Ina Bada Nono Amma Baya Isar Jaririna, Ko Kuwa Ba Maiƙo

0
22
  • Ina da ƙarancin ruwan Nono
  • Ina da ruwan nono a wadace amma baya ƙosar da yaro na, babu maiƙo
  • Ta ya zan gane yaro na na ƙoshi
  • Ina son shayarwa tsawon shekara biyu saidai surutun mutane ne ke mun yawa
Ina Mafita? 

Kamar yadda nasha faɗa babban abinda kesa ruwan nono tsatstsafowa shine yawan dora yaro a nono,gwargwadon yawan shayarwa gwargwadon yawan yadda za’a rika cikowa yana tuttudowa,shiyasa nace ko larurar tasa ana ba yaro madara to akwai ribar da ake biyowa da ita ta jikin kan nono ya zamto sanda yaro ke tsotso madarar yana tsotso kan nonon hakan zai stimulating ruwan nonon ya fara zuwa… ko wacce bata haihu ba aka cika stimulating nononta karshe zai kawo ruwan nono ballantana me jariri,sannan sanya me gida ma ya rika stimulating dinsa nan ma zai taimaka wajen zuwansa

Sai kuma iya saita yaro kan nono shima wani abu ne: domin da yawa basu ma iya shayyarwa ba,zaka sami mace haihuwarta wajen shida amma a aikace bata iya dora yaro akan nono yadda zai sha ya koshi ba,itama taji dadin shayarwar batare da jin zafi ba. sannan ba yawan ruwan nonon ne ma’aunin cewa yaro baya samun isashshe ba a’a kaɗan me amfani,quality shine bawai quantity ba.

Domin karanta bayani akan Zubar Jinin Haila Sosai Fiye Da Ƙima wato “Rushing” [Heavy Bleeding] Danna nan 

Akwai Ruwan Nono Amma Ba Maiƙo

Still dai zan maimaita samun maiko a nono ya ta’allaƙa ne ga yawan shayarwa da kuma tsawon lokacin da aka dauka ana shayarwar,a duk sanda jariri ya zuƙe nonon toh hakan ke sa hauhawar kitsen a ciki,shi ruwan nono hawa uku ne, na farkon dake zuwa ma yaro ruwa ne da kuma carbohydrate wato sugar dake bada kuzari amma ba gina jiki ba wato (FORE MILK)

Toh yana zuƙe fore milk shine nono mai kunshe da kitse da sinnadarin protein dake gina jiki (HIND MILK) zata biyo baya… 

Toh galibin kuskuren sanda Hind ke dab da fara zuwa sannan iyaye ke canzawa yaro nono zuwa na daya ɓangaren wanda ƙarshe sai ya zamto an maida shi baya wato fore milk dai zai kuma sha,yana shanyewa cikinsa dama ya cika shikenan sai ya zamto shayarwar baki daya nono kala daya ya samu,me sugar mara maiko…kafin anjima kuma fore milk ta qara taruwa ta maida hind kasa tunda HIND tafi kauri kamar yadda gasara ke kwanciya kasa.

(1) Don haka matakin farko akalla sai yaro yai minti 15 akan nono guda daya kafin HIND MILK ta fara zuwa masa,don haka ba damuwa bane abar yaro yasha nono daya,ba dole ne sai yasha kowanne a dukkan zama ba. 

Domin karanta bayani akan Vaginal Infection shiga nan

(2)  Za’a iya ake amfani da breast milk pump ki zuƙesa,akalla na tsawon minti 4 zuwa 5 saiki dora yaron akai nan da nanan zai zamto Hind milk tazo masa.

(3)  Hakazalika niƙa garin waken suya arika damawa ana kununsa ana sha zai taimakawa mace,ana iya soya waken suyan ko aniƙo garinsa a haka,sannan hulba na taimkawa in aka sarrafata ta kowacce hanya duk wadannan lactogens ne.

(4)   Cin abinci masu protein irinsu kifi,awara,naman kaza,ƙwai da sauran su na taimakawa.

(5)   Sai nutsuwa da hutun jiki,bada nono a sanda aka gaji likis kan hanasa zuwa a wadace koda ace akwai san.

Taya Zan Gane Yarona Na Ƙoshi

Ko daga bacci ya farko karki bashi ruwa sai nono,za kuma ki gane yana ƙoshi ne ta hanyar yawan fitsari,da yawan jiƙe pampers tare da jin yana ƙara nauyi,sannan bayan ya sha nono ke da kanki zaki ji nonon ya rage nauyi ba kamar kafin ya sha ba.

Surutu Ne Ke Hanani Dogowar Shayarwa

In kikaga wata na magana kan nonon ki ko yaron ki ya girma ki yayesa tun farko bada fuskar hakan kikai,akwai matan da baka isa kace kaga sanda suke ba yaro nono ba,koda cikin mata yan uwansu…toh bakasan ma suna yi ba ballantana kai zancen sunƙi yaye yaro,don haka toshe wannan ɓarakar ta hanyar rashin bada fuska da sakayawa sanda ake ba yaro nono sune mafita

Domin karanta bayani a kan post injection inflammation: {kumburi bayan anyi allura} ko mataki  domin kare kanka daga kamuwa da ciwon ƙoda ko abubuwa wanda ya Kamata mace ta kiyaye lokacin al’ada danna wannan koren rubutun

Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

labarin da ya wuceZubar Jinin Haila Sosai Fiye Da Ƙima wato “Rushing” [Heavy Bleeding]
Labarin na GabaPost Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura}