Likita Ina Neman Taimako Haɗe Da Shawara Game Da Matsalar Ƙanƙantar Azzakari [Micro Penies]

0
15

Wannan na Daga tarin tambayoyin gami da ƙorafin da ako yaushe nake samu daga wasu cikin maza nasha kau da kai garesu, tare da ɗan tsaga bayani kadan cikin wasu rubututtukan nawa, amma dai a yanzu abun yayi yawan da dole na fito nai bayani a iya kan wannan matsalar kurum. 

Haƙiƙa daga sanda mutum ya fara jin cewa anragesa ta wannan ɓangaren toh mataki ne da zai kai mutum ga rasa self confidence dinsa na namiji, yana kuma iya kai mutum ga damuwa da fargaba na ba gaira babu dalili wanda zasu dabaibaye sa haka kurum. 

Sai dai kaso sama da 80% na masu irin wannan tunanin azzakarinsu yakai tsaikon da akeso wanda ya dace da halittar su, zubin su da halaiyarsu dai dai da na kowa kurum ganin kitse suke wa roogo! Amma a zahiri ƙalau suke.

Azzakari na fara girma ne jikin namiji daga shekara 11 sannan ta kammala girmanta zuwa 18yrs daga nan ta cika girman ta, don haka galibi daga shekara 20 shikenan kurum abunda ka ganka dashi shine abunda Allah ya baka na tsayi bazaka ƙara ba,domin kamar tsayi ne, daga shekara 21 shima ka gama tsayin da duk zakai. 

ƙwata-ƙwata adadin masu fuskantar ƙanƙantar gaba a duniya wato Micropenis shine 0.015% cikin 100,wanda ke nuna kaso 99.85% duk azzakarinsu yakai tsaiko saide rashin godiyar Allah

Ina So Baki Daya  Kusani

A jima’i bunkice na masana game da azzakari an tabbatar da:

  • Mafi ƙanƙantar azzakari da inkana da shi shine zaka zargi kanka da matsalar ƙanƙantar gaba shine inya gaza kaiwa 3.6 inches ƙwatanƙwacin 9.16 centimeter sanda sha’awa ta kama mutum ya miƙe. 
  • Yayin da average wato tsayin da Allah aƙallah kusan kowa inde yakai toh babu zancen matsala shine: wanda yake (3.66 Inches wato 9.3centimeter) Idan an auna tsayin a sanda yake kwance wato flaccid kafin Erection, da kuma kaiwa tsawon 5.16 inches wato 13.12cm centimeters a sanda ya mike…. Wato Erection yayin sha’awa. 
Sharaɗin Kiyayewa 

Kafin gwajin ya kamata kowa ya sani yanayin wheather musamman lokacin sanyi ko yanayin zafi a inda yake da na’urar sanyaya ɗaki (AC) suna da tasiri wajen sanya shi ya kuɗe ciki don haka yanayin dumi shine zai sa a sami awo me kyau. 

Hakana tasa wasu kanga gabansu karami amma ba a nan abun yake ba domin galibi inya miƙe su kansu suna ganinsa da girma musamman a masu masturbation saboda takurarku ce tasa fata ɓoyesa… don haka wannan normal ne babu buƙatar damuwa don ya kasance ƙarami amma in sha’awa ta taso kai achieving Erection ka gansa yakai girman sa. baka da buƙatar ka dami kanka… 

Kamar yadda nace lokuta musamman na sanyi azzakari yakan ɓoye kansa ciki saboda canjin temperature.

Ba Ƙasa Da Ido Ake Akalli Azzakari Ba

Idan kana so ka gane tsayin azzakarinka bawai yadda kake ganinsa da ido bane,a’a ka bari saika fito wanka ko kuwa yanayi me kyau saika sami irin ƙaton Mirror dinnan wato madubi saika tsaya ka dora hannuwanka a ƙugunka kai poster asannan ne zaka gane zahirin tsayin azzakarinka sanda ya zamto kansa na pointing din kasa. 

A sannan ne in zaka auna saika sa ruler dinka ko tape dinka irin na awon teloli ka ɗora daga tushenta na gashin gabanka (BASE) zuwa Karshen penis glands din wato wajen fitrr fitsari (TIPS) saika kaga numba nawa ka samu shine zai zamto tsayin azzakarinka 

Kuma anfison gwajin ne sanda azzakari yake a miƙe wato aka sami Erection fiye da inyana kwance inkaga ya mike yayi kasa da 9.1centimeter (cm) Toh sannan ne zaka ce kana da kankantar azzakari wanda kuma galibi ɗan Nigeria ya wuce hakan. 

