Damar Samun Ɗa Namiji Ko Ɗiya Mace Ga Ma’aurata

1
88

Ilmin kimiyya ya samar mana da wasu dabaru da ma’aurata za su yi amfani da su idan suna da zaɓi Allah ya ƙaddari su samu ɗiya ko ɗa a ɓangaren haihuwa.

Wasu iyalan za a ga Allah na ba su maza gaba ɗaya, wasu kuma mata zalla wasu kuma matan da mazan to ga wasu dabaru da ake amfani da su dan zaɓin abinda ake so a haifa idan Allah ya ƙaddari hakan kuma ana dacewa.

1- Idan Iyalan na buƙatan ɗa namiji za su himmatu yin jima’i lokacin ovulation ko immediately bayan ovulation. Sirrin shi ne Y-Chromosomes Sperm ya fi tafiya da sauri ko gudu zuwa akan X- chromosome. Don haka ya fi shi azama da bala’in gudu ya kai ga ƙwan ɗiya mace dan a samu fertilization. Don haka matuƙar iyali suka samu sa’ar haɗuwa dai-dai wannan lokacin za su iya samun ɗa namiji idan ciki ya shiga.

Dan haka magidanta ba za su yi jima’i kwanaki 4 zuwa 5  kafin ovulation ɗinsu ba don samun wannan damar. Damar kawai shi ne haɗuwa dai-dai lokacin ovulation ko kuma bayan ovulation ɗin. Don haka akwai buƙatar kowacce mace ta san yaushe ne ovulation ɗinta, me wannan kalma ke nufi don samun biyan buƙata. Allah ya ba mai rabo sa’a.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

2- Idan Iyalai kuma na bukatar ɗiya mace, damar samun wannan shi ne a himmatu yin jima’i kwanaki 3 zuwa 4 kafin ovulation sannan a keɓantu ko a dakatar da saduwa kwanaki 2 zuwa 3 bayan ovulation, Sirrin shi ne duka Y-chromosomes za su mutu ne kafin zuwan ƙwan mace saboda saurin tafiya da suke. Don Haka X-chromosomes da suke tafiya a hankali za su samu damar haɗuwa da ƙwan ɗiya mace daga ƙarshe su samu damar ƙyanƙyashen wannan ovum ɗin sai a samu ɗiya mace da iznin Allah.

3- Hanya ta gaba shi ne, Idan magidanta na buƙatar ɗa namiji akwai buƙatar maigida ya riƙa shiga sosai, ya tabbatar da lokacin da zai yi release ya shiga can ciki sosai ba gefe-gefe ba. Ya tabbatar da gabansa ya shiga can ƙarshe, wannan yana ba da damar samun ɗa namiji. Yin wannan shi zai ba da damar zuwa cikin lokaci sperm ɗin ya haɗu da Y-CHROMOSOMES don Allah ya ba shi sa’ar haɗuwa

Sannan yana da kyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

labarin da ya wuceHawan Jini Ga Mace Mai Juna Biyu
Labarin na GabaGangliyon Sist [Ƙarin Mahaɗar Ƙashi]

SHARHI ƊAYA