Haƙƙin Zaman Gidan Miji

0
1206

Tabbatar mace cikin gidan mijinta, doka ce tabbatacciya daga Allah Maɗaukaki, ga abin da Allah ya ce: “(ku mata) ku tabbata cikin gidajenku, kada ku bayyanar da adonku irin bayyanar da adon maguzancin farko”.

Bisa dogaro da wannan ayar, haramun ne mace ta fita daga gidan mijinta ba tare da izininsa ba, ko da kuwa ta leƙa waje ne.

Wannan ya sa wani ɗan uwa ya gargaɗi mata da cewa:
Sai ta ukunsu gadangama kenan,
Ba ta nufin gyara sai cuta.
Ba ta nufin khairi ga mijinta,
Ba ga kishiyoyi ba ga maƙotaba.
Ba ta nufin gyara sai ɓarna,
Sai duka safe ta cuci mijinta.
Ya tafi ofis ko kuma kanti,
Ba ta ƙara zama ɗakinta.
In mai noma ne ko zage,
Ka tafi gona zaure za ta.
Tana neman ta ga masu wucewa,
Wai ita dai suga kyan fuskarta.
In taga sun ƙi shiga harkarta,
Sai ka ji ta ce za ta maƙobta.

Ayyukan Cikin Gida:

Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah ya yarda da su, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Dukkan ku makiyaya ne, kuma dukkan ku ababan tambaya ne game da abubuwan kiwonku,…. Mace ma makiyayiya ce a kan gidan mijinta da ‘ya’yansa, kuma ita ma abar tambaya ce game da abubuwan kiwonta”.
Sannan an karɓo hadisi daga Asma’u ‘yar Abubakar Siddik, Allah ya yarda da su ta ce: “Na kasance ina yi yiwa zubairu (mijina) hidindimun gida baki ɗaya, kuma ya kasance yana da wani doki da nake wahala da shi, ina yi masa ciyawa kuma ina kula da shi”. Iman Ahmad ne ya rawaito shi.
A wata ruwayar kuma (Asma’u) ta ƙara da cewa, tana ɗinke guga, da kwaɓa gari. Ahmad ne ya rawaito shi.
Sannan kuma dai an karɓo hadisi daga Aliyu, Allah ya yarda da shi, ya ce, haƙiƙa matarsa Faɗima da ta sami labarin an kawo wa Annabi (Tsira da amincin Allah ya su tabbata a gare shi) bayi, sai ta je gida domin ta koka wa Annabi (tsiri da amincin Allah su tabbata a gare shi) game da kantar da hannunnta yake yi a sakamakon amfani da dutsen niƙa (ko ya agaje ta da baiwa), da ba ta sami Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a gida ba, sai ta gaya wa A’isha (R.A), da Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya dawo, sai A’isha ta faɗa masa saƙon Faɗima, sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tafi gidan ‘yarsa Faɗima; ko da ya isa sai ya tarar da ita da mijinta Aliyu (R.A) Sun riga sun kwanta bacci, da suka yunƙura za su ta shi domin taro shi, sai ya ce da su, “Ku yi zamanku a inda kuke’. Sannan sai ya zauna kuma ya ce da su: “Ashe ba na sanar daku abin da ya fi wanda kuka tambaya ba, idan za ku kwanta bacci ku yi tasbihi talatin da uku, hamdala talatin da uku, takbir kuma sau talatin da huɗu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Duba da waɗannan dalilai da wasunsu ne wasu daga cikin malamai suka yanke hukuncin cewa: ɗaukar ɗawainiyar aikace-aikacen da suka shafi cikin gida nauyi ne da ya rataya a wuyan matar aure. Ko da yake ba laifi ba ne a shari’ance ga wanda yake da iko ya samo wa matarsa ‘yar aiki, sai dai fa ba ita ba samun ladan da ake ba wa waɗanda suka tsayu da kansu domin aiwatar da waɗannan ayyuka na cikin gidayaku ‘yan uwa mata!

ku sani fa ba ƙasƙanci ba ne ku tsayu da:

 Ba wa dabbobin miji abinci da kuma share garkensu.
 Wanke banɗaki.
 Sharar tsakar gida.
 Dafa abinci.
 Gyara shimfiɗa.
Da sauran su.
Waɗannan abubuwa dukkan su share fagen shiga Aljanna ne, shi ya sa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabbansa ba su goyi bayan ‘ya’yansu da matansu su yi watsi ko sakaci da su ba. Wannan kenan.

Kula Da Abubuwa Mallakar Miji:

Tabbas ne dukkan wasu abubuwa mallakar miji da suka haɗar da kuɗinsa, abincinsa, kadarorinsa, kayan aiwatar da sana’arsa da dai sauran su; kowanne yana ɗaya daga cikin abubuwan da Allah zai tambayi mace game da su a lahira. Don haka da mai kulawa, da mai banzatarwa, da mai sacewa, duk za su amsa tambayar Allah ba fasawa.

