Gulma (Tsegumi) Don Gurɓata Tsakanin Jama’a

0
895

Gulma dai ita ce faɗar maganar da za ta gurɓata tsakanin mutane, kuma ta haifar musu da rashin jituwa.

Sau tari ‘yan siyasar da muke da su, sun mayar da gulma tsakanin jama’a wata ƙwarewa da gogewa a fagen siyasa musamman gulma ga shugabanni da masu mulki a hannu.

A musulunce, gulma na ɗaya daga cikin manyan laifuka da suke jawo azabar ƙabari. Imamul Bukhari da Muslim sun rawaito hadisi da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah ya yarda da su cewa: haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya wuce wasu ƙaburbura biyu sai ya ce : ” Tabbas ana azabtar da waɗanda suke cikinsu… ɗayansu dai yana yawo da gulma ne, ɗayan kuma ba ya tsarkaka daga fitsari…..”.Sannan kuma an karɓo hadisi daga Huzaifa Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Magulmaci ba zai shiga Aljanna ba.” Bukhari ne ya rawaito shi .

Domin karanta cikakken bayani a kan Munafuntar Jama’a Da Rashin Fayyacacciyar Alƙibla danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasa Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceCin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa.
Labarin na GabaMunafuntar Al’umma Da Rashin Fayyace Alƙibla