An karɓo Hadisi daga A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Na ce wa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Kaza-da-kaza ya ishe ka game da Hafsa”.
Tana nufin gajartarta. (inji mai ruwaya). Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam) ya ce: “Haƙiƙa kin faɗi kalmar da inda za a gauraya ta da ruwan kogi da ta gurɓata shi (saboda muninta)….”. (Abu Dawud da Tirmizi ne suka ruwaito shi).
Kuma an karɓo Hadisi daga Abu Bakrata, Allah ya yarda da shi, ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “A hajjinku da cin dukiyoyinku da cin mutuncin junanku, haramun ne gare ku….”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).
Kuma Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce:
“Kada waninku ya yi da wani…” (Hujrat,12)
Kamar yadda ya ce:
“Kada wasu jama’a su yi isgili ga wasu”. (Hujrat, 11)
Kuma an karɓo hadisai daga Abu Musa, Allah ya yarda da shi, ya ce: “Na ce ya Manzon Allah! Wane ne mafificin Musulmi? Ya ce: “Wanda Muslimai suka kuɓuta daga cutar harshensa da ta hannunsa”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan