Mai Huɗuba:
Sheikh Dr Saleh Usama Bn Abdullahi Alkhayyaɗ
Mai Fassara:
Dr Usman Muhammad Ahmad (Azzuhri)
Shugaban Sashi
Dr Abdurrahman Muhammad Sani YYakubu
Huɗubar Juma’a ta Masallaci Mai Alfarma 3/7/1446H
Dr. Usama bin Abdullahi Khayyaɗ
(Kiyaye Rassa Tare Da Tozarta Asali)
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya yi wa bayinSa ni’ima da Musulunci, ina gode masa tsarki ya tabbata a gare Shi, idanuwa ba sa riskar Sa kuma hankula ba sa kewaye Shi da fahimta.
Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Mai cikakken sarauta da tsarkaka da aminci. Kuma ina shaidawa lallai Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammadu Bawan Allah ne kuma ManzonSa, Ya bayyana wa al’umma asalin wannan Addini da rassansa, da manyan ginshiƙansa.
Ya Allah Ka yi daɗin tsira da aminci ga BawanKa kuma ManzonKa Muhammadu, da Alayensa da Sahabbansa manyan jagorori masu taƙawa da nagarta, da waɗanda suka bi bayansu da kyatatawa muddin darare da yini na bibiyan juna.
Bayan haka:
Ya ku bayin Allah!
Ku ji tsoron Allah, saboda tsoron Allah shi ne tafarkin ankararrun mutane, kuma hanyar ma’abota hankali, sannan kuma gwadaben ma’abota basira. Cikinsa akwai aminci daga faɗawa kuskure, da rabauta da Aljanna, da kuɓuta daga wuta, ((Kuma duk wanda ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinSa, to waɗannan su ne masu rabauta)).
Ya ku Musulmi!
A lokacin da matsaloli suke mamaya, illoli suke yaɗuwa, kuma cututtuka suke yawaita, to, hankula za su ɗimauce, zukata kuma za su rikice, fahimtu za su ruɗe, sai hakan ya nisantar da mutum daga bin miƙaƙƙiyar hanya, ya karkatar da shi daga tafarki, ya kawo ɓarna mai girma a cikin tsarin rayuwa, saboda matsaloli za su yaɗu, karkata kuma za ta bazu, ma’aunan rayuwa su lalace, lamura su babbauɗe, sai a wayi gari an fara gabatar da na baya, kuma a jinkirta na gaba, a ƙasƙantar da manya, kuma a girmama ƙasƙantattu, a kiyaye ƙananan rassa, tare da tuzarta asali.
Ya ku bayin Allah!
Lallai a duniyarmu ta yau akwai misalai mabambanta da ba za su ƙirgu ba na kiyaye rassa da tozarta ginshiƙai, sai ka ga wani cikin mutane yana ƙoƙari wajen aikata ayyuka masu kusantarwa zuwa ga Allah dare da yini, don ya samu kusanci zuwa ga Majiɓincinsa Allah da su, kuma ya samu matsayi mai girma da ni’ima dawwamammiya a wajenSa, amma kuma za ka same shi yana haɗa hakan da abin da zai ɓata masa ƙoƙarinsa da wahalarsa, da abin da zai lalata masa aikinsa da jajircewarsa, a lokacin da zai yi wa Allah shirka da waninSa, a addu’a, ko neman taimako, ko neman agaji, ko yanka, ko bakance, ko karkatar da wani abu cikin nau’ikan bauta, wanda haƙƙi ne keɓantacce ga Allah, ba ya halatta a karkatar da wani abu cikinsu ga waninSa tsarki ya tabbata a gare Shi.
A lokacin da zai je wajen wani boka ko ɗan duba ya tambaye shi kuma ya gaskata shi, da kuma lokacin da yake rataya laya ko ɗanwuri, yana riya cewa zai tunkuɗe cuta daga kansa da iyalinsa ko ‘ya’yansa, alhali kuwa Allah Maɗaukaki Ya bayyana wa bayinSa a cikin LittafinSa da fayyataccen bayani cewa: Lallai sakamakon wannan shirka shi ne lalacewar aikin mutum da rushewarsa, kuma ba zai amfani ma’abocinsa ba a Lahira, da kuma haramta masa shiga Aljanna, da kuma sanya wuta ta zama makomarsa.
Allah Maɗaukaki Ya ce: Haƙiƙa kuma an yi maka wahayi kai da waɗanda suka gabace ka cewa: “Tabbas idan ka yi shirka, to, lalle aikinka zai ɓaci, kuma tabbas za ka kasance daga cikin asararru. (Suratuz-Zumar: 65).
Bayani mai daraja wanda ba ya buƙatar wani ƙari, ya zo daga Annabi a cikin ingantaccen Hadisi game da makomar wannan lamari. Haƙiƙa Imam Ahmad ya rawaito a cikin Musnadinsa, da Hakim a cikin Mustadrak ɗinsa da isnadi ingantacce daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Duk wanda ya je wurin mai duba ko boka, kuma ya gaskata shi a kan abin da yake faɗa, to, lallai ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).
Haka kuma Imamu Ahmad ya rawaito a cikin Musnadinsa, da Al-Hakim a cikin Mustadrak ɗinsa da isnadi ingantacce daga Uƙba ɗan Amir Allah ya ƙara masa yarda, cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Duk wanda ya rataya laya, to, lallai ya yi shirka).
Daga cikin misalan kiyaye rassa da kuma tozarta ginshiƙan addini, akwai abin da za ka ga wasu daga cikin masu mayar da hankali wajen karanta AlƘur’ani da Tajwidinsa da kyautata sautinsu wajen tilawa, sannan kuma suna yin sakaci wajen kiyaye iyakokin da aka gindaya a cikinsa, kuma suna yin sakaci wajen aiki da abin da aka saukar game da su, kuma suna kau da kai daga yin tuntuntuni a cikin ma’anoninsa, da tasirantuwa da wa’azozinsa, da ɗaukar darasi daga labarai da misalai da ke cikinsa.
Haka nan, cikin mutane akwai wanda yake nisantar najasa don kada ta taɓa tufafinsa, amma ba ya kauce wa yin gulma da annamimanci da yin karya. Akwai kuma wanda yake yawaita yin sadaka, amma ba ya nisantar dukiyar haram. Haka kuma, cikin mutane akwai wanda zai tashi ya yi sallolin dare yayin da mutane ke barci, amma yana jinkirta sallar farilla a kan lokacinta.
Akwai kuma wanda yake azumtar yini, amma yana cutar da makwabtansa, yana take haƙƙoƙinsu, yana cin mutuncinsu, har maƙwabtaka da shi ya zama damuwa matsananciya, da sharri mai yawa, da bala’i mai girma a gare su. Akwai kuma wanda yake faranta wa abokan hulɗarsa da danginsa na nesa ta hanyar ƙulla alaƙoƙi masu ƙarfi da su, amma kuma sai ka ga yana munana wa iyayensa da ‘yan’uwansa, yana yanke zumunci, yana nisantar makusantansa da mutan gidansa.
A cikin mutane, akwai wanda yake sakin hannu ga talaka na nesa, amma yana barin iyalinsa cikin yunwa, suna neman taimako a hannun mutane, ko kuma yana ƙuntata musu a kan kuɗin da ya zama wajibi ya ba su, kuma ba ya kyautatawa wajen ba su abin da zai ishe su. Akwai wanda kuma yake tsare tufafinsa da abin hawansa da shimfidarsa daga datti da ƙazanta, amma ba ya kiyaye kunnuwansa da idanuwansa daga gani ko jin abin da aka haramta masa.
Haka nan, akwai wanda yake bin ƙananan lamura, amma yana yin sakaci game da manyan lamura, kuma yana bin abin da yake masa sauƙi, amma ba ya bin abin da yake da nauyi a gare shi. Ibnul Jauzi Allah Ya masa rahama ya ce: “Abubuwan da muka gani daga mutane a wannan babi, wato dangane da kiyaye ƙananan lamura da kuma tozarta manya, akwai ababen al’ajabi waɗanda za a shafe lokaci mai tsawo wajen ambatonsu”.
Ya ku bayin Allah!