Idan Muka Duba Kididigar Duniya Gaba Ɗaya

A kwai Bayanai da shafin bayanai (WORLD DATA) suka fitar bisa survey da sukai na jerin kasashen duniya tun daga kasar da mazajenta suka fi tsayin azzakari zuwa mafi kankanta, inda kasar ECUADOR  itace kasar da mazajenta suka fi ko ina tsayin jela da murabba’in AVERAGE tsayin da yakai 17.61 centimeters,sai Kasar CAMEROON,BOLIVIA da SUDAN matsayin na 2, na 3 dana hudu,yayin da Kasar CAMBODIA itace average na tsayin jelar yan kasarta 10.04centimeter,yayin da Kasar Nigeria  ke matsayin ta 43 a duniya da mazajenta keda AVERAGE na tsayin azzakari da yakai 14.38cm centimeter. wanda a hakan ma nasan muna da mazaje masu yawa da azzakarinsu yakai tsayin na wasu yan kasar Ecuador din wato 17cm +

Sannan binkice ya nuna fiye da kaso 85% sun nuna gamsuwarsu da yadda duk azzakarin namiji yake matsayinsa na Average, in fact tsayin azzakari ba shine jima’i ba, iya sanin kalar mace da yadda zaka sarrafa ta ka tattabata Shine ke bada gamsashhen jima’i, wasu magana a kunne yayin jima’i shi ke gamsar dasu.

Don haka babu bukatar kuje kuna kashe kanku, kuna sa kai a damuwa ba gaira babu dalili, ko kuita shaye shayen magungunan da ba zasu amfane ku da komi ba.

Mudai  likituci bamu da wani magani da sunan na ƙara tsayin azzakari, ko surgery shima babu, saide ai wanda za’a katsewa mutum majanyen dake rike da azzakarin acan tushen sa wato ligament domin ta zazzago shine ma wasu suke samun abu me ɗan nauyi su daura akanta suna tafiya yana lilo wai duk don ta zazzago…

Haka ko advance surgery saide ya zamo cosmetic kurum kaga ina lafiya ace azzakari sai ansaka mara roba da sunan implant antsai dashi kullum ahaka duk da ba kowa ma ake wa hakan ba sai wanda rashin tsayin ya amsa rashin tsayi. 

Yana dakyau ku shiga nan domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki

Fina Finan Batsa Da Maganganun Batsa Basa Komai Sai Lalata Tunani 

Kamar yadda nasha fada sau tari kalle-kallene na finafinan batsa ke jawowa, wanda kuma na fada muku duk wannan ba azzakarin gaskiya bane, hatta abunda zakuga ana fitarwa matsayin maniyyi wallahi ba maniyyi bane artificial cream ne aka haddasa… Wanda yake turosa da syringe yake amfani boye kansa yake bayan camera man, Akalla ka sami mutum 12 acikin dakin da ake shutting na porn, shiyasa komi zakaga perfect…

Yau zan tabbatar muku da hakan a link din da nasa muku karshen wannan post din, zai kaiku YouTube kuga yadda suke hada pronographic scene din.

Sai kuma lalacewar tarbiya da karanci kunya domin mata a yanzu sune kan gaba wajen ƴaɗa batsa ako ina, zakai takaici kaga irin abunda ƴaƴan mu, kannen mu ke videos akai suna dorawa a YouTube da sunan koya jima’i don neman kudi, ko kuma kaga ankirkiri group a Facebook da WhatsApp ana mata zallah amma ɓarnar da suke kare ma bazai ci ba.

Ahaka duk sai suzo suyita tattauna hatta abinda ke faruwa a shimfida saboda rashin mutunci na wasu matan, kaji abubuwan ƙarya da gaskiya wasu suji kuma su hau kai su zauna, daga ranar ta fara ganin gazawar mijin ta, ko ta kalli porn ta dauka duk gaskiya ne, mijin ta da bashi da kaza ko baya iya minti kaza suna jima’i ba lafiyar sa ƙalau ba. 

Wani Abu Da Baku Sani Ba Shine 

Shifa farjin mace baki Dayan Sa FLEXIBLE ne, babu wata mace wai ita dunduɓus kurum saidai in infection gareta, amma Allah ya tsarasa ne yasa masa transitional epithelium da duk yadda namiji yake zai daidai dashi inya sanya gabansa, kamar roba ne, yana talewa, ya tsuke, ko ɗame,

Average na zurfin farji wanda galibi bai wuce wa shine 10centimeter fiye 90% na mata haka suke, kai me average 14cm Ka gayan ina zaka shigar da ragowar 4cm din cikin 10cm?

Ni’imar Allah sakamakon can gaba bakin mahaifa ne shiyasa koda ka kai 17cm din ma kana iya jin ka shige baki daya domin hakan zai kusata tips din penis dinka ga bakin mahaifa shiyasa inda rabon ciki kana yin release shikenan maniyyinka zai nemi hanya ya shige cikin mahaifar cikin sauki.

Wannan bayanin zai zamto mabuɗin idanu ya zamto adena rudarku da porn ko zantukan shirme, lafiya ƙalau kuke, ku mance da masu karanta muku wani ya ake kwanciya… duk suma a finafinan batsa suke kawo muku wanda duk karya ne galibi ba abunda kuke gani bane.

Allah ya taimake mu, ya shirya mana zuri’a baki ɗaya amin.

Domin karanta Meyasa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Yana Fitowa  Kafin Ko Bayan Sanin Period Din Su? Danna nan

labarin da ya wuceMeyasa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Yana Fitowa  Kafin Ko Bayan Sanin Period Din Su?
Labarin na GabaToshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki