Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

0
25

Majaddid shaihuna Usman ɗan Fodiyo Allah ya ƙara rahama a gare shi, ya rubuta littafi mai suna; Usulul adli liwalatil umuri wa ahlil fadli- wato Ginshiƙan kafuwar adalci domin shugabanni da manyan mutane.

A cikin wannan littafi, ya yi bayanin hanyoyi goma waɗanda in dai shugabanni daga sama har ƙasa za su bi su, babu makawa za su kasance masu adalci a shugabancinsu. A taƙaice ga waɗannan ginshiƙai; 

TUSHE NA ƊAYA 

Shugaba ya san matsayi da darajar shugabanci da yake yi. Ya sani cewa shugabanci ni’ima ce babba wacce in ya yi gaskiya da adalci za ta kai shi ga samun ni’ima madawwamiya a lahira da kyakkyawan suna a duniya.

Idan kuwa aka samu akasi to zai gamu da matsananciyar azaba a duniya da lahira saboda haka kada ya yi wasarere da shugabanci ya riƙe shi ƙam ƙam ya yi da gaske ba wasa. 

Domin karanta bayani akan Mutuwa Da Rabon Gadon Bahaushe Danna nan 

TUSHE NA BIYU 

Lallai ne shugaba ya ja malamai masu tsoron Allah da aiki da iliminsu masu son alhairi ga al’umma masu faɗar gaskiya marasa tsoro marasa kwaɗayi. 

Ya ja su a jikinsa ya rinƙa neman shawarwarinsu da fatawa akan al’amuran shugabancinsa, ya kuma rinƙa amfani da shawarwari da nasihohi da suke yi masa. 

Haka kuma ya nemi masana ƙwararru a kowane fanni na rayuwa kamar manyan ‘yan kasuwa, tsofaffin shugabanni, da ma’aikata na kowane ɓangare dattawan gari har ma da matasa maza da mata masu tsoron Allah da kishin ƙasa domin ya amfana da iliminsu da ƙwarewarsu a fannonin rayuwa da sauransu. 

TUSHE NA UKU 

Kasancewarka mai gaskiya da riƙon amana da adalci ba zai kuɓutar da kai ba a wurin Allah sai ka tabbatar mai ma’aikatanka da jami’an gwamnatinka suna da hali irin naka. Amma idan kana ganin ɓarna ka yi shiru, to haƙiƙa sai ka ba da amsa akan wannan ɓarnar , kuma sai an tuhume ka akan duk ɓarnar da aka yi kana sane ka yi shiru ayi maka azaba a kanta ranar ƙiyama. 

Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan 

TUSHE NA HUƊU 

Lallai ne shugaba ya kasance mai yawan haƙuri afuwa da kau da kai ya guji saurin fushi da yanke hukunci cikin ɓacin rai.

TUSHE NA BIYAR 

A duk lokacin da za ka ɗauki wani mataki ko yanke hukunci ko shawara ko sanya hannu akan wani ƙudiri waɗanda suke ƙarƙashinka ka ɗauki kanka a matsayin ɗaya daga cikin talakawa duk abinda ba za ka so a yi maka ba to kada ka yi wa waninka, duk abinda za ka so ayi maka to ka zartar da shi. 

TUSHE NA SHIDA 

Kada ka wulaƙanta talaka da sauran mutane masu kawo buƙatunsu gare ka da koke-kokensu, saboda babban amfanin shugabanci shi ne sharewa mabiya hawayensu da sauran buƙatunsu da yin abinda ya kamata akansu. 

TUSHE NA BAKWAI 

Ka yi rayuwa matsakaiciya tare da tsantseni da wadatar zuci kada ka sabawa kanka da zurfafawa da al’mubazzaranci a wajen jin daɗi da kece raini wannan zai sa ka mance da wahalhalun da talakawa suke ciki zuciyar ka ta bushe, in suna kuka ka rinƙa jin kamar kukan daɗi suke yi. Kana sheƙa dariya abinka. 

TUSHE NA TAKWAS 

Dukannin abinda zai yiwu cikin sauƙi da lumana, kada ka bi hanyar tsanani ne da tursasawa wajen tabbatar da shi. Ana amfani da tsanani kawai a lokacin da sauƙi ba zai yi amfani ba. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

TUSHE NA TARA 

A kowane lokaci ka rinƙa tunanin mutuwarka da kwanciyar ƙabari da tashin alƙiyama da musiba da azabobin da suke cikinta, da kuma ni’ima da rahamar da Allah ya tanada ga masu binsa. Ka rinƙa tunanin shin kai a wane ɓangare za ka kasance idan Allah ya tashi alƙiyama.

TUSHE NA GOMA 

Ka sanya tsarin shugabanci na Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance madubinka, ma’aunin shugabancinka ka rinƙa kwaikwayonsa gwargwadon ikonka. Bayan waɗannan tuwassa goma waɗanda Shaihu Usman ɗan Fodiyo ya ambata ya kuma ce imamul Gazzali ne ya faɗe su a cikin wani littafinsa, sai kuma ya kawo waɗansu muhimman abubuwa guda takwas waɗanda Shaihu Muhammad bin Abdulkarim Almagili ya faɗe su cikin wani littafinsa. 