Lallai babu shakka cewa tushen wannan karkacewa da asalin wannan kaucewa yana cikin barin muhimman tushe da kiyaye ƙananan rassa. Wannan kuwa ba komai ba ne face tsagwaron rinsinawa ga al’adu da kuma bin ɗabi’un gargajiya, nesa da hasken wahayi biyu wato Alƙur’ani da Sunna, kuma nesa da ƙa’idojinsu, tare da bin son zuciya ba tare da shiriya daga Allah ba, da kuma rashin ilimi game da Addinin Allah, da ƙarancin masu nasiha, da rashin tallafin masu taimako.
Ku saurara! Lallai mafita daga duk waɗannan abubuwa, ba ta samuwa sai da magani na ilimi da kuma aiki. Game da ilimi kuwa, yana nuna wa ma’abocinsa ƙa’idoji da tushe da kuma ginshiƙai da ake gina rassa a kansu, ƙananan sassa kuma su samu ginuwa daga su. Hakan yana ba shi tsararren tunani mai kyau sai ya dinga sanya abubuwa a inda suka dace, kuma ya fahimci matsayi da darajar ayyuka.
Shi kuma aiki a ɓangarensa, yana kasancewa mai inganci daidai da abin da Allah ya shar’anta, yana tafiya a bisa tafarkin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mai rabauta da samun karɓuwa a wajen Allah, tare da kaiwa ga dukkan burin da ake fata.
Haka kuma, lallai ƙin bin son zuciya da ƙoƙarin tsara al’adu da ɗabi’un gargajiya bisa dokokin shari’a yana daga cikin abin da ake fatan za a gyara wannan karkacewa da tsayar da wannan kaucewa da shi, wanda zai dawo da Musulmi zuwa ga tafarkin Addininsa madaidaici.
Allah ya amfanar da mu da shiriyar LittafinSa da Sunnar ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah mai girma da ɗaukaka a gare mu da dukkan Musulmi daga kowanne zunubi, lallai shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai.
Huɗuba ta biyu:
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mai hukunci, Mai adalci, Mai tausasawa, Mai cikakken sani. Ina gode Masa -tsarki ya tabbata a gare Shi, Shi ne Mamallakin duniya da Lahira, kuma zuwa gare Shi ne makomar ƙarshe take.
Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu BawanSa ne kuma ManzonSa, mai bishara da kuma gargaɗi, fitila mai haskakawa. Ya Allah, ka yi daɗin salati da sallama ga BawanKa kuma ManzonKa Muhammad, da Alayansa da Sahabbansa. Bayan haka:
Ya ku bayin Allah!
Lallai babbar asarar da wanda ya tsare ƙananan rassa ya bar muhimman tushe zai samu, musamman idan waɗannan tushen sun kasance Tauhidi da Imani ne, ya dace ya sanya masu hankali su ba da cikakkiyar kulawa a kan wannan al’amari, su nisanci faɗawa cikin raminsa, su kuma nisanci kowace hanya da ke kaiwa gare shi..
Ya ku bayin Allah!
Wace iriyar asara ce mafi girma fiye da lalacewar aikin mai aiki, ko rage ladansa, ko ninka laifinsa? Ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah, ahir ɗinku da barin muhimman tushe, ku san ƙimar kowane abu, ku ajiye shi a matsayinsa, al’amuranku za su daidaita, rayuwarku za ta inganta, kuma ku samu yardar Ubangijinku.
Kuma a kodayaushe, ku tuna cewa lallai Allah Ya umurce ku da salati da sallama ga Mafi alherin talikai, a inda Maɗaukakin Sarki Yake cewa, ((Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).
Ya Allah Ka yi daɗin tsira da aminci ga BawanKa kuma AnnabinKa Muhammdu, Kuma Ka ƙara yarda da Halifofinsa guda huɗu shiryayyu, Abubakar da Umar da Usman Ali, da sauran Alaye da Sahabbai da Tabi’ai, da Matansa iyayen Muminai, da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako, ka haɗa mu tare da su cikin afuwarKa da karamcinKa da kyautatawarKa ya mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmi, Ka kiyaye shingen addini, Ka taimaki bayinKa masu Tauhidi, Ka haɗa kawunan Musulmi da zukatansu, Ka daidaita sahunsu, Ka gyara Shugabanninsu, Ka haɗa kalmarsu a kan gaskiya ya Ubangijin talikai, kuma Ka sanya wannan ƙasa ta zamto mai aminci da lumana da sauran ƙasashen Musulmi.
