Daren Lailatul Ƙadari

0
393

Ana samun daren Lailatul Ƙadari ɗaiɗaikun daren goman ƙarshe; wato daren 21, 23, 25, 27 ko 29, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ku nemi daren lailatul ƙadri a wutirin goma na ƙarshe”.

Ya tabbata cewa wasu cikin sahabbai an nuna musu wannan dare a mafarki. Kamar yadda ya zo cikin hadisin da Imam Muslim ya fitar; inda suke bai wa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) labarin hakan, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce musu; “Ina ganin mafarkinku ya dace cewa bakwan ƙarshe ne; wanda zai nemi daren lailatul ƙadri, sai ya neme shi a bakwai na ƙarshe”.

Haka kuma an rawaito hadisi daga Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ku kirdadi daren lailatul ƙadri a (kwanaki) bakwai na ƙarshe”. (Bukhari 1165, Muslim 206). Bisa ire-iren waɗannan hadisan malamai suka fi ƙarfafa cewa an fi sa ran daren a daren 27.

Sannan waɗannan hadisai sun nuna cewa ba a ganin abubuwan da suka saɓa wa ɗabi’arsu; kamar yadda ake yaɗawa cewa a wannan dare ana kallon komai yana sujada, kuma ana hango Ka’aba, da dai sauran maganganu.

Alamu da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya bayyana a wannan dare, shi ne abin da ya zo cikin hadisin Muslim cewa; “Ba a zafi a ranar da ta biyo bayan daren lailatul ƙadri (bayan wayewar gari kenan)”.

Kuma Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Mun tattauna game da lailatul ƙadri, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Cikinku wa zai tuna daren da wata ya fito kamar rabin akushi?”. (Muslim 1170).

Domin karanta cikakken bayani akan Zakkar Fid-Da-Kai danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceMa’anar Azumi A Musulunci
Labarin na GabaZakkar Fid-Da-Kai