Fifita Sila Da Sanadin Faruwar Abu Fiye Da Hukuncin Allah Da Ƙaddararsa

0
847

Dalili daga Alƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) sun tabbatar da cewa: “Tun kafin halittar bawa, Allah ya ƙaddara yadda bawa zai kasance da duk abubuwan da zai yi, in ya zo duniya.

Sannan kuma wasu dalilan daga dai Alƙur’ani da hadisan Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) sun fayyace, kowanne bawa akwai sanadi da silar dake zamar masa tsanin takawa don cimma abin da aka ƙaddara masa.
A kan haka, riƙo da ƙaddara kaɗai da yin watsi da silar faruwar abu ɓata ne, kamar yadda jifa da ƙaddara da riƙo da silar faruwar abu kaɗai yake ɓata.
Bayan haka, wajibi ne mu san cewa, abin da Allah ya ƙaddara faruwarsa ko babu sila zai faru, amma kuma faruwar sila da sanadin afkuwar abu ba sa tilasta afkuwar abu.
Bisa ga misali, shiga cikin wuta sanadin ƙonewa ne, amma kuma mutanen Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) da suka jefa shi cikin wuta bai ƙone ba, duk da cewa sanadin ƙonewar ya faru sannan kuma ya kuɓuta daga ƙonewa saboda ƙubutar Allah ya ƙaddara masa duk da cewa sanadin kuɓutar (wato rashin faɗawa wuta) bai faru ba.
An karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da su daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ka sani haƙiƙa, da duk al’umma za su taru a kan su amfane ka da wani abu ba  za su iya amfanar ka ba; sai da abin da Allah ya rubuta maka (amfanuwa da shi). Kuma da, za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su iya cutar da kai ba, sai da abin da Allah ya rubuta maka cutuwa da shi ….
Imamut Tirmizi ne ya rawaito shi.

Ina masu cewa, ba don wane ba, da wane bai zama gwamna ba, ba don wane ba da wane bai zama ɗan majalisa ba, ba don wane ba da wane bai zama ciyaman ba. Haba ‘yan’uwa! siyasa fa ba hauka ba ce, mai yasa za a riƙa mantawa da ƙaddarar Allah da ikonsa na bayar da mulki ga wanda ya so da karɓe shi daga hannun wanda ya so, don haka muyi hattara. Ina kuma jagororin jam’iyyun siyasa masu aibata masu mulki a hannu, suna cinna musu wawayen mutane don sun ƙi aiki da wasu daga cikin tsare-tsaren da suka gabatar musu da su, in ban da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), babu wanda ba a mayar masa wasu daga cikin maganganunsa da tsare-tsarensa . to tunda haka ne kuwa mai yai zafi za su rinƙa kiran masu mulki da ƙauyawan ‘yan siyasa; don kawai sun ƙi karbar wasu daga cikin ƙudurorinsu da tsare-tsarensu; kenan watsi za a yi da maslahar sauran waɗanda ake mulka, don kada su su ce an yi musu butulci a matsayinsu na jagororin silar samun mulki?.
Shin wai zamantowarsu jagororin silar samun mulki shi ya fi tabbatar da samun mulkin ko kuwa ƙaddara da karfin ikon Allah ne ya fi? Ya ‘yan’uwa musulmai, mu yi hattara, mu nutsu mu san mai muke yi.
Ba daidai ba ne hauma-haumar siyasa ta sa mu ɓarar da imaninmu, mu tuna fa akwai lahira gabanmu, kuma ai mu musulmai, mun tabbata lahira ta fi duniya.  ‘yan’uwa musulmai, mu kiyayi yi wa kanmu sakiyar da ba ruwa.

Domin karanta cikakken dayani a kan Zirga – Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga  littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasa Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceMunafuntar Al’umma Da Rashin Fayyace Alƙibla
Labarin na GabaZirga-Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya