An tambayi Imam Hasanul Basari?
Me ya sa ba ka damuwa da maganganun mutane? Sai yace,
“Lokacin da aka haife ni, ni kaɗai aka haifa,
Kuma lokacin da zan mutu, ni kaɗai zan mutu
Kuma ni kaɗai zan kwanta a kabarina,
Kuma ni kaɗai za a tashe ni a yi min hisabi.
Kuma ni kaɗai za a ba sakamakona,
Don haka ina ruwana da maganganun mutane?
Domin in dai maganganun mutane shi ne damuwarka, sai dai idan ba ka shirya zaman duniyar ba.”
Allah ya datar da mu.
Danna nan don karanta Nasiha mai tsoratarwa
Edita; Rumasa’u M. kallamu