Su kuwa mabiya suna da waɗannan haƙƙoƙi akan Shugabanninsu:
- Tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da mutuncin mabiyansa. Wajibi ne ya kula da tsaron kan iyakoki, ya yi maganin ‘yan fashi da ɓarayi da ‘yan ta’adda. Ya kula sosai da jin daɗin jami’an tsaro da iyalansu ta yadda za su samu ƙarfin gwaiwa da kishin kare ƙasa.
- Kulawa da addini da bunƙasa shi ta hanyar jan managartan malamai a jiki da neman shawarwarinsu da fatawoyinsu da sauraron karatuttukansu da wa’azin su.
Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa danna nan
Kada ya bar kafirci ko bidi’a ko lalata da masu yinsu su samu sakewa har su kafu a inda yake da iko. Ya ƙarfafa koyar da ingantacce sahihin addini bisa koyarwar ƙur’ani da sunna da fahimtar magabata na ƙwarai.
- Wajibi ne shugaba ya kula da al’amarin musulunci, kada ya yi sakaci da salloli biyar a cikin jama’a ya ringa halartar sallolin juma’a da na idi, ya kula da yadda limamai suke gabatar da huɗubobi, da karatuttukansu, ya kula da ladanai da kiran salla daidai.
- Ya nada alƙalai masana masu adalci da tsoron Allah da kamewa, ya sanya idanu sosai a kansu, saboda sai an tuhume shi kan duk shari’un da suka yi, zai kuma samu lada kan adalci da taimako da suke yi wa mutane.
- Wajibine akan shugaba musulmi ya ringa fita jihadi da kansa, sannan kuma ya tura mujahidai suna yi a ƙalla sau ɗaya duk shekara. Gwargwadon ikonsa. Kada kuma ya yi sakaci da sauran nau’o’in jihadin.
- Aiwatar da Shari’ar Allah da hukunta masu laifi ba sani ba sabo kamar yadda Allah ya shari’anta da manzonsa, kada ya kuskura ya yi wani hukunci da ya saɓawa shari’ar Allah Ta’ala.
- Ya kula da tattalin arziƙin mabiyansa da jin daɗinsu da walwalarsu. Ya tabbatar yana bin hanyoyin da shari’a ta yarda da su domin samun kuɗin shiga kamar zakka, ganima da jizya, ya kuma sarrafa su ta hanyoyin da shari’a ta yi izini a sarrafa su.
- Kafa hukumar kula da waƙafi da tsara al’amarinsa ta yadda kowa zai amfana da shi, mutane kuma su samu ƙarfin gwuiwar bayar da kafa waƙafin.
- Yin adalci wajen rabon arziƙin ƙasa da gudanar ayyukan ci gaban al’umma.
- Wajibi ne shugaba ya kasance mai gaskiya da riƙon amana ya guji zalunci da nuna son kai da bambanci tsakanin mabiyansa.
Domin karanta Haƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu Danna nan
Shahararren malamin nan masanin siyasar musulunci Abul Hassan Almawardi Rahimahullahu ya faɗa a cikin sanannen littafinsa ‘Al-Ahkamus sultaniyya cewa akwai haƙƙoƙi goma akan shugabanni.
Ataƙaice su ne;
- Kiyaye addini daga gurɓata.
- Tabbatar da doka da oda da baiwa kowa haƙƙinsa.
- Tabbatar da tsaro a birane da ƙauyuka.
- Tabbatar da hukuncin Allah ba sani ba sabo.
- Tabbatar da tsaron kan iyakoki.
- Yin jihadi domin ɗaukaka addinin Allah Ta’ala.
- Tattara kuɗin shiga da sarrafa su ta hanyar da shari’a ta yarda da su. 8. Rabon arziƙin ƙasa da biyan ma’aikata albashinsu.
- Naɗa amintattu mutanen kirki masu gaskiya akan muƙamai.
10. Sanya idanu akan dukkanin al’amuran mabiyansa da wanda ya naɗa su kula da ɓangarorin gudanarwa kada ya bari kowa yake cin karensa ba babbaka.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan