Haƙƙoƙin Da Ma’aurata Suke Tarayya A Kansu

0
1011

A Musulunce ma’aurata na yin tarayya a kan haƙƙoƙi masu zuwa kamar haka:

1. Taimaka wa junansu a kan bin Allah (S.W.T).
2. Kyautata zamantakewa.
3. Haƙuri da juna.
4. Biya wa junansu buƙatar sha’awa.
5. Rufa wa junansu asiri.
6. Kishin junansu.
7. Kula da tsafta da kwalliya.
8. Mutunta dangin kowannensu.
9. Kyautata tarbiyyar ‘ya’yansu.

Ga bayanin waɗannan haƙƙoƙi nan tafe ɗaya bayan ɗaya a fayyace:
1. Taimaka wa junansu a kan bin Allah:

An karɓo hadisi daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Allah ya jiƙan mutumin da zai tashi cikin dare sai ya yi salla, kuma ya tashi matarsa domin ta yi sallah, in ta ƙi tashi ya yayyafa mata ruwa a fuskarta, kuma Allah ya jiƙan matar da za ta tashi cikin dare sai ta yi salla, kuma ta tashi mijinta domin ya yi salla, in ya ƙi tashi ta yayyafa masa ruwa a fuskarsa”. Abu Dawud, Nasa’I, Ibn Majah da wasunsu ne suka rawaito shi.
Kuma an karɓo daga Abu Sa’id (R.A) ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan mutum ya tashi iyalansa cikin dare, suka yi salla za a rubuta su cikin maza da mata, masu ambaton Allah da yawa”. Ibn Majah ya rawaito shi.
Sannan kuma an karɓo daga A’isha (R.A) ta ce: “Mun kasance muna tanada wa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) aswaki da ruwan alwalarsa, sai Allah ya tashe shi a sanda ya so, tashinsa cikin dare, sai ya goge bakinsa kuma ya yi alwala, sannan ya yi salla”. Ibn Hibban ya rawaito.

2. Kyautata Zamantakewa:

Wannan haƙƙi na kyautata zamantakewar ma’aurata ya ƙunshi abubuwa da dama da suka haɗar da:
(a) Cin abinci tare.
(b) Zantawa da juna.
(c) Yin wanka tare.
(d) Wasa da dariya.
(e) Gudanar kyauta a tsakaninsu.
Da dai sauran abubuwan da suke kyautata zaman tare.

(a) Cin Abinci Tare:

An karbo daga A’isha (R.A) ta ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana zuwa da abin sha, sai in sha daga mazubin abin shan, alhali ina yin haila, sannan sai manzon ya karɓa ya sanya bakinsa a gurin da na sa bakina ya sha, kuma na kasance ina ɗaukar ƙashi mai nama in gwagwiyi, sannan ya karɓa, sai ya sanya bakinsa a inda na sa bakina, shi ma ya gwaigwaya”.
Sannan Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Sa’ad ɗan Abi Waƙƙas (R.A) daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da shi: “Haƙiƙa babu wata ciyarwa da za ka nufi Allah da ita, face sai an ba ka lada a kanta, har lomar da kake sanyawa a cikin bakin matarka”.

Ina angwaye da tsofaffin hannu a harkar aure? Cikinku wane ne yake ba wa matarsa abinci a baki? Kuma wane ne yake sanya bakinsa a inda matarsa ta sa nata bakin; ya ci abin da ta ci ko kuma ya sha abin da ta sha? Tare da cewa yin hakan shi ne koyarwa da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi mana.
Ina mazan da idan matansu suna haila ko kuma jinin biki ba sa iya zama a kusa da su; ballantana su ci wani abu tare da su, shin su irin waɗannan mazan da wane suke yin koyi ne? Manzonmu dai bai yi haka ba, kuma mu al’ummarsa bai umarce mu da yin haka.

(b) Zantawa da juna:

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Daddaɗar kalma sadaka ce”. Bukari da Muslim ne suka rawaito a hadisin da aka karɓo daga Abu Huraira (R.A).

Don haka zantawar ma’aurata da kalmomin da za su faranta wa junansu rai da su, yana daga cikin ƙofofin alherin duniya da lahira da rayuwar aure ta ƙunsa.
A duniyance, yin hakan zai ƙara wa ma’aurata nishaɗi da ƙaunar juna, a lahirance kuma zai tara musu ladan sadaka da za su girba.
Wani abin ban sha’awa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ko wajen faɗar sunan matarsa sai ya yi salon da zai faranta mata rai, kamar yadda aka karɓo hadisi daga Abu Salama ɗan Abdurrahman ya ce: “Haƙiƙa A’isha matar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ta ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da ita “Ke A’ish jibril yana yi miki sallama”. Bukhari ne ya rawaito (hadisi mai lamba (6201) da mai lamba (827) cikin littafinsa Al’adabul Mufrad.

(c) Yin wanka Tare:

Daga A’isha (R.A) ta ce: “Na kasance ina yin wankan janaba ni da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) daga mazubi guda dake Tsakanina da shi, hannayenmu na sassaɓawa a cikin mazubin, sai ya riga ni, har sai na ce da shi bar min saura, bar min sauran”. Bukhari da Muslim da Abu Awana ne suka rawaito shi.

Tambaya: wai kuwa tun da kuka yi aure, kun taɓa yin wanka tare? In kai ne ba ka ba ta ƙofar yin haka ba; to ka gyara, idan kuma ke ce ba ki waye da ana yin haka ba, to ki yi ƙoƙari ki waye da yin aiki da wannan sunna don kyautata auratayyarku.

(d) Wasa da Dariya:

Wata rana Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tambayi sahabinsa Jabir ɗan Abdullah ya ce da shi: “Jabir ka yi aure? Ya ce: “I”. (na yi aure). Sai ya ce: “Budurwa ko bazawara?” na ce: “A’a, bazawara ce”. Ya ce: “Ina ma budurwa ce, ka rinƙa wasa da ita, ita ma ta rinƙa wasa da kai, ka rinƙa sa ta dariya, ita ma ta rinƙa sa ka dariya…”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
An karɓo daga A’isha (R.A) ta ce: Ta kasance tare da Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a wata tafiya a lokacin ina amarya, ban yi jiki ba, sai ya ce da sahabbansa su yi gaba; sai suka yi gaba, sannan sai ya ce da ni: “Zo mu yi tsere”. Sai muka yi tsere na wuce shi, bayan haka sai na kuma fita wata tafiya tare da shi, sai ya ce da sahabbansa su yi gaba, sannan ya ce da ni: “Zo mu yi tsere”. Na manta da mun yi tsere na wuce shi, kuma yanzu na yi jiki, sai na ce ta yaya zan yi tsere da kai a wannan yanayin da nake ciki? Sai ya ce ai kuwa sai kin yi. Sai muka yi ya wuce ni, kuma ya rinƙa dariya, sannan sai ya ce: “Ɗaya da ɗaya kenan”. Humaidi da Abu Dawud da Nasa’I da wasunsu ne suka rawaito shi.

‘yan uwa ma’aurata ba fa sai lallai wasan tsere ba, akwai wassanni salo-salo iri daban daban da za ku iya yi don nishaɗantarwa da kyautata zamantakewar juna.

(e) Gudanar Kyauta Tsakanin Ma’aurata

Imamul Bukhari ya rawaici hadisi a cikin littafinsa- Al’adabul Mufrad, wanda aka karɓo daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ku rinƙa yin kyauta, sai ku rinƙa son junanku”.Wannan hadisi na koyar da mu ribatar halayyar kyauta, don ƙarfafa soyayyarsu da ƙara ƙaunar junanmu, kenan idan ma’aurata suka ɗabi’antu da halayyar yi wa junansu kyauta; to ƙauna da soyayyarsu za su ƙarfafa kamar yadda zamantakewarsu zacta ƙara kyautata.

Amma fa kada hakan ya sa ma’aurata su manta da cewa tushen soyayyarsu fa neman yardar Allah ne da raya sunnar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ba a abin da ɗayansu zai ba wa ɗayan ba. ‘Yan uwa muddin muka tsayu a kan haka tsaikon samun abin hannun ɗayanmu ba zai gurɓata zamantakewar aurenmu ba. Wannan kenan.

3. Haƙuri da Juna:

Allah (S.W.T) ya ce: “Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya, ku nemi taimako da haƙuri da salla (cikin al’amuranku), hakika Allah na tare da masu haƙuri”.
Kuma dai Allah (S.W.T) ya ce: “Ka yi haƙuri a kan duk abin da ya same ka, haƙiƙa hakan na daga cikin muhimman al’amura”.
Sannan kuma an karbo hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya yarda da su, ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Muminin da yake cuɗanya da mutane kuma yake haƙuri da cutarsu, shi ne yafi alheri a kan muminin da ba ya cuɗanya da mutane, kuma ba ya haƙuri da cutarwarsu”. Ibn Majah ne ya rawaito shi.

Duba da waɗannan dalilai, haƙuri ya zamar mana dole matuƙar dai muna son samun taimakon Allah da zamantowarmu mafiya alherin bayi.
Don haka mita da fushi da raki duk ba za su maganta mana ɓacin ran da abokin zama ya sabbaba mana ba. Mafita kawai shi ne haƙuri da bin al’amura sannu a hankali. “Haƙuri maganin zaman duniya”. “Mahaƙurci Mawadaci”.

4. Biyawa Junansu Buƙatar Sha’awa:

Abu ne sananne ga kowa cewa, Allah (S.W.T) ya halicci jinsin maza da ɗabi’ar sha’awar jinsin mata, kamar yadda ya halicci mata da sha’awar jinsin maza. Sannan da yake Allah Gwani ne mai hikima cikin al’amuransa, sai ya shar’anta wa bayinsa aure domin ya zama halattacciyar hanyar da ya yarje musu bin ta don cimma biyan buƙatarsu ta sha’awa. Wanda a sakamakon haka maza suka zama kariya da sutura ga mata kamar yadda su ma matan suka zamar wa maza kariya da sutura. Allah (S.W.T) ya ce: “… su mata sutura ce gare ku, haka kuma maza sutura ce a gare su…”.
Kuma an karɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Mas’ud, Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Haƙiƙa aure ya fi sa rintse ido (daga kallon haram), kuma ya fi zama kariya ga tsiraici (daga afkawa haram) wato zina”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Saboda haka sai kowane ɗaya daga cikin ma’aurata ya tsayu da gaske wajen sauke wannan haƙƙi na biyan buƙatar sha’awa zai ams a sifarsa ta zamowa abokin zamansa kariya da sutura. Ga mai son ya bayar da wannan haƙƙi kuwa daidai da yadda Musulunci ya tsara, to ga abin daya kamata ya yi kamar haka:
1. Tsaftace baki kafin kusantar abokin biyan buƙatar sha’awa.
2. Gabatar da wasa da taɓa gurare dake motsa sha’awa, kamar sumba, runguma, da sauransu.
3. Yin addu’a da ambaton Allah kafin fara biyan buƙatar sha’awa.
4. Wadatuwa da kafar da Allah ya amince a sadu da ita.
5. Nisantar saduwa a lokacin zubar jinin al’ada, da na haihuwa.
6. Nisantar saduwa ta dubura.

Wanda ya kiyaye waɗannan dokoki da tsare-tsare ya halatta ya zaɓi salon da ya so, don aiwatar da biyan buƙatar sha’awarsa a tsaye ne ko a tsugune ko kuwa a kwance.
Don ƙara samun nutsuwa game da dalilin waɗannan dokoki kuwa ga bayanansu kamar haka:

An karɓo daga Shuraih ɗan Hani’I ya ce, na ce da A’isha: Wane abu Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yake fara yi idan ya shigo gidansa? Sai ta ce: “Aswaki yake fara yi”. Muslim ne ya rawaito shi.

Bayan haka a bayanan da suka gabata, munji cewa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da sahabinsa Jabir a lokacin da ya auri bazawara. “ina ma budurwa ka aura wacce za ka ringa wasa da ita, ita ma tana wasa da kai, kuma kana sa ta dariya ita ma tana sa ka dariya”.
Kuma an karbo daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Da ɗayanku lokacin da zai sadu da iyalinsa zai ce: “Ya Allah ka nesanta ni daga shaiɗan, ka kuma nesanta shaiɗan daga abin da ka azurta ni da shi”. To da idan aka azurta su da samun ɗa ta dalilin wannan saduwa, shaiɗan ba zai cutar da shi ba har abada”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Allah ba ya duban rahama ga mutumin da ya sadu da wani namiji ko mace ta dubura”. Tirmizi ne ya rawaito shi.
Sannan Allah (S.W.T) ya ce:
kuma suna tambayar ka game da jinin haila, ka ce (da su) shi ƙazanta ne (don haka) ku nisanci saduwa da mata a lokacin haila ka da ku kusance su, har sai sun yi tsarki…”. Baƙara, aya ta 222.
Kuma dai Allah (S.W.T) ya ce: “Matanku mashukar(gona) ‘ya’yanku ne, to ku zo wa mashukarku ta yadda kuka so”. (wato matuƙar dai ta kafar da aka halarta muku saduwa da su ne”.

Haɗarin Ƙin Saurarar Miji In Ya So
Biyan Bukatar Sha’awa

An karɓo daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan mace ta kwana tana mai ƙauracewa shimfiɗar mijinta, Mala’iku za su yi ta tsine mata har ta wayi gari”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Rufawa Junansu Asiri:

Sirri shi ne ɓoye abin da babu wata masalaha ko amfani cikin bayyanar da shi, kuma ɗabi’antuwar ma’aurata da ita wannan kyakkyawar halayya ta rufin asiri wani babban jigo ne game da tabbatuwar inganci da karantar matsaloli tattare da rayuwarsu ta aure dama watarta.
Don haka lallai ne ma’aurata su sani ba duk abin daya shafi rayuwar aurensu ya halatta su bayyana ga waninsu ba, abin ya shafi maganganunsu ne ko kuwa ya shafi ayyukan da suka gudanar ne.
Bisa ga misali, an karɓo daga Asma’u ‘yar Yazid Allah ya yarda da ita tace: Na kasance a wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) a lokacin maza da mata na zaune a wajensa sai ya ce: “Mai yiwuwa wani na faɗar abin da yake aikatawa da iyalinsa kuma mai yiwuwa wata na bada labarin abin da take aikatawa tare da mijinta sai kowa yayi shiru, sai ni kuwa nace: “I wallahi ya manzon Allah matan na faɗa, kuma mazan ma suna faɗa. Sai yace: to kada ku ƙara faɗa, haƙiƙa fa hakan kamar wani watsattse ne ya haɗu da wata watsattsiya a tsakiyar hanya ya afka mata mutane na kallon su”. Imam Ahmad ne ya rawaito shi.
Kuma an karɓo daga Abi Sa’idil khudri Allah ya yarda da shi yace, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Daga cikin mafiya sharrin matsayi a Wajen Allah ranar Alkiyama akwai mutumin da zai keɓe ya kaɗaita da matarsa ita ma ta kaɗaice da shi, sannan yaje ya yaɗa sirrinta”. Muslim da Ahmad ne suka rawaito shi.

Saboda haka, rashin kulawa da wannan haƙƙi zubar da mutunci ne a duniyance, kuma jefa kai ne cikin mummunar rayuwa a lahira, Allah ka tsare mu. Amin

Kishin Junansu:
Kishi wata kyakkyawar sifa ce daga cikin kyawawan siffofin bayin Allah na ƙwarai.
Kishin ma’aurata kuwa a junansu shi ne: bayyanar da damuwar ɗayansu da ɓacin ransu akan ɗaya a duk lokacin daya durfafi abin da zai gurɓata musu addini ko zai zubar musu da mutunci.
Don haka ba daidai bane miji ya zurawa matarsa ido ya barta tana wasa da addini, ko aikata sakarci da shirme. Haka kuma bai dace ba mace tayi biris ta kauda kai daga ayyukan assha da mijinta yake aikatawa ba.
Idan kuwa ma’aurata sukayi sakacin kula da wannan haƙƙi, to sun tabbata marasa kishin junansu, wanda a ƙarshe hakan na iya kai su gayin rayuwa irin ta dabbobi inda zaka ga mace na sanya gabanta inda take so, shima kuma mijin na yin duk abinda yaga dama. Wannan Kenan.
Sannan kuma zaman ma’aurata cikin zargin junansu da tare dafaruwar wani ƙwaƙƙwaran abin zargi ba, ya saɓa da koyarwar addininmu na musulunci da tsarin zamantakewa. Saboda haka bai halatta a rinƙa samun haka a tsakaninmu ba.
An karɓo hadisi daga Jabir ɗan Atik Allah ya yarda da shi yace: “Haƙiƙa Annabi (tsira da amicin Allah su tabbata agare shi) yace: “…kishin da Allah baya so shi ne kishi ba tare da wani abin zargi ba”. Abu Dawud ne ya rawaito shi.
Kula Da Tsafta Da Kwalliya

