Haƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata

0
1017

A Musulunce idan mutuwa ta raba tsakanin ma’aurata, to wanda yake raye cikinsu yana da haƙƙi daga cikin abin da wanda ya mutu ya bari.

Idan mace ce ta mutu, ta bar mijinta, to mijin zai gaji rabin abin da matarsa ta mutu ta bari na abubuwan mallakarta, idan ba ta da ɗa a raye. Idan kuma tana da ɗa a raye, to mijin nata zai gaji ɗaya bisa huɗun abin da ta mutu ta bari ne. Allah (S.W.T) ya ce:
“Kuma kuna da rabin abin matanku suka bari idan ba su da ɗa, amma idan suna da ɗa, to kuna da ɗaya bisa huɗu daga abin da suka bari, bayan (an zartar da) wasiyya da suka yi, ko kuma bashin dake kansu…”.
Idan kuwa miji mutuwa ta ɗauke shi ta bar mata, to ita matar za ta yi wa mijin takaba, sannan kuma za ta gaji ɗaya bisa huɗun abin da ya bari idan ba shi da ɗa a raye, idan kuma yana da ɗa a raye, to za ta gaji ɗaya bisa takwas daga abin da mijinta ya mutu ya bari, wannan shi ne abin da mace ke gada daga miji ko da kuwa su nawa ya mutu ya bari a matsayin matansa.
Allah (S.W.T) ya ce: “…su kuma (matan aure) suna da rabo ɗaya bisa huɗu na abin da kuka bari idan ba su da ɗa. Amma idan kuna da ɗa, to suna da ɗaya bisa takwas daga abin da kuka bari bayan (an zartar da wasiyya da kuka yi, ko wani bashi dake kanku…”.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceAmfanin Ƙaho
Labarin na GabaNauye-nauyen Rayuwar Aure