Tarbiyyar Addini

0
606

Duk da muhimmancin samun mutum daga iyaye masu addini, wannan ba zai wadatar ga barin yi masa tarbiyya irin ta addini ba. Ita tarbiyya gini ce a kan harsashin da iyaye suka kafa, ta zamowar su masu addini.

Kodayake tarbiyya (idan aka dace) za ta iya gyara mutumin da bai gaji halin addini daga iyayensa ba, amma mafi yawan lokaci, tarbiyya ga wanda ya gaji halin addini ta fi sauƙi da tasiri. Saboda haka wajibi ne ga mai shirin yin aure mace ko namiji ya fi bayar da muhimmanci ga siffar addini a wurin wanda zai aura fiye da kowace irin siffa daban. Sai dai idan halin addini ya haɗu da sauran halaye, ko siffofi, kamar kyawun halitta da dukiya ko dangi da sauran su, to haka ya fi kyau, idan kuma aka sami dukkan siffofi sun haɗu, sai dai babu addini shi kaɗai to abu ya ɓaci, lallai ne a nemi mai addini.
Sannan kuma ita kanta tarbiyyar addini ba za ta yiwu cikin sauƙi ba, idan mahaifa ba masu addini ne ba,  domin su ne masu tarbiyya na farko, yana da kyau mu san cewa ita tarbiyyar addini ana fara yi wa yaro ita tun kafin a haife shi, ta hanyar aiwatar da ladubban da addini ya tanadar wa miji da mata, waɗanda idan suka bi su, babu shakka, albarkar yin haka za ta shafi ɗan da za su haifa. Haka kuma, ba za ta samu ba daga mahaifa bin tsarin rayuwar Yahudu da Nasara, waɗanda ba ruwansu da addini. Misalin Manzo Allah (Sallallahu alaihi wassallam )ya ce: “Idan mutum zai kusanci iyalinsa ya yi addu’a ya roƙi Allah Ya kiyaye su (Shi da matar) daga shaiɗan, kuma ya nesantar da shaiɗan daga abin da za su Haifa”.Manzo Allah (Sallallahu alaihi wassallam ) yace : “idan aka samu yin hakan kafin kusanta, Allah zai kare shi daga Shaiɗan”.
Lallai babu shakka, irin wannan ɗa an fara yi masa tarbiyya ta addini tun kafin a sami cikinsa.
Haka idan ana maganar tarbiyyar addini, lallai ne a tsaya a kan batun karutu, domin shi ne tushen tarbiyya, don haka kowace irin makarantar da yaro zai shiga, ya kamata a tabbata makaranta ce wanda ta ƙunshi koyar da karatu tare da koyar da tarbiyyar addinin Musulunci, kamar yadda Allah Ya saukar kuma ManzoSa (Sallallahu alaihi wassallam ) ya isar. Haka kuma abokin karatu yaro ko abokin hirarsa, shirarsa, shirye-shiryen talabijin da na rediyo da rikoda da na’ura mai ƙwawalwa ( computer) duka lallai ne ya yi masa jagora don ya yi amfani da abin da zai haɓaka tarbiyyars  ba wanda zai rusa ta ba. Idan aka yi wa mutum haka babu shakka an taimake shi, domin zai iya cin jarrabawarsa cikin sauƙi. Kuma zai gagari abokan gabarsa (shaiɗan da ruɗin duniya da son zuciya).

Domin karanta cikakken bayani a kan Yanayi Mai Tsafta danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Yake Son sa. wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceNasiha Tsakanin Musulmi
Labarin na GabaHarsashin Gina Al’umma (Iyaye)
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.