Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma

0
86

Akwai hanyoyi da yawa da shugabanni da ma’aikata suke bi wajen ɓarnatar da dukiyoyin al’umma kuma sai Allah ya hukunta su a kansu domin nau’i ne na cin amana da rusa tattalin arziƙin ƙasa.

Kaɗan daga cikin waɗannan hanyoyi su ne;

1) Fantamawa da wadaƙar da shugabanni da manyan ma’aikata suke yi; da su da iyalansu da abokansu da surukansu da barorinsu da dukiyar al’umma musamman a lokacin bukukuwansu.

2) Antaya dukiya ga wanda aka ga dama haka kawai; saboda an ga dama ya zama miloniya ya yi nashe-nashe yana muwalat ya zama kamar wani sabon mutum. A can gefe kuma ga talakawa suna ta kuka wasu ma suna mutuwa; an hana su ɗan abinda za su sayi abinci da magani.

3) Tara dukiyar ƙasa da taskance ta da hana talakawa da sauran mabuƙata sai dai a yi ta cewa tattalin arziƙin ƙasa ya haɓaka; asusun gwamnati ya cika maƙil da kuɗi; amma babu wani talaka da zai gani a ƙwaryar tuwonsa sai dai a yi ta surutu maras kan gado. Wanda in ba su masu faɗar ba, babu mai fahimtar abinda suke faɗa.

4) Yin amfani da dukiyar al’umma a kan buƙatun ƙashin kai, kamar motoci, injina; kayan aiki da kuɗin al’umma a gonakinsu, ko ma’aikatunsu ko gidajensu da sauransu.

5) Fifita manya da masu hannu da shuni a kan waɗanda ba su da komai ko ba su san kowa ba; ta hanyar rage, ko yafe musu haraji ko kuɗin fito ko ɗaukar su ko ‘ya’yansu ko matansu aiki; ko ba su bashi don su juya wataƙila ma a ce an yafe musu.

6) Kashewa mawaƙa da makaɗa kuɗaɗe masu yawa don kawai neman suna; alhali ga malaman makaranta da likitoci da sauran talakawa suna fama da ƙarancin albashi wanda ya jawo taɓarɓarewar aikin gwamnati da rashin zaman lafiya a ƙasa, sai ka ga a lokaci guda wani mawaƙi ko ɗan bal ko wata ‘yar fim suna zama miloniyoyi a sama.

7) Kashe kuɗaɗe masu nauyin gaske a kan harkokin zaɓe; waɗanda da za a tsakuro ɗaya bisa ukunsu a sa a ɓangaren ilimi ko noma ko lafiya ko tsaro da an ga canji a rayuwar al’umma.

Amma ina sai a yi watsi-watsi da waɗannan kuɗaɗe masu ciwon gaske a yi abinda aka ga dama; a ce an zaɓe wane ya ci wane ya faɗi.

8) Kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tarbar shugabanni na gida da na wajen domin ƙawata tituna; tara musu talakawa, shirya abinci da sauran abubuwa na ganin ido sai ka ga a yini ɗaya an kashe miliyoyin nairori na fitar hankali; saboda wai shugaba wane zai kawo ziyara ƙasa ko jiha.

9) Warewa harkokin wasannin kuɗaɗe masu ɗimbin yawa fiye da kuɗin da aka warewa ma’aikatar lafiya; tsaro, ilimi da sauransu waɗanda suka fi wasanni muhimmanci; amma dai haka suke rufe idanunsu su toshe kunnuwansu su narka kuɗi a can ba ruwan su.

10) Caɓawa masallatai ado wani lakacin da gwalagwalai amma a yi burus da limamai da ladanai da ma su kansu masallatan masu sallah a wasu masallatan; sai ka ga adon yana shagalar da masu sallah maimakon su tara hankalinsu ga sallarsu; sai su yi ta kallon ƙyale – ƙyalen da aka yi.

A wasu ƙasashen kuma sai a gina masallaci gari guda amma kuma babu masu sallar, sai dai ‘yan yawon buɗe idanu ne za su rinƙa zuwa suna ɗaukar hotuna a cikinsa.
Kamar yadda a waɗansu ƙasashen ake ƙawata ƙaburburan shaihunai a kashe miliyoyin daloli domin kawai a samu goyon bayan mabiyan wannan mamacin (shehin).