Abubuwan Su ne; 

1) Ya kai shugaba ka miƙa dukkanin al’amuranka ga Allah shi kaɗai, ka dogara da shi ka nemi taimakonsa duk abinda za ka yi ka yi shi saboda Allah, ka sani kai ma fa ɗaya ne daga cikin halittunsa kuma mafi yawancinsu sun fi ka ƙarfi ba don mulkin da Allah ya ba ka ba, ai da babu yadda za ka yi iya ka domin kyautata rayuwar mabiyanka da addininsu ka godewa Allah kada ka fitar da rai da samun rahamarsa da magance duk wata matsala da damuwa da ake ciki. 

2) Ka ƙawata zahirinka da baɗininka domin ka kasance mai kwarjini da ƙima. Ka rinƙa yin shiga ta kamala da ado wanda bai saɓawa shari’a ba. Ka so alhairi da masu son alhairi ka ƙi sharri da mugunta da masu aikata su ka kasance cikin nutsuwa, in za ka yi magana ka faɗi gaskiya, in ka yi alƙawari ka cika, ka rinƙa bibiyar dokokin da ka kafa da umarnin da ka bayar ka tabbatar ana aiki da su. Duk wanda za ka ja shi a jiki ko za ka naɗa shi wani muƙami ka tabbatar mutumin kirki ne mai kwarjini da gaskiya da amana. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

3) Ka tsara gwamnatinka tsaf, duk wanda za ka naɗa wani muƙami ko ka ba shi wani aiki ka tabbatar ya cancanta kuma yana da nagarta da tsoron Allah. Ka tabbatar ka zaɓi mashawarta da jami’an tsaro da alƙali da sakatarori da malamai da jami’an lafiya da masu tsara harkokin tattalin arziƙi da sauransu. Ƙwararru managarta. 

4) Ka kasance mai tsananin kulawa da taka tsantsan wurin abincinka da tufafinka da makwancinka a halin da kake a gari da lokacin da ka yi tafiya, kada ka bari wani ya kusanci waɗannan al’amura naka sai cikakken masoyinka amintacce wanda ba ka da ko ɗar a kansa, wanda zai iya rasa ransa akanka.

5) Ya wajaba ya rinƙa bibiya da binciken al’amura da kansa, ya rinƙa bincikar duk abinda bai sani ba na halayen mutanen da ya damƙa amana a hannunsu, da ma’aikatansu. Ya sami amintattun masu leƙen asiri da kawo masa labarin halin da gari da mutane suke ciki. Ya guji sauraron annamimai masu kawo tsegumi da soke soken mutane da ƙungiyoyi. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

6) Ya wajaba shugaba ya bai wa kowa haƙƙinsa, ya kyautatawa kowa, kada ya fifita wani akan wani, kada ya ɗau haƙƙin wani ya bai wani. Ya ba da dama ga masu rauni su rinƙa ganinsa suna isa masa da koke-kokensu ya saurare su, ya kyautata musu ya yi musu taimakon da ya wajaba. 

7) Ya kula da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ya tabbatar ta hanyar da Allah ya yarda ne kaɗai ake samunsu kuma ana sarrafa su ta hanyar da ya yi izini. Ya guji karɓar rashawa da cin hanci da kyaututtuka daga mabiyansa musamman waɗanda babu wata alaƙa ta kusa tsakaninsa da su kafin ya samu wannan shugabancin. 

Haka kuma ya guji zaluntar mabiya ta hanyar kwace musu dukiyoyinsu da kadarorinsu ko ƙuntata musu hanyoyin samun su ba tare da wani dalili na shari’a ba. Kada ya tare kuɗi ya taskance su yamatse hannu alhali al’umma suna cikin matsi da ƙunci da wahala. 

8) Kula da dukiyoyin Allah kamar zakka, da ganima ya sarrafa su ga wanda Allah Ta’ala ya yi umarni a sarrafa ta gare su. 

Daga ƙarshe addinin musulunci ya tabbatar da ƙa’idojin tabbatar da adalci musamman kan abinda ya shafi shari’a da ɗangantaka tsakanin alƙali da mai ƙara da wanda ake ƙara. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

Ga waɗansu dunƙulallun jumloli akan wannan gaɓa; 

1) Asalin kowa mara laifi ne har sai an tabbatar da laifinsa. 

2) Wanda ya kai ƙara shi ne zai kawo shaida amma ba za a ce lallai shi zai bi duk hanyar da zai kuɓutar da kansa ba. 

3) Ana yin hukunci ne da zahiri ba da zato ba. 

4) Haramun ne a hukunta wanda wanda bai yi laifi ba. 

5) Kada alƙali ya ɗauki wani ɓangare ya goya masa baya.

