Nakan Ji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ]

0
20

Wannan yanayin shi ake kira “Globus Historikus”wato ko yaushe mutum ya riƙa jin kamar ya haɗiyi wani abu amma ya kakare masa a maƙogoro yaƙi ya tsirga,duk irin kokarin da zai na ya daina ji yayi amma abin ya kafe.

Abubuwa da dama kan jawo haka musamman a yau da  damuwa da halin matsi su kaiwa mutane yawa,ɓacin rai da fargaba sune kan gaba wajen jawo haka, gami da yawan tuna abubuwa marasa daɗi da suka ko suke faruwa da mutum.

Hakan kan faru ne inya zamanto tsokokin maƙoshin na harbawa akan kansu wato ‘Voluntarily’ me makon su jira umarni daga mutum ya ƙudurci hakan wato ‘involuntary’ wanda wannan voluntary ɗin abu ne da bai dace suyi ba,don haka in suka tsuƙe wato contractions sai mutum ya riƙa jin wannan abin saboda stress.

Hakazalika wasu dalilan da ba wannan kansa arika jin wannan yanayin na tokarewar abu a maƙoshi kamar; matsalar ƙurji jikin ƙashin mukamiƙi (ostiyofayit) wanda ke danne maƙoshin, ko kuma ya zamto dalilin wani ɓarawo ƙwaroron bututu na wucewa abinci da ya haifar da rabuwar hanyar maƙogoron gida biyu (dayibatikyula),ko ya zamto matsalar daga matsuƙin maƙogoro na ƙasa take shine ke buɗewa baya tsukuwa dede mutum ke samun matsalar ƙwarnafi ko tasowa acid wanda shike sa jin hakan sakamakon acid din ciki na tasowa ya taɓa sassan magana sai ya haifar da ƙurji agun wato inflammation. 

Domin karanta Cewa Uwa Zata Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa Danna nan

Ko kuma matsalar ta zamo baki ɗaya daga kogunan ƙashin fuskar mutum ne wato (sayunus) wanda kila dalilin mura ƙwayoyin cuta suka shiga suke haddasa harma ciwon kai yayin sallah da in mutum yai ruku’u zai rika jin kamar fuskarsa zata zazzago ta faɗo,ko kila ma ya rika jin numfashin sa ko tusononsa na wari sosai wato Chronic sinusitis,larurar tairoyid gland musamman maƙoƙon wuya shima na iya sawa, ko thyroid cancer

Haka kuma yana iya kasancewa Ƙarancin sinadaran ƙwarin ƙashi ne ya jawo musamman ‘kalsiyom’ tun ma ba a macen dake shekarun daina haila ba,hakazalika kamar yadda na faɗa abaya cutar damuwa wato depression ko fargaba ‘anxiety’ na daga kan gaba wajen haddasa hakan,sai bayan yan binkice a gane ainishin matsalar bama a maƙogoron take ba,wannan sune ababen da kan jawo haka.

Abin yi shine da farko mutum yai iya yinsa wajen daina tunawa da abin, kurum yake mance batun sa,da kansa zai tafi,ko ya ƙara da riƙa tauna cingam ko yaushe. 

Amma in abin yaci tura kuma yana damun mutum toh ya dace aje ga likita a tsaya a duba da kyau,wannan dai matsala ce da ake iya magancewa, likitoci za su haska cikin bakin su tabbatar babu matsalar tonsils wato kumburin wasu abubuwan ganɗa na gefe da gefe,ko canzawar kalar cikin ganɗar da hanƙa.

Domin karanta bayani akan Larurar Sarƙiwar Numfashi Da Ake Kira (Asthma) Danna nan

Babban likita ya dace agani in hakurin mutum har ya fara ƙarewa batare da yaji abin ya barsa ba,likitan da akan gani shine ƙwararren likitan kunnuwa,hanci da maƙoshi wato ENT DOCTOR.

Saboda karamin asibiti ba a cika samun irinsu ba,wanda a karamin asibiti ko ba kowa ne zai fahimci matsalar ba,amma agun ENT ko Inta kama can har hoton wuyan wato X-RAY da Endoscopy a haska cikin ciki duk zasu iya yi su duba agani, gami da sauran gwaje-gwaje.

Amma dai galibi hakan ba alama bace ta wata babbar matsala don takan tafi da kanta batare da magani ba,har sai in abin yaci tira. 

Domin bayani akan Gyambon Ƙoda [Pyelonephritis] Danna nan

labarin da ya wuceGyambon Ƙoda [Pyelonephritis]
Labarin na GabaMatsalar Zubar Yawun Bacci