(Piriton) Ana shan priton sabo da abubuwa da dama, kamar irin su mura, toshewar hanci, ƙaiƙayin jiki da kuma attishawa.
Ana shan priton (1) kullum da rana (2) kullum idan mura ta same ka za ka iya shan priton ko kuma kana fama da ƙaiƙayin jiki, za ka sha priton (1) Kullum a dare kafin kwanciya barci, bugu da ƙari, idan ka yi tafiya a kan abin hawa ko mashin ko mota iska ta bige ka, za ka ji hanci na ƙaiƙayi ko za ka ji kunnanka yana ƙaiƙayi ko ka ji maƙogaronka yana zafi ya bushe ko kuma ka ji kamar za ka yi amai, a irin wannan yanayin da ka tsinci kanka, a lokacin za ka ɗauki priton (1) Tablet ka sha, in ka sha bayan wasu yan lokuta kamar minti talatin za ka ji duk wannan matsalar ta rabu da kai.
(DOKOKI)
Priton yana sa barci ko mutuwar jiki
(1) Idan za kai tuƙin mota ƙar ka sha priton, har sai ka sauka daga titi.
(2) Idan za kai aiki ko na office kar ka sha priton har sai ka dawo gida.
(3) Ba a so a ba wa yaro priton ɗan ƙasa da shekara shida (6)
(4) Idan za ka ajiye priton, kada ka ajiye inda rana za ta daka, ko kuma inda ƙananan yara za su ɗauka.
(5) Sannan mace mai shayarwa idan ɗanta yana ƙasa da wata shida (6).
Kar ta sha priton har sai ta je da su ga likitan dake kusa da ita.
MATSALOLIN CUTARWA KO ILLOLI(SIDE EFECTS)
Yana sa barci mai nauyi. Sannan alamun jin amai yana busar da yawun baki
Ko kuma jiki ya kama tsananin ƙaiƙayi, Kuma yana sa ciwon ciki ko kuma mutum ya fita hayyacinsa ya rasa mai yake.
Wannan ɗan taƙaitaccen bayani ne, kada a manta, duk lokacin da ba a da lafiya, likita ya kamata a tuntuɓa, domin samun magani da ya kama, ba yanar Gizo-Gizo ba. Mun samar da wannan bayinin domin wayar da kan al’umma.