah guda ɗaya (sai an tauye fiye da ɗaya ne ake yin ƙabli), amma banda sunnar bayyanawa ko asirta karatu (duba bayani na 3 na qasa). 
  2. Wanda ya manta mustahabbi6, babu sujjada a kansa. 
  3. Tuna rashin bayyanawa ko asirtawa na karatun surah (ban da karatun Fatiha). Kafin qulla ruku’u, idan mai sallah ya dawo, ya sake karatun surah a bayyane ko a ɓoye, babu sujjada a kansa. 

Idan kuma ya wuce zuwa ruku’u, sai ya yi ‘qabli’ saboda ɓoyewa (a inda ake bayyana karatu), ko ‘ba’adi’ (saboda bayyana karatu a inda ake asirtawa). 

  1. Wanda ya yunƙura zai tashi a zaman sujjadar farko, sai ya dawo ya zauna kafin hannayensa su rabu da qasa, babu sujjada a kansa. 

6Misalan Mustahabban sallah su ne: 

  1. Ɗaga hannaye yayin kabbarar harama, 

مُدَ2. Faxin

َ bayan ɗagowa daga ruku’u, 

  1. Tasbihi cikin ruku’u, 
  2. Damanta sallama, 
  3. Motsa ɗan yatsa (sabbaba) a tahiya… da sauransu.

QABLI DA BA’ADI 12 

  • Amma idan hannayensa sun bar qasa, zai miqe ya ci gaba da sallah, sai ya yi sujjadar qabli. 
  • Idan kuma ya dawo, bayan ya rabu da kasa, a rafkane ko a sane, zai yi sujjada ba’adi. 
  1. Furta zance kaɗan, idan ba da ganganci ba ne. 
  2. Nuni da hannu, ko kai, matuƙar jiki bai juyawa alƙibla baya ba. 
  3. Wanda ya yi waiwaye a sallah bisa mantuwa, babu komai a kansa. Idan da ganganci ne ya yi makruhi, idan kuma waiwayen ya sa gangar jikinsa juyawa, sallarsa ta ɓaci, sai ya sake ta. 
  4. Gyatsa, ko amai, ko ajiyar numfashi ko nishi (saboda da ciwo) na marar lafiya (amma ban da na ganganci ba). 
  5. Yin kuka domin tsoron Allah a cikin sallah. 
  6. Yin shiru (ɗan kaɗan) saboda sauraron magana. 
  7. Atishawa cikin sallah. 

Kuma ba sai mutum ya yi ‘hamdala’ ba idan yana cikin sallah, haka nan ba zai mayar da ‘Yahdikumullah’ ga wanda ya ce masa: Yarhamukallah ba. Idan kuma ya faɗi “Alhamdulillah” ɗin, babu komai a kansa. 

  1. Wanda ya yi gyangyaɗi (kaɗan) a cikin sallah babu komai a kansa. Amma idan ya yi nauyi, zai sake alwala, ya kuma sake sallah. 
  2. Ƙarin karatun surori a raka’a ta 3 ta Magriba, ko raka’a ta 3 da 4 a Azahar, La’asar da Isha’i, ba komai a kansa. 
  3. Yiwa Annabi وسلم عليه هللا صلى Salati idan ka ji an ambaci sunansa, alhalin kana cikin sallah. 

RAFKANUWAR DA KE ƁATA RAKA’A 

  1. Manta rukuni. Misali: 
  • KARATUN FATIHA:

Wanda ya manta karatun Fatiha a raka’a ta farko, har ya qulla raka’a ta biyu, zai jefar da waccan raka’a ta farko, ya maye ta da ta biyu, ya yi sujjada ba’adi. • RUKU’U: 

Wanda ya manta ruku’u a raka’a ta farko, har ya qulla raka’a ta biyu, zai jefar da waccan raka’a ta farkon, ya maye ta da ta biyu, ya yi sujjada ba’adi. Idan kuma ya tafi sujjada, sai ya manta bai yi ruku’u ba, sai ya koma ya sake ruku’u ya ci gaba da sallah (amma an so ya maimaita karatun sallah kaɗan), sai kuma ya yi sujjada ba’adi. 

  • SUJJADA: 

Wanda ya manta yin sujjada ta biyu, har ya tashi, bayan ya qulla wata raka’ar (ruku’a), zai dawo ya cika ta, sai ya cika sauran sallar, ya yi sujjada ba’adi. 

RAFKANUWAR DA KE ƁATA SALLAH BAKI ƊAYA 

  1. Manta kabbarar harama. 

Wanda ya qulla raka’a ko har ya sallame, sai ya tuna bai yi “kabbarar harama” ba, zai sake niyya, ya yi kabbara, ya sake sallah (domin babu sallah, idan babu kabbarar harama). 

  1. Yin amai da gangan. 
  2. Nishi da qarfi don isar da saqo (ko da mai sallar marar lafiya ne). 4. Juyawa alqibla baya a cikin sallah, da gangaci, ko da lalura. 
  3. Bayyana tsiraici (a cikin sallah). 
  4. Yin Magana ko dariya da gangan (a cikin sallah). 

