Babban nauyi a wajen tarbiyya yana kan uba, kuma duk kulawar uwa in uba bai yi nasa aikin ba, to sai an samu matsala a tarbiyyar ‘ya’ya.
A dunƙule ga wasu daga cikin nauye-nauyen da suke kan uba,
1. Zaɓen mace managarciya mai addini.
2. Kaucewa saɓon Allah a lokacin neman auren,
3. Kaucewa saɓon Allah a lokacin biki.
4. Kula da haƙƙoƙin da matarsa take da su a kansa.
5. Kula da ladaban ma’amalar aure a ranar farko,
6. Cikakkiyar kulawa da matar a lokacin da take da ciki. kula da lafiyarta da tausaya mata da taimaka mata da kwantar mata da hankali. Haka a lokacin da take naƙuda, da lokacin da ta haihu.
7. Nuna farin ciki da godiya ga Allah kan duk abin da ta haifa, mace ko namiji
8. Cikakkiyar kulawa da lafiyarta da faranta mata da taimakon ta, da ciyar da ita a lokacin da take shayarwa.
9. Yin hidimomin jariri waɗanda suka haɗa da sa masa suna mai kyau. yi masa aski, yi masa kaciya(shayi), yanka masa ragon suna, da al’adu masu kyau na nuna farin ciki waɗanda ba su ci karo da shari’a ba.
10. Daga nan kuma sai a duƙufa wajen tarbiyyar jiki. hankali da tunani da ilmi, zamantakewa, ƙwaƙwalwa, siyasa da sauransu tun daga wannan lokaci har zuwa balagar ɗa namiji da aurar da ‘ya mace kamar yadda Za a yi bayani a nan gaba da kuma sauran maƙaloli da za su zo in sha Allahu.
Domin karanta cikakken bayani a kan Aikin Uwa danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar ( Shehu Mansur Dala ) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.