Hana Wanin Miji Shiga Gidan Miji

Ya inganta cikin bayanan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a hajjinsa ta ban-kwana ya ce: “Haƙiƙa maza kuna da haƙƙi a kan mata, na kada su kuskura su yi izinin shiga gidajenku ga wanda ba kwa so ya shigar muku gida, kuma kada su bar wani ya hau muku shimfiɗa alhali ba kwa so”. Muslim ne ya rawaito shi, kuma an karɓo shi ne daga sahabin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) wato Jabir, Allah ya yarda da shi.
Kuma an karɓo daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi ya ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya ce: “Ba ya halatta wata mace ta yi izinin shiga gidan mijinta, sai da izininsa”. Bukhari ne ya rawaito shi.

Neman Izinin Miji Dan Yin Azumin Nafila:

Bukhari,Muslim, Abu Dawud, Nasa’I da wasun su, sun rawaito hadisi da aka karɓo daga Abu Huraira (R.A) Ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Bai halatta ba mace ta yi azumi mijinta na nan a gari in ba Azumin Ramadan ba”.
Sannan kuma ko azumin Ramadan ɗin, in dai na ramuwa ne, bai halatta mace ta yi shi ba har sai ta sanar da mijinta, ta nemi izininsa saboda yalwar kwanakin da take dasu game da ramuwar Azumin da ake bin ta ɗin.

Neman Izinin Miji A Lokacin Buƙatar Fita:

A zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da zazzaɓi ya tsananta ga matarsa A’isha (R.A) a dalilin ƙagen zina da aka yi mata, ta nemi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da ya yi mata izinin tafiya gidansu, domin ta sami tabbacin shin abin da ake faɗa game da ita ya isa kunnen iyayenta kuwa? Don kuma ta dace da samun lallashin mahaifanta da tausayawarsu. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi mata izini ta tafi gida…”. Sahihul Bukhari, hadisi na (4750).

Godiya Da Yaba wa Miji:

Yana daga cikin kyawawan halayen Musulmi ƙwarai ya zama mai yin tukuici da godiya da yabawa kan abin kirkin da aka yi ma.
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda ya yi muku abin kirki, to ku yi masa tukuici, idan ba ku sami abin yi masa tukuici ba, to ku yi masa addu’a, har sai kun ga cewa kun saka masa (wato da yin addu’ar)”.
A wata ruwayar kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa ya yi: “Duk wanda aka yi masa abin kirki, sai ya ce da wanda ya yi masa kirkin, Allah ya saka maka da alheri, to haƙiƙa ya kai matuƙa wajen yabawa”. Tirmizi, Nisa’I da Ɗabarani ne suka rawaito shi.
To ‘yar albarka yi da gaske ki yi aiki da wannan koyarwa ta Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ki yaba wa mijinki game da ɗumbin alherin da yake yi miki, sai ki rabauta da kyakkyawan sakamakon Allah (S.W.T), kuma ki ƙara kima da daraja a wajen mijinki, sannan kuma ki kubuta daga faɗawa cikin jerin mata butulai waɗanda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da ire-iren su Allah baya duban matar da ba ta gode wa mijinta, alhali ba za ta iya wadatuwa daga shi ba”. Nasa’I ne ya rawaito.
Kuma an karɓo shi ne daga Abdullahi ɗan Amr(R.A) wani ƙarin abin ban tsoro ita wannan ta’ada ta butulci ita ce sanadiyyar yawaitar mata a cikin wuta kamar yadda ya tabbata a hadisin da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (R.A), daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Na hangi cikin wuta, ban taɓa ganin abin ban tsoro ba irin na yau, kuma na ga mafi yawaicin ‘yan cikinta mata ne. Sahabbai suka ce: “Me yasa ya Manzon Allah? Ya ce: “Saboda suna butulcewa”. Aka ce Allah suke butulcewa?ya ce: “Miji suke butulcewa, kuma suna da butulcewa kyautatawa, da za ka kyautatawa ɗayarsu tsawon shekara, sannan ta ga wani abin da bai mata daɗi ba daga gare ka, sai ka ji ta ce: “Tun da take ba ka taɓa ganin wani alheri ba daga gare ka ba”. Bukhari ya rawaice shi. Hadisi mai lamba (5197).
To ‘yar uwa ki kiyayi cewa da mijinki me ya taɓa tsinana miki? kin dai ji irin abin da faɗar hakan ke jawowa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye-nauyen Rayuwar aure danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceMene Ne Kishi
Labarin na GabaKishi Iri Nawa ne