Mace zata iya fara yin amfani da magungunan tazarar haihuwa kafin ta fara yin al’adarta, ko lokacin da take yin al’adarta, ko bayan ta gama yin al’adarta. Tasirin magungunan wajen hanata daukar juna biyu, ya danganta ne da nau’in maganin. Amma magana ta gama-gari ita ce anfi bayarda shawarar fara yin amfani da magungunan a cikin kwanakin farkon fara yin al’adarta. Ga bayanin yadda rabe-raben yake:
ƘWAYOYIN MAGANIN TAZARAR HAIHUWA MASU ƘUNSHE DA HAƊAKAR SINADARAN ESTROGEN DA PROGESTERONE (COMBINED ORAL CONTRACEPTIVE PILLS – COCs)
Ƙwayoyin maganin tazarar haihuwa masu haɗuwar hormones kamar Microgynon, Yasmin, ko Nordette, suna daga cikin magungunan hana ɗaukar ciki waɗanda mata suka fi yin amfani da su. Waɗannan ƙwayoyin suna ɗauke da sinadaran estrogen da progestins. Idan mace ta fara shan waɗannan ƙwayoyi a cikin kwanaki biyar na farkon jinin al’adarta (rana ta ɗaya da fara jinin al’adarta), za ta sami kariya daga ɗaukar ciki nan-take.
Wannan yana faruwa ne saboda sinadaran da suke cikin ƙwayoyin suna fara yin aiki nan-take wajen hana fitar ƙwan haihuwa (ovulation). Amma idan ta fara shan ƙwayoyin bayan kwanaki biyar da fara jinin al’adarta, to, riga-kafin ba zai yi aiki nan-take ba, kuma dole ne sai ta ƙara da yin amfani da wata hanyar kariya kamar kwaroron roba (condom) har tsawon kwanaki bakwai, domin ƙwayar maganin tana ɗaukar lokaci kafin ta fara aiki.
ƘWAYOYIN MAGANIN TAZARAR HAIHUWA MASU ƘUNSHE DA SINADARIN PROGESTIN KAƊAI (MINI PILLS)
Ƙwayoyin tazarar haihuwa masu progestin kaɗai, kamar Cerazette, Micronor, da Noriday, suna da bambancin fara yin aiki idan aka kwatanta su da ƙwayoyi masu haɗakar sinadaran estrogen da progestin, saboda progestin kawai suka ƙunsa. Idan mace ta fara shan waɗannan ƙwayoyi a ranar farko da ta fara jinin al’adarta, to, za ta sami kariya nan-take.
Amma idan ta fara shan su bayan ‘yan kwanaki da fara al’adarta, to, dole ne ta yi amfani da ƙarin wata hanyar kariya idan za ta yi jima’i har sai bayan tsawon awoyi 48 (kwanaki biyu) don tabbatar da samun kariya daga ɗaukar juna biyu, saboda ƙwayoyin suna buƙatar lokaci kafin su fara yin tasirin hana mace samun juna biyu ta hanyar hana ta saka ƙwan haihuwa (ovulation) da kuma sanya kaurin bangon mahaifa.
MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA NA NA’URA (HORMONAL INTRAUTERINE DEVICES – IUDs)
IUDs waɗanda suke ƙunshe da sinadaran estrogen da progesterone, su ne kamar Mirena da Skyla. Wannan na’ura ce da ake sanyawa a cikin mahaifa don samar da kariya daga ɗaukar juna biyu na dogon lokaci, kamar shekaru uku zuwa biyar. Idan mace ta sanya IUD a lokacin da take yin jinin al’adarta, musamman a cikin kwanaki bakwai na farkon al’adar, za ta samu kariya daga ɗaukar ciki nan-take.
Amma idan an sanya mata IUD a wani lokaci daban ba wannan ba, a zangon jinin al’adarta (menstrual cycle), dole ne sai ta yi amfani da wani ƙarin hanyar kariya kamar kwaroron riba (condom), har na tsawon kwanaki bakwai kafin na’urar ta fara aiki.
ALLURAI NA TAZARAR HAIHUWA (CONTRACEPTIVE INJECTIONS)
Allurai na tazarar haihuwa kamar Depo-Provera ko Sayana Press wasu hanyoyin tazarar haihuwa ne masu ƙunshe da sinadaran estrogen da progesterone da ake bayarwa ga mace a duk bayan watanni uku. Idan aka yi wa mace allurar a cikin kwanaki biyar na farkon zangon jinin al’adarta (menstrual cycle), to, za ta sami kariya daga ɗaukar juna biyu nan-take. Amma idan aka yi mata allurar a wani lokaci na daban, to, dole ne sai ta yi amfani da wata hanyar samun kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai domin allurar ta fara aiki.
DAN-MAƘALE NA TAZARAR HAIHUWA (CONTRACEPTIVE PATCH)
Ɗan-maƙale, wato faski, na hana ɗaukar ciki, kamar Ortho Evra ko Xulane, wani ƙaramin abu ne da ake manna shi a fatar jiki wanda yake sakin sinadaran estrogen da progesterone zuwa cikin jiki. Idan mace ta manna wannan faski, a rana ta farko na jinin al’adarta, za ta sami kariya nan-take. Amma idan ta manna faski bayan jinin al’adarta ya yi kwanaki da farawa, to, dole ne sai ta yi amfani da wata hanyar kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai kafin faski ɗin ya fara aiki da kyau.
Don karanta dalilan da ke kawo rashin haihuwa danna nan
ZOBEN FARJI (VAGINAL RING)
NuvaRing wani sassauƙan zobe ne da ake sakawa mace a cikin farjinta don sakin sinadaran estrogen da progesterone a cikinsa. Idan mace ta saka zoben nan a rana ta farko na jinin al’adarta, to, za ta sami kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Amma idan ta saka shi a wani lokaci daban a cikin zangon jinin al’adarta, to, dole ne sai ta yi amfani da wata hanyar kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai kafin zoben ya fara aiki da kyau.
ASHANAR HANNU (CONTRACEPTIVE IMPLANT)
Ashanar hannu, kamar Nexplanon, dabarar tazarar haihuwa ce, mai kama da ƙaramar sanda wacce ake saka ta a ƙarƙashin fatar hannun mace ta sama. Tana sakin sinadarin progestin ne domin hana ɗaukar ciki na tsawon shekaru 3 ko fiye. Tana hana saka ƙwan haihuwa, kaurara majinar bakin mahaifa don hana ‘ya’yan maniyyi shiga, sa’annan tana ƙara kaurin bangon mahaifa don hana ƙyanƙyasasshen ƙwan haihuwa maƙalewa a jikin bangon mahaifa.
Idan aka saka ashanar hannu a cikin kwanaki biyar na farkon jinin al’ada (Rana ta 1 ita ce ranar da jinin al’ada ya fara), tana bada kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Idan kuwa aka saka ta bayan kwanaki biyar da fara al’adar, to, dole ne sai mace ta yi amfani da wata hanyar kariya, kamar kwaroron roba, na tsawon kwanaki bakwai, har sai allurar ta fara aiki sosai.
ME YA SA LOKACIN FARA AMFANI DA MAGUNGUNAN YAKE DA MUHIMMANCI?
Lokacin da ake fara amfani da magungunan tazarar haihuwa yana da matuƙar muhimmanci don samun cikakkiyar kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Fara amfani da su a lokacin ko bayan mace ta fara yin jinin al’adarta yana taimakawa wajen daidaita tsarin jikin mace na halitta, yana rage haɗarin fara amfani da su yayin da ba a san tana ɗauke da ciki ba, kuma yana bayar da kariya da wuri. Idan an fara amfani da su bayan jinin al’adarta, yawanci za a buƙaci yin amfani da wata kariya (na kwanaki bakwai) don jikinta ya daidaita da hormones.
Domin karanta bayani akan ciwon ciki da mara lokacin al’ada danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu