Ko an san dalilan da yasa girke-girkenmu ke da ƙamshi, amman ba ɗanɗano?
Shin ko an san mene ne dalilan da suke sa girke-girken iyayenmu na da ya fi namu daɗi da lafiya?
ko mun yi namu ba ya yin garɗi kamar na iyayenmu mata da suka manyanta?
Bari a ji sirrin nasu.
- Yayin da ake girki a yanzu, muna amfani da tukwanen karfe, muna rufe su da murfayensu na karfe, a maimakon mu yi amfani da faifai na kaba.
- Muna amfani da gas ko risho a maimakon murhu na gargajiya.
- Ana amfani da dukkan abubuwan da suke da alaka da Turawa, mun guji na gargajiya kwata-kwata, muna amfani da colender, maimakon madambaci(GITTERE)
- Wajen niƙa kayan girki muna amfani da blender a maimakon dutsen niƙa, mixer a maimakon turmi.
- Yanzu za a ga gidaje da yawa ba sa amfani da turmi, wai ya yi ƙauyenci kuma da jijjiga jiki, gaskiya yana da kyau mu gyara.
Domin sanin yadda ake faten shinkafa danna nan