Mutum Nawa Ne Ake Buƙatar Suga Wata Kafin A Ɗauki Azumi?

0
381

Amsa: Mutum ɗaya idan yaga watan azumi, ya wadartar ga mutanen wannan ƙasar, da mutum ɗayan nan ke ciki kowa ya ɗauki azumi.

Hujja: “Wani Balaraben ƙauye yace: “Ya ga jaririn watan Ramadan”; Sai Manzo ya ce: “Ka shaida babu abin bauta da cancanta sai Allah, ka shaida Allah ne ya aiko ni? “Sannan Balaraben ya ce, “Na shaida”. Sai aka umarci Bilal ya faɗa wa mutane, su tashi da azumi gobe”.

Marawaici Ibn Abbas, littafi Ahamad, Turmuzi, Nassa’i Ibnu Maajah, Abu Dawud.

Domin karanta cikakken bayani akan Akwai Wata Alama Dake Tattare Da Jaririn Watan Ramadan? danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Idan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina, Yaya Azumina Zai Kasance? danna nan.

Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

labarin da ya wuceWane Ne Azumin Ramadan Ya Wajaba Akansa?
Labarin na GabaAkwai Wata Alama Dake Tattare Da Jaririn Watan Ramadan?
Lawan Bello
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.