Ya Allah Ka amintar da ƙasashenmu Ka gyara shugabanninmu da masu jagorancin mu, Ka taimaki shugabanmu Hadimin Masallatai biyu masu alfarma, Ka sanya masa nagartattun mashawarta, Ka datar da shi a kan abin da Kake so kuma Ka yarda da shi Ya Maji roko.
Ya Allah Ka datar da shi da Magajinsa ga abin da alheri ne ga Musulunci da Musulmi, da abin da yake gyara ne ga ƙasa da kuma bayinKa, ya Wanda komai zai dawo gare shi a Ranar ƙarshe.
Ya Allah Ka kare wannar ƙasa, Ka ba ta kowane irin alheri Ka tsare ta daga kowane irin sharri, da sauran ƙasashen Musulmi. Ya Allah, ka ‘yanta Masallacin Ƙudus, Ka kiyaye Musulmi a Falasdinu. Ya Allah Ka kiyaye su ta gabansu da bayansu, da damansu, da hagunsu, da kuma samansu, kuma muna neman tsarinKa kada a shammace su ta ƙarƙashinsu.
Ya Allah Ka kasance musu Mai taimako kuma Mai goyon baya, Mai ƙarfafa su kuma Mai basu nasara, Ya Allah Ka sauko wa maƙiyanKa kuma maƙiyansu da bala’i, ya Ma’abocin ɗaukaka da karamci. Ya Allah Ka inganta mana Addininmu wanda shi ne kariyar lamuranmu, Ka kyautata mana duniyarmu wacce a cikinta muke rayuwa, kuma Ka gyara mana Lahirarmu wacce zuwa gare ta za mu koma, Kuma Ka sanya rayuwa ta zama ƙari ga duk wani alheri a gare mu, Ka sanya mutuwa ta zama hutunmu daga dukkan wani sharri.
Ya Allah Ka sanya wa zukatanmu tsoranKa, Ka tsarkake su Kai ne Mafi alherin Mai tsarkakewa, Kai ne Masoyinsu kuma Majiɓincinsu. Ya Allah Ka kyautata ƙarshen lamuranmu gabaɗaya, Ka tsare mu daga kunyar duniya da azabar Lahira. Ya Allah muna neman tsarinKa daga gushewar ni’imarKa da sauyawar amincinKa, da uƙubarKa ta bazata, da kuma dukkan fushinKa.
Ya Allah, muna roƙon Ka Ka bamu ikon yin ayyuka nagartattu, da barin munanan ayyuka, da ƙaunar talakawa. Kuma Ka gafarta mana, Ka yi mana rahama, kuma idan Ka ƙaddara aukuwar wata fitina ga bayinKa, Ka karɓi rayukanmu ba tare da mun shiga cikin fitinar ba.
Ya Allah, Ka isar mana kan maƙiyanKa kuma maƙiyanmu da abin da Ka ga-dama, ya Ubangijin talikai.
Ya Allah, Ka yi maganin maƙiyanKa kuma maƙiyanmu, kuma muna neman tsarinKa daga sharrinsu. Ya Allah ka warkar da marasa lafiyanmu, Ka ji ƙan mamatanmu, kuma ka cika mana burikanmu cikin abin da Ka yarda da shi, kuma Ka sa ayyukanmu na ƙarshen su zama kyawawa.
((Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kawukammu, idan ba Ka gafarta mana kuma Ka yi mana rahama ba, to, tabbas za mu kasance cikin hasararru)).
((Ya Ubangijinmu! Ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma Lahira kuma ka tsare mu daga azabar wuta)).
Tsira da aminci su tabbata ga BawanKa kuma ManzonKa Annabi Muhammadu da Alayensa, da Sahabbansa baki ɗaya.
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.
Don karanta Tarihin Dutsen Dala danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu