Na Kan Wuni Cikin Kasala A Duk Sanda Na Yi Jima’i Ko Inzali

0
181

Wannan na daga cikin alamomin larurar da muke wa laƙabi da Fost Ogasmik Ilines Sindurom, wato rukunin alamomin matsala da ke biyo bayan inzali.

Wata matsala ce da wasu rukunin mutane cikin maza ke fuskanta, yadda da zarar sun yi inzali wato releasing ta kai ga maniyyi ya fita a jikinsu walau yayin saduwa da iyali, ko yayin istimna’i, ko kuwa dalilin mafarkin jima’i a sanda suke bacci, da dai duk wata hanya da maniyyi ka iya fitowa a jikin su toh za su sami kansu cikin yanayi na rashin jin daɗin jikinsu a wannan rana har zuwa kwana biyu, ko kwana biyar kai wasu ma har tsawon sati ɗaya cikin rashin daɗi.

Domin a wasu in su ka yi inzalin nan abin kan biyo musu da alamu irin na me yin mura inda nan take za su fara jin zazzaɓi-zazzaɓi, tsananin kasala, da ƙaiƙayi ko raɗaɗin idanu, wasu harda ciwon kai.

Domin karanta Alamomin Cancer Danna nan

Wanda kuma abin kan cigaba har su kasa samun nutsuwa su yi aikin da ke gabansu a wannan lokaci, sam suke rasa concentration, har suma riƙa jin ɓacin rai ko hayaniya ba sa so kusa da su, sai dai duk wannan alamomin za ka same su ka rasa bayan kwana 3 zuwa 7, shikenan mutum zai dawo normal, ba zai ƙara jinsu ba har sai in ya kuma samun fitar maniyyi.

Wannan al’amarin kansa da yawa cikin irin waɗannan mazajen ƙauracewa jima’i, ba wai don ba su da sha’awa ba, sai don sukan sami kansu a halin rashin daɗin jiki, amma haka in ka kalle su lfy ƙalau surarsu da suffar su take dama.

Wannan na daga cikin larurorin da masana a fannin lafiya suka tasa gaba domin zurfafa bincike a kan dalilin da ke jawo hakan, wannan tasa har yanzu ba wani sanannen abu da za a iya dangantawa da shi ke jawo hakan, haka zalika rashin sanin abinda ke jawo ta yasa ba a san maganin matsalar ba, ko a asibiti ba mu da maganin larurar.

Sai dai sabbin bincike da suka fara fitowa suna alaƙanta cutar da matsalar allergies ne da ke faruwa sakamakon garkuwar jikin mutum da ya dace a ce yana ba shi kariya daga cuttuka ita ce ke kuskuren fahimtar inzali a matsayin matsala inda take kai farmaki ga ƙwayoyin sassan halittar maniyyi na jikin mutum bayan sun aikinsu, inda mutum ke ƙarewa da wannan alamomin wato dai Autoimmune Disorder, sai dai har yau binciken bai kammala ba, kuma duk abinda aka ce autoimmune ne to gaskiya galibi ba shi da magani, sai dai a ba wa mutum abinda zai rage masa kaifin matsalar, wanda kuma zuwa yanzu galibi sai dai ƙarfafa gwuiwa, da kuma bin alamun matsalar ɗaya bayan ɗaya bayan sun afku.

Domin karanta bayani a kan Idan Ka ji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] Danna nan

Wato in mutum na jin zazzaɓi a ba shi maganin zazzaɓi, ciwon kai a ba shi maganin ciwon kai, kasala a ba shi maganin sanya kuzari, zafin idanu a ba shi maganin hakan, wato dai symptomatic treatment.

Sai Kuma in abin ya yi tsamari akan bai wa mutum maganin da suke aiki a ƙwaƙwalwa wajen sarrafa yanayin mutum, suke gusar masa da tunanin wannan damuwar inda hakan kan taimaka wasu su riƙa samun jima’i da iyalinsu, wasu kuma akan ba su shawarar tsara irin lokacin jima’in yadda alamomin za su ke zuwa musu da sauƙi.

Amma dai matsalar ba ta da magani zuwa yanzu, amma in an je ga babban likita mutum na iya amfanuwa daga wani tsarin.

Domin karanta Illar Wayar Salula Guda Goma (10) Ga Lafiyar Jiki Danna nan

labarin da ya wuceIllar Wayar Salula Guda Goma (10) Ga Lafiyar Jiki
Labarin na GabaMe Ke Jawo Ƙarancin Numfashi Ga Jarirai Bayan An Haife Su