Babban abin birgewa game da wannan haƙƙi datar da wanda ya tsayu akan tabbatuwarsa da damun ƙaunar Allah (S.W.T).
Wani ƙarin abin ban sha’awa kuma Allah ya halicci bayinsa da ɗabi’ar son abu mai kyau da tsafta, ke nan bayan ƙaunar Allah da mai tsafta yake samu, zai rabauta kuma da samun dandazon masoya daga cikin bayin Allah.
Allah (S.W.T) yace: “…haƙiƙa Allah yana son (bayinsa) masu yawan tuba, kuma yana son (bayinsa) masu tsarki”.
Kuma an karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “…haƙiƙa Allah kyakkyawa ne, kuma yana son kyu…”. Muslim ya rawaito shi.

Don haka wayayyun ma’aurata basa wasa da wannan haƙƙi na tsafta da kwalliya.
Batun abubuwan mallaka.
Tsaftar Jiki Da Kwalliyarsa:
Tsaftar jiki ta ƙunshi yin wanka a kai a kai, goge baki, aske gashin hammata dana mara, yanke farata, da rage gashin baki ga namiji.
Kwalliyar jiki kuwa kamar sa kwalli, dasa zobe, shafa mai, taje kai ko kitse shi ga mace, da yin ƙunshi, sanya sarƙa, ko ɗan kunne ko kuma awarwaro, da sauran abubuwan da ba suci karo da ƙa’idojin addininmu ba.
Bai halatta Musulmi ya canja halittar da Allah yayi masa ba da sunan kwalliya, kamar yin tsage (shasshawa, da fashin goshi, da bille, da makamantansu), ƙona gashi da ƙara shi, da fiƙe haƙori da yin bilicin da cisge furfura ko rina ta ta koma baƙa, duk waɗannan yin su haramun ne ga musulmi.
Tsaftar Sutura Da Kwalliyarta

Tsaftar sutura shi ne wanke ta, kwalliyarta kuma ya ƙunshi yi mata ado, da goge ta, da sanya turare, da karya hula. Da dai makamantansu, matuƙar dai basu saɓa ƙa’idojin addininmu ba.

Tsaftar Gida Da Abubuwan Mallaka

Tsaftar gida da abubuwan mallaka kuwa su ne wanke abin wankewa, da share na sharewa da goge na gogewa da tsara na tsarawa. Mai gida ya yi nasa, (kamar yashe kwata), uwar gida da amarya masu yi nasu. Wannan ke nan.Mutunta Dangin Juna
Kyautata hulɗar miji da dangin matarsa (wato surukansa); da kuma kyautata huldar mace da dangin mijinta, abu ne mai tushe da asali a Musulunci.

An karɓo daga Aliyu ɗan Abu Ɗalib Allah ya yarda da shi yace: “Na kasance mutum mai yawan fitar da maziyyi, sai na ji kunyar tambayar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) (hukuncinsa), saboda matsayin ‘yarsa (na kasancewar ta mata) a gare ni, sai na umarci Miƙdad ɗan Aswad ya tambayar mini shi, sai ya tambaye shi, sai Manzo yace: “Zai wanke tsiraicinsa ne kuma ya yi alwala”. Bukhari da muslim ne suka rawaito shi.
Wannan ya sa malamai suka ce: Jin kunyar siriki da yi masa ladabi tsare haƙƙi ne daga cikin haƙƙoƙin da Musulunci ya buƙaci a ba wa surukai.
Sannan kuma Imam Muslim ya rawaici hadisi da aka karɓo daga Aisha Allah ya yarda da ita ta ce: Halatu ‘yar Khuwailid ‘yar’ uwar Khadija ta nemi izinin shiga wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) sai ya tuna neman izinin (matarsa) Khadija, sai ransa ya yi fari ya nuna farin cikinsa da zuwan Halatu, sannan yace: “Ya Allah ga Halatu ‘yar Khuwailid ka taimake ta ka zama gatanta…”.

Shi kuma wannan hadisi na sanar da mu cewa ko bayan mutuwa matar da mutum ya aura danginta na da hakkin a ci gaba da mutunta su da darajanta su, to ina ga kuma a ce tana raye kuma ana tare da ita.

Domin karanta cikakken bayani akan Kyautata Tarbiyyar ‘ya’ya danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafi danna nan

labarin da ya wuceJiga-jigan Magunguna
Labarin na GabaAmfanin Ƙaho