11) Rashin kula da aiki ta hanyar zuwa a makare da tashi kafin lokacin ya yi; da ma ƙin yin aikin ai an je wurin aikin sai a ɓuge da hira ko karance-karancen jaridu ko matse-matsen waya da kallon talabijin; ka ga kuɗin da ake kashewa kan waɗannan ayyukan da ma’aikatan kusan duk asarar su ake yi.

12) Kashe dukiyar al’umma kan bukukuwa na ƙasa ko na siyasa ko bukukuwan da ake danganta su ga addini kamar bikin ranar samun ‘yancin kai, Bikin ranar demokuraɗiyya; bukukuwan mauludin Annabi da na shaihunai, sai ka ga an fitar da miliyoyin kuɗi an yi watandar su, alhali ga lalurorin rayuwa babu cikakkiyar kulawa.

13) Biyawa ‘yan siyasa da ‘yan jagaliya aikin hajji ba don komai ba sai don kawai sun yi wa shugaba yaƙin neman zaɓe sai ya saka musu da kujerun hajji, waɗansu ma in sun je hajijiya kawai za su yi su dawo. Amma malamai masu koyar da alhazai aikin hajji da likitoci da sauran maa’aikatan da za su taimakawa alhazai su yi ibada cikin nutsuwa da inganci waɗannan babu wani laifi don gwamnati ta biya musu aikin hajji amma a ji tsoron Allah a yi gaskiya da adalci a dubi cancanta wajen zaɓar waɗanda za a biyawa.

14) Ha’inci wajen ba da kwangila ta hanyar kashe-mu-raba tsakanin ‘yan kwangila da jami’an gwamnati; sai a zaftare kuɗin ko dai a ƙi yin aikin sam ko kuma a yi shi mara inganci ta yadda da an kwana biyu zai tashi daga aiki, in titi ne sai ya ɓaɓɓagure in gini ne ya rushe in wasu injina ne su lalace. Subhanallah.

15) Wawashe kuɗaɗen al’umma a je a damfare su a bankunan ƙasashen turai, su yi ta gina kansu da su; ‘yan ƙasa kuma suna ta mutuwa. Waɗansu ma sai su je can su kafa masana’antu alhali ga miliyoyin ‘yan ƙasa ba su da aikin yi.

16) Tarukan siyasa musamman na neman zaɓe da karɓar waɗanda suka baro jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar gwamnati; in ka ji yawan kuɗin da ake kashewa a irin wannan harkar abin akwai matuƙar takaici da ɗaure kai.

17) Ware kuɗi mai yawan gaske da sunan wai za a yi addu’ar neman zaman lafiya ga ƙasa; ko kuma samun nasara a zaɓe. Sai dai abin takaicin shi ne mafi yawancin wannan kuɗi masu addu’ar ta gaske; saboda Allah ko labarinsu ba su ji ballantana su gan su. Sai a a yi dumbuza ana bai wa bokaye da miyagun malamai da matsafa da waɗanda ma ba musulmi ba. In ya zama dole sai an fitar da wannan kuɗi kamata ya yi a bi talakawa da gajiyayyu da malaman zaure da na tsangayu da ɗalibansu a ba su abinda zai faranta musu rayuka su ma su sami sa’ida da walwala to ko ba su yi addu’a ba; Allah zai biya buƙata sakamakon faranta musu da aka yi.

A gaskiya hanyoyi da waɗansu shuwagabanni suke bai wajen tarwatsa da ɓarna da dukiyar al’umma suna da yawan gaske, abin fa ya zama sai dai a ce innalillahi wa inna ilaihirraji’un.
Ya Allah ka ba mu ikon gyaran halayen mu, ka yi mana a fuwa da gafara ka a zurtamu da shugabanni managarta masu ƙarfi da amana amin.

Domin karanta cikakken bayani akan Hidisai Goma Kan Hatsarin Shugabanci danna nan

Domin karanta cikakken bayani akan Haramcin Zalunci, Tasirin Addu’ar Wanda Aka Zalunta Da Wajabcin Sa danna nan.

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceƊagowa Daga Ruku’u
Labarin na GabaYadda Sakamakon Zalunci Yake