Bayan abin da aka faɗa a baya, na matsalar dake tattare da wasu nau’o’in kwalliyar mata wadda ta kaucewa hanya, to akwai kuma wasu matsalolin da za a iya faɗa a dunƙule kamar haka:
(a) In tsarin kwalliyar zamani ya fi karkata ya zuwa tsiraici da mace.
(b) Haka kuma kwalliyar zamani tana jan kuɗi sosai, domin wadda ta zaƙe a cikinta za ta sami kanta a cikin ɓarnar dukiya da almubazzaranci, kuma wasu sukan fifita kashe kuɗaɗe maƙudai a kan kayan ado masu tsada, fiye da taimakawa faƙirai da mabuƙata.
(c) yana rage darajar mace, kamar dai ita wata abin sha’awa ce kawai ga maza, bayan kuma mace (kamar namiji) bayan harkar sha’awa tana da ayyuka da gudunmawa a rayuwa iri-iri idan ta martaba kanta.
Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan
(d) wasu kayan kwalliyar sukan zama isgili ga mace, maimakwan su ƙara mata kwarjini da muhimmanci, sai su mayar da ita abin abin dariya saboda wasu shafe-shafe da akan yi a leɓe da girar ido da sauransu, har canzawa mace kamanni na cikakkiyar mutum suke, wani dalili dake tabbatar da abin da na faɗa shi ne, da wuya ka ga mace mai ilmi ko mai wani matasayi na alafarma ta yi irin waccan kwalliyar, idan kuma ta yi, sai ka samu mutane duk suna raina ta.
(e) Yawaita yin amafani da kayan kwalliya na zamani sukan sanya wasu matan jin isa da fariya da girman-kai.
(f) kasancewar kullum mata suna bayyana adonsu barkatai, wannan yana illata maza ta fuskoki guda biyu:
(i) Wasu mazan sukan zama fitinannu, su faɗa cikin zinace-zinace da sauran miyagun ayyuka, kamar fyaɗe da kwartanci.
(ii) Wasu mazan kuma yawaita ganin mata barkatai cikin ado da tsiraici a koda yaushe, yana dakushe musu mazakuta, yadda ba su cika damuwa da iyalin su ba, sai da taimakawar ƙwayoyi ko kuma magugunan gargajiya, masu zaburar da sha’awa.