RAFKANUWA CIKIN SALLAH TARE DA LIMAN 

  1. Idan liman ya yi rafkanuwa a cikin sallah, ya halatta mamu (masu bin sa sallah) su yi masa tasbihi, su ce: SUBHANALLAH, domin ankarar da shi. 
  2. Liman yana ɗauke rafkanuwar mamu, banda a wuraren da: 
  3. a) Idan mamu ya tauye farilla ne, ko 
  4. b) Rafkanuwar ta samu mamu a lokacin yana masbuki (mai cika sallah) rafkanuwar ta same shi. 

Misali, wanda aka matse a sahu, ya kasa ruku’u, har liman ya ɗago daga ruku’un, ya tafi sujjada; tom, idan mamu zai iya riskar liman a sujjada ta biyu (2), to sai ya yi ruku’un, ya yi ƙoƙarin ya riske shi a sujjada ta biyu. Idan kuma mamu ba zai iya samun liman a sujjada ta biyu ba, sai ya jefar da raka’ar, ya rama ta bayan liman ya sallame, kuma babu sujjada a kansa.

Idan kuma a sujjada ne aka matse mamu, sai ya yi ƙoƙarin yin sujjadar da bai yi da liman ba kafin liman ya ƙulla wata raka’ar (ma’ana a yi ruku’u). Idan har liman ya kai ga yin ruku’u na wata raka’ar, nan ma mamu zai jefar da raka’ar, ya rama raka’ar bayan liman ya sallame sallah, shi ma babu sujjada a kansa. 

  1. Rafkanuwar liman na hawa kan mamu, matuƙar mamu ya sami raka’a (ko da ɗaya ce) tare da liman, koda limanin ya yi rafkanuwa a raka’ar da mamu bai riska ba. 

Misali, liman ya yi rafkanuwa a raka’a ta ɗaya (1), mamu kuma ya sami raka’a ta biyu (bayanin sujudus sahwinsa na bayani na 4 na qasa). 

  1. Idan mamu ya samu raka’a ɗaya cikakkakiya ko fiye da ɗaya tare da liman (a sallar jam’i), zai yi sujjadar ƙabli tare da liman. 

Idan kuma sujjada ba’adi ce, mamu zai yi ta ne bayan ya cika sallarsa. Idan kuma ya yi sujjada ba’adi (da ganganci) tare da liman, sallarsa ta ɓaci. Idan kuma da mantuwa ne masbuƙi ya yi sujjada ba’adi tare da liman, zai yi sujjada ba’adi, bayan ya cika sallah. 

  1. Idan mamu ya sami ƙasa da raka’a ɗaya a tare da liman7, ba zai yi sujjadar qabli ko ba’adi ba. Idan ko ya yi, to sallarsa ta ɓaci. 
  2. Idan kana bin liman sallah, sai ka ga (liman) ya miqe daga raka’o’i biyu, maimakon ya yi ‘zaman tahiya’, za ka yi masa ‘tasbihi’, idan ya rabu da ƙasa, sai ka tashi ka bi shi. 
  3. Idan liman ya zauna a raka’a ta xaya (1), misali a sallar Asubah, ko a raka’a ta 3, misali a sallar Azahar, La’asar ko Isha’i, mamu ba zai zauna tare da shi ba (zai miƙe ne), ya yi masa ‘tasbihi’, sai limamin ya tashi a ci gaba da sallah. 
  4. Idan liman ya yi sujjada ɗaya, bai yi ta biyu ba sai ya miƙe zuwa wata raka’ar, a nan mamu ba zai tashi tare da limamin ba, zai yi masa ‘tasbihi’ ne. Idan limamin bai dawo ba, sai mamu ya tashi, ya bi shi, saboda tsoron kar limamin ya qulla raka’a. 
  5. Idan liman ya yi sujjada ta uku (3), mamu zai yi masa tasbihi, amma ba zai bi shi ba (ma’ana, kar mamu ya yi sujjada ta 3 tare da shi).

10.Idan liman ya tashi ƙarin raka’a ta 5 (misali, a Azahar, La’asar ko Isha’i, ko ya tashi qara raka’a ta 4 a Magriba, ko ta 3 a Asubah), mamu ba zai bi shi ba, idan yana da yaƙinin ƙari liman zai yi. Idan kuma mamu ya bi shi (bayan yana da yaƙinin wannan raka’ar ƙari ce), sallarsa (mamu) ta ɓaci. 

11.Idan liman ya yi sallama kafin cikar sallar (misali da raka’a), sai ka masa tasbihi, ya dawo ku cika sallah, ku yi sujjada ba’adi. 

12.Mamu zai iya gyarawa ko tashin limansa karatu, idan ya cije. * Amma wanda ya gyarawa limamin da ba nasa ba karatu, sallarsa (mamu) ta ɓaci. 

13.Ba a gyarawa liman karatu sai an jira (ya yi shiru, ma’ana, yana buƙatar a tashe shi, ko a gyara masa). 

14.Idan sujjada ba’adi ta kama masbuki8ta ɓangaren limaminsa, shi kuma a lokacin ciko sallah ‘ƙabli’ ta kama shi, sai ya yi sujjada ƙabli ta isar masa.

Domin Karanta  Cikekken Littafin Danna Nan

labarin da ya wuceSujjadar Rafkanuwa
Labarin na GabaShakku A Cikin Sallah