Hadisai Na Ƙarya Da Raunana A Kan Ashura

0
42

Ƙirƙirar hadisai da yaɗa su yana ɗaya daga cikin manyan  hanyoyi da ‘yan bidi’a suke bi domin yaɗa bidi’o’insu, musamnan hadisai na falalar mutane lokuta da wurare.

Ranar ashura da azuminta da yin kuka a ranar da shafa kan maraya da cika-ciki da sauransu, sun samu rabo mai tsoka a cikin hadisan ƙarya da raunana.

Shaihin malami Abul Faraj Abdurrahman Ibnul Jauzi Rahimahullahi (A.H.S. 510 Y.M.S 597) yace: Waɗansu jahilai masu da’awar su ahlussunna ne, sun ƙirƙiro hadisai kan falalar ashura wai don su muzgunawa ‘yan shi’a, duka su biyun ba ruwan mu da su.

Duk da cewa hadisin ya inganta cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi umarni da yin azumin ashura yace yana kankare zunubin shekara, amma ba su gamsu da wannan ba sai da suka ƙirƙiri hadisai masu ɗimbin yawa akan hakan.

Ga wasu daga cikin waɗannan hadisan ƙarya:

1-An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu); yace Haƙiƙa Allah ta’ala Ya wajabtawa banu Isra’ila azumin ranar ashura; shi ne ranar 10 ga watan Muharram, kuma wanda ya yi azumin wannan yini a cikin sa Allah zai yalwata masa wannan shekarar. Ku yi azumi a wannan ranar saboda a ranar Allah Ya karɓi tuban Annabi Adam (Alaihis Salam).

A ranar Allah Ya ɗaukaka Annabi Idris (Alaihis Salam), a ranar; Allah ya kuɓutar da Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) daga wuta; a ranar Annabi Nuhu (Alaihis Salam) ya fito daga jirgin ruwa; a ranar aka saukar da Attaura ga Annabi Musa (Alaihis Salam); a ranar aka fanshi Annabi Isma’il (Alaihis Salam) daga yanka.

A ranar Allah Ya fitar da Annabi Yusuf (Alaihis Salam) daga kurkuku; a ranar Allah Ya dawowa da Annabi Yaaƙub (Alaihis Salam) ganinsa, a ranar Allah Ya yaye wa Annabi Ayuba (Alaihis Salam) bala’in da ya same shi. A ranar Allah Ya fitar da Annabi Yunusa (Alaihis Salam) daga cikin kifi; ita ce ranar da ruwa ya yi hanya a bani Isra’ila.

A ranar Allah Ya gafartawa Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) zunubansa waɗanda suka gabata da waɗanda suka jinkirta. A ranar Annabi Musa (Alaihis Salam) ya ƙetare ruwa, a ranar Allah ya karɓi tuban mutanen Annabi Yunusa wanda ya yi azumi a wannan rana, za a kankare masa zunuban shekara arba ‘in.

Ranar farko da Allah Ya halitta ita ce ashura ranar ashura aka fara yin ruwan sama. Rahamar da taf ara sauka a duniya ranar ashura ta sauka. Wanda ya yi azumi a wannan rana, kamar wanda ya yi azumin gaba ɗayan zamani ne. Shi ne azumin annabawa.

Wanda ya raya daren ashura za a ba shi ladan ibadun halittun sammai bakwai. Wanda ya yi salla raka’a huɗu ya karanta Fatiha da ƙulhuwa ƙafa hamsin, Allah zai gafarta masa zunuban shekaru hamsin da suka wuce, da shekaru hamsin masu zuwa, za a gina masa minbari dubu na haske a cikin mala’iku.

Wanda ya shayar da wani kurɓi ɗaya na ruwa, zai kasance kamar wanda bai taɓa yin saɓo ba. Wanda ya ciyar da miskinai a ranar har suka ƙoshi, zai ƙetare siraɗi kamar walƙiya. Wanda ya yi sadaka ranar ashura zai kasance kamar wanda bai taɓa hana mai bara ba.

Wanda ya yi wanka ranar ashura ba zai ƙara yin rashin lafiya ha sai dai cutar ajali. Wanda ya sa kwalli ranar ashura, ba zai yi ciwon ido ba a wannan shekarar. Wanda ya shafa kan maraya a ranar ashura, za a ba shi ladan wanda ya kyautatawa gaba ɗayan marayun duniya. Wanda ya yi azumin ashura za a ba shi ladan mala’iku dubu goma, wanda ya yi azumi ranar ashura za a ba shi ladan aikin hajji da umra dubu. Wanda ya yi azumin ashura za a ba shi Ladan shahidai dubu. Wanda ya yi azumin ranar ashura za a rubuta masa ladan sammai bakwai.

A ranar aka halicci sammai da ƙassai da duwatsu da koguna, da al’arshi; da alƙalami da lauhul Mahfuz da mala’ika Jibrilu. A ranar ashura aka ɗaga Annabi Isa (Alaihis Salam) zuwa sama, a ranar aka ba wa Annabi Sulaimam (Alaihis Salam) mulki.

A ranar ashura za a yi tashin alƙiyama. Wanda ya gaishe da mara lafiya ranar ashura za a ba shi ladan wanda ya gaishe da marasa lafiyar duniya.

Shaihin malami Ibnul Jauzi ya ce: “babu wani mai hankali da zai yi kokwanto kan cewa wannan hadisi ƙarya ne. Kuma wanda ya ƙirƙiro shi ya tonawa kansa asiri inda ya ce; ranar ashura ita ce ranar farko da Allah ya halitta, alhali kwanaki tara ne suke gabatar ranar ashura, to su kuma yaushe aka halicce su? Kuma wai a ranar aka halicci sama da ƙasa da duwatsu ranar Juma’a Alhali wannan ya saɓawa sahihin hadisi.

Sannan ga lada mai yawa wanda ya saɓawa ƙa’i’dojin shari’a, ya ya za a yi daga azumin rana ɗaya kawai a ba wa mutum ladan hajji da umra da shahidai dubu.

2- A wani hadisin na ƙarya an ce wai a ranar ashura aka halicci Annabi Adam (Alaihis Salam); aka haifi Annabi lbrahim (Alaihis Salam); aka haifi Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wa Sallam)! Kuma wai a ranar Allah Ya dai-daita a bisa al-arshi; kuma wai wanda ya bai wa mai azumin ashura abin buɗa baki; za a ba shi ladan wanda ya ciyar da gaba ɗayan al’ummar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceNasiha A Kan Mata
Labarin na GabaWasu Daga Malaman Alƙur’ani A Jihar Zamfara