Akwai hukunce-hukunce da dama da suka shafi ƙananan yara masu yawa waɗanda ya wajaba ga iyaye su san su tun kafin yin aure da samun cikin yaron.
A bayanin da ya gabata an taɓo wasu daga cikin waɗannan hukunce-hukunce, ɗari a kansu shi ne:
1) Ya halatta a huda kunnen mace sabo da ado duk da cewa za ta ji zafi.
2) An fi so a yi wa namiji kaciya tun kafin ya fara jin kunyar tsiraici, waɗansu malaman suna ganin ya kamata a yi wa yaro kaciya ranar bakwai.
3) Kaciyar mata ba wajibi ba ce, in akwai matsala ya kamata a bar ta.
4) An yi sauƙi a yayyafa ruwa a kan fitsarin ƙaramin yaro da ba a yaye shi ba, amma na jaririya sai an wanke.
Domin karanta cikakken bayani a kan Hukunce – Hukuncen Raino danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar ( Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.