Menene Maganin Ƙazamin Kishi ( Haramtacce)

0
25

Nutsuwa da bin al’amura sannu a hankali na ɗaya daga cikin abubuwan da suke hana faruwar ƙazamin kishi. Bayan haka, addu’a ma babbar makari ce da take maganin ƙazamin kishi. 

An karɓo hadisi daga Ummu-salama (Radiyallahu An ha) ta ce: “Haƙiƙa naji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa “babu wani musulmi da wata musiba za ta same shi ya faɗi abin da Allah ya umarce shi da faɗar sa (wato) face sai Allah ya musanya masa abin da ya rasa da wanda ya fi shi alheri”. 

Ummu-salama ta ce: (yanzu) cikin musulmai wanene yafi Abu salama alheri, farkon mutan gidan da suka yi hijira zuwa ga Manzon Allah? (duk da haka dai) sai na faɗi addu’ar. Sai kuwa Allah ya musanya mini da auren Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Ta ce: “Haɗib ɗan Balta’a Manzon Allah ya aiko wajena ya nema masa aurena. Sai nace da shi (ka gaya masa) ina fa da ‘ya, kuma ni mace ce mai zafin kishi. Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Batun ‘yarta, zan roƙi Allah ya sa mata wadatuwa daga ita, ita kuma zan roƙa mata Allah ya tafiyar mata da zafin kishin da take da shi”. 

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

Muslim da wasunsu suka rawaito shi. 

KO WAƊANNE ILLOLI HARAMTACCEN KISHI YAKE DA SU? 

Haramtaccen kishi yana da illoli kamar haka: 

  1. Jawo wa mai yin sa fushin Allah 
  2. Sa gaba da ƙiyayya fafur ya kuma haifar da fitina gagaruma a tsakanin al’umma. 

An karɓo daga jabir ɗan Atik (Radiyallahu An hu) ya ce: haƙiƙa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:” Kishin da Allah baya so shi ne kishi ba tare da wani abin zargi ba.” Abu Dawud ne ya rawaito shi. 

MENENE MATSAYIN MUMINI MAI KISHI? 

Siffatuwar mumini da halataccen kishi wata gudar alama ce da take nuna nagartarsa da kuma cikarsa. Wannan ya sa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa maza da mata suka shahara da siffatuwa da halayyar kishi. 

An karɓo hadisi daga Mugiratu ɗan Shu’uba (Radiyallahu An hu) ya ce:, sa’adu ɗan Unada (Radiyallah An hu) ya ce: “(Ni kam) da zan ga wani mutum tare da matata, wallahi da na sare shi da kaifin takobina ba da faɗinsa ba.” 

Sai wannan Magana da ya faɗa ta isa kunnen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Sai ya ce:” Kuna mamakin kishin Sa’adu ne? na rantse muku da Allah na fi shi kishi. Ni kuma Allah ya fi ni kishi….”. Muslim ne ya rawaito shi. 

Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu An hu) ya ce (wata rana) muna zaune wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai yace:”

Wata rana ina bacci, sai na ganni a Aljanna, kwatsam kuma sai ga ni ga wata mace tana yin alwala a gefen wani ƙerarren gida. Sai na ce “wannan kuma na wane?” sai ya ce: “Na umar ne”. 

Sai na tuna kishin Umar, sai na juya da baya da baya. (Nan take) a wajan sai Umar (Radiyallahu An hu) ya fashe da kuka. Sannan ya ce: “Ya Manzon Allah yanzu kai zan yi wa kishi?” Bukhari ne ya rawaito shi. 

WANE KISHI NE MAFI BAYYANA? 

A duk kishin da bayi suke yi, babu mafi bayyana da fitowa sarari kamar iri biyu: 

  1. Kishin miji da mata, a tsakaninsu. 
  2. Kishi tsakanin kishiyoyi. 

A bisa misali kan na farko, a baya mun ji cewa, sahabin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbta a gare shi, Sa’adu ɗan Ubada (Radiyallahu An hu) ya ce: “Da zai ga wani mutum tare da matarsa, sai ya sa kaifin takobinsa ya sare shi da shi”. 

Sannan kuma an karɓo daga Abu Mulaika cewa, haƙiƙa Aisha (Radiyallahu An ha) ta ce: “Na rasa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wani dare (da yake da kwana a wajena), sai na zaci ko ya tafi wajan wata daga cikin matansa ne, sai na tafi bincike (da ban same shi ba), sai na dawo. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

Kwatsam sai gashi na ganshi ya yi ruku’u, ko sujjada yana cewa: “Subhaanaka wa bihamdika, la’ilaha illa anta” sai na ce, babana da babata fansarka, kai kana cikin wani sha’ani. Ni kuma ina cikin wani sha’anin daban”. Nasa’I ne ya rawaito shi. 

Don haka, idan mace da miji na ƙwarai ne, basa barin ko-ta-kwana a duk lokacin da ɗayanasu ya ga abokin zamansa yana aikata abin da zai sa Allah ya yi fushi da shi, ko kuma yana shirin aikata rashin gaskiya. 

Dangane da misalin kishin kishiya da kishiyarta kuwa: Imamul Bukhari, Allah ya rahamshe shi ya rawaici hadisi da ke ɗauke da cewa annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi duk lokacin da ya yi sallar La’asar yana shiga wajen kowace ɗaya daga cikin matansa (don sanin halin da take ciki).

To da yake Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mutum ne mai son kayan zaƙi da matarsa Zainab ‘yar Jahsh ta sami zuma, sai take bashi ita ya sha, a duk lokacin da ya shiga wajenta. 

A dalilin haka sai ya zama duk lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya je wajenta sai ya daɗe fiye da yadda ya saba yi. 

Ganin haka, sai Aisha da hafsa suka shirya cewa, duk wadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yaje wajenta daga cikinsu, to, ta ce masa ya sha wani abu mai wari, domin kuwa wari yake yi. 

Da shigarsa kuwa wajen ɗayarsu, sai ta gaya masa haka, sai yace da ita zuma na sha a wajen Zainab ‘yar Jahsh, amma tunda haka ne na rantse da Allah bazan sake sha ba, amma fa kar ki gaya wa kowa dalilin haka. 

Bayan haka sai Allah Ta’ala ya saukar da aya; 

“Ya kai wannan Annabi mai yasa kake hana kanka abin da Allah ya hallata maka domin neman yardar matanka. Allah mai matuƙar yafiya ne mayalwacin jinƙai ne. 

Haƙiƙa Allah ya tilasta muku warware rantse-rantsenku (ta hanyar yin kaffara, wato horo da ya ɗora muku yin sa), kuma Allah ne majiɓincinku, kuma shi cikakken masani ne mai hikima. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

Kuma a yayin da Annabi ya asirta wani zance da wata daga cikin matansa, to, da ta ba da labarin zancen, kuma Allah ya bayyana masa shi, sai ya sanar da sashinsa ya kuma kau da kai daga wani sashe. 

To a lokacin da ya ba ta labari da shi, sai ta ce wane ne ya gaya maka wannan? Sai ya ce, masani wanda ya san komai ne yabani labari, Idan ku biyun kuka tuba zuwa ga Allah haƙiƙa da zukatanku sun karkata idan kuwa kuka tarar masa, to haƙiƙa Allah shi ne mataimakinsa da Jibrilu da muminai salihai, kuma mala’iku ma bayan haka mataimakansa ne”. 

Sannan kuma Imamun Nasa’I ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Anas da kuma Ummu-salama (matar Annabi) cewa ita Ummu-salama ta kawo wa Annabi da sahabbansa abinci a mazubinta (a ranar kwanan Aisha) sai ita kuwa Aisha ta tanƙwabi hannun, sai mazubin ya faɗi ya dare gida biyu.

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Sai Annabi ya haɗa tsagi biyu na mazubin ya kuma tattara abincin a cikinsa, sannan ya riƙa cewa sahabbansa: ku ci babarku ta yi kishi, ku ci babarku ta yi kishi. 

Sai sahabbai suka ci, Annabi kuma sai ya bar wannan fasasshen mazubin a wajensa har sai da Aisha ta zo da na ta mazubin sai ya aika wa Ummu-Salama da shi.Sannan kuma ya bawa Aisha fasasshen mazubin da ta fasa wa Ummu-Salama”. 

Sannan kuma dai an karɓo hadisi daga Ummu-Salama cewa, sauran matan Annabi tsira da amincin Allah tabbata a gare shi maganar cewa, su fa basu gane ba, mutane na kintatar ranar kwanan Aisha su aiko wa Annabi tsira da amincin Allah tabbata a gare shi da kyauta, ai su ma suna son alheri kamar yadda Aisha take so. 

Da ranar Ummu-Salama ta zo kuwa; sai ta gaya wa Annabi tsira da amincin Allah tabbata a gare shi hakan. Sai Annabi ya yi shiru bai ce komai ba. Da ranar kwananta ta sake kewayowa, sai ta sake yi masa wannan magana, sai ya kuma yi mata shiru bai ce da ita komai ba. 

Su kuma sauran matan sai suka tambaye ta cewa: Wace amsa Annabi tsira da amincin Allah tabbata a gare shi ya ba ta? Sai ta ce da su, bai ce da ita komai ba. Sai suka ce da ita, to, kar dai ki ƙyale shi; har sai (ya magantu) ya ba ki amsa. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Da ranar kwananta ya kuma kewayowa, sai ta sake yi masa wannan maganar, sai Annabi tsira da amincin Allah tabbata a gare shi ya ce: “kada fa ku cutar dani a game da Aisha. Duk cikinku fa babu wacce aka taɓa yi mini wahayi a halin ina rufe da mayafinta in ban da Aisha”. Bukhari da Nasa’i ne suka rawaito shi. 

Abin nufi da wannan amsa da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya basu; shi ne, idan har suna so su nuna kishinsu kan Aisha, to su yi shi a kan bin da shi ya yi mata; ba a kan abin da wasu can daban suka yi mata ba. 

Idan sun ce don me mutane suke yi masa abin alheri a ranar kwanan Aisha; to kuma mai za su ce game da wahayin da Allah ya yi masa yana lulluɓe da malulluɓin Aisha? Amma kuma bai yi masa wahayi a yana lulluɓe da malulluɓin wata daga cikinsu ba.

Idan har ba su da ta cewa game da batun wahayin da Allah ya yi masa, to bai kamata kuwa su matsa masa a kan abin da sahabbansa suke yi masa a ranar kwanan Aishan ba. Tun da dai bashi ya ce da su idan za su yi masa abin alheri su keɓe ranar kwanan Aisha su yi masa ba. Wannan ke Nan. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMenene Bambanci Tsakanin Kishin Allah Da Na Bayinsa?
Labarin na GabaShin Ko Kishi Yana Hana Faɗar Gaskiyar Kishiya?