6) Kada a naɗa alƙali ko ma’aikaci a ma’aikatar shari’a sai masani, amintacce mai gaskiya da riƙon amana. 

7) Wanda ake tuhuma a matsayin mara laifi yake har sai an tabbatar da laifin akansa. 

8) Haramun ne a azabtar da wanda ake zargi da aikata laifi ko a tilasa shi ga amsa laifi da ake tuhumarsa akansa ko a wulaƙanta shi ko a ci mutuncinsa. 

9) A lokacin sauraron ƙara wajibi ne alƙali ya daidaita tsakanin mai ƙara da shaidu da lauyoyin kowanne ɓangare a komai har a wurin kallo. 

10) Wani ba ya ɗaukar laifin wani, kada a hukunta ɗa akan laifin ubansa, ko ɗan uwa akan laifin ɗan uwansa da sauransu, wannan babban zalunci ne. 

11) Wajibi ne gwamnati ta yi adalci wajen ayyuka, da samar da damar yin aiki da rabon arziƙin ƙasa da sauran al’amuran gudanar wa na yau da kullum. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

Haƙiƙa da za a bi waɗannan dokoki da ƙa’idoji a ɓangaren gudanar da al’amuran gwamnati da hukomomi da ƙungiyoyi kai har ma da makarantu da gidaje tabbas da an zauna lafiya da arziƙi ya yaɗu a samu nutsuwa da kwanciyar hankali a duniya da lahira. 

SAKAMAKON ZALUNCI 

Shi kuwa zalunci babu abinda yake haifarwa ga azzalumai da ƙasa sai musiba da bala’i a duniya da lahira. Kowane irin zalunci babba da ƙarami gamammen zalunci wato zalunci da shugabanni suke yi wa miliyoyin mabiyansu, da kuma zalunci da ɗaiɗaikun mutane suke yi wa junansu, kamar zalunci tsakanin ma’aurata, da ubangida da yaronsa da maƙoci, da malami da ɗalibansa da sauran rukunonin al’umma, duka irin waɗannan zalunce-zalunce Allah Ta’ala ba ya barinsu su wuce kawai ba tare da wani sakamako ba. 

Sakamakon wani zalunci yakan kasance hallakar da gaba ɗayan al’umma kamar yadda ya faru ga Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu. Wani sakamakon yakan tsaya ne kawai akan wanda ya aikata zalunci shi kaɗai. Amma kuma idan mutanen kirki suka rungume hannu suka zurawa azzalumai ido suna sheƙe ayarsu babu mai kwaɓarsu.

To sakamakon in ya zo yakan shafi kowa har managartan, saboda ƙin ɗaukar matakin hana zalunci sakamakon zalunci yakan kasance ta hanyoyi daban-daban kamar talauci mai naci, taɓarɓarewar tsaro, yunwa, azzaluman shugabanni da koma-baya da rashin ci gaban al’umma. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

Alƙur’ani mai girma da hadisan manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) cike suke da bayanan mummunan sakamakon azzalumai a duniya da lahira. 

A dunƙule ga abinda suke nunawa; 

  1. Allah Ta’ala ba ya ƙaunar zalunci ba ya kuma ƙaunar azzalumai, yana fushi da su yana la’antarsu. 
  2. Zalunci yana janyo musiba a bayan ƙasa kamar girgizar ƙasa, ambaliyar ruwa, tsawa, iska, gobara, yawan mace-mace, annoba, fari da sauransu. 
  3. Zalunci yana jefa mutane cikin ɗimuwa da kiɗima da rashin samun shiriya ta yadda za a fita daga halin da ake ciki, haka kuma yakan ƙeƙasar da zuciya, azzalumai su ƙi tuba har su mutu akan zaluncin su gam da matsananciyar azaba a lahira. Shi ne ma’anar faɗin Allah Maɗaukaki:”Allah ba ya shiriyar da azzalumai. 
  4. Allah Ta’ala ba ya ba da nasara da rinjaye ga azzalumai ko da kuwa an ga sun ci wata nasara to ba mai ɗorewa ba ce, kuma abinda zai biyo baya na musiba da sharri ba ƙarami ba ne. 
  5. A lahira azzalumai ba za su ji da daɗi ba domin akwai azzaluman da za su shiga wuta har abada ba za su fita ba, waɗansu kuma za su daɗe a cikinta gwargwadon irin zaluncin da suka yi. 
  6. Azzalumai ba za su samu rabauta ba a lahira. 
  7. Ba za su samu kariyar Allah ba. 
  8. Ba za su shiga inuwar Allah ba. 
  9. Allah Ta’ala zai haɗa su da waɗanda suka fi ƙarfinsu su gana musu uƙuba. 
  10. Ƙasar da zalunci ya samu wurin zama, sama da ƙasa ba za ta samu bunƙasa ba, ba za a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya ba a cikinta, komai sai ya sukurkuce a yi ta ragabza ba ji ba gani ana ci gaban mai haƙan rijiya.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceHaƙƙoƙin Mabiya Akan Shugabanni
Labarin na GabaNasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma