Dabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano

0
344

Ko an san dalilan da yasa girke-girkenmu ke da ƙamshi, amman ba ɗanɗano? 

Shin ko an san mene ne dalilan da suke sa girke-girken iyayenmu na da ya fi namu daɗi da lafiya? 

ko mun yi namu ba ya yin garɗi kamar na iyayenmu mata da suka manyanta?

Bari a ji sirrin nasu. 

  1. Yayin da ake girki a yanzu, muna amfani da tukwanen karfe, muna rufe su da murfayensu na karfe, a maimakon mu yi amfani da faifai na kaba.
  2.  Muna amfani da gas ko risho a maimakon murhu na gargajiya.
  3. Ana amfani da dukkan abubuwan da suke da alaka da Turawa, mun guji na gargajiya kwata-kwata, muna amfani da colender, maimakon madambaci(GITTERE)
  4. Wajen niƙa kayan girki muna amfani da blender a maimakon dutsen niƙa, mixer a maimakon turmi.
  5. Yanzu za a ga gidaje da yawa ba sa amfani da turmi, wai ya yi ƙauyenci kuma da jijjiga jiki, gaskiya yana da kyau mu gyara.

Domin sanin yadda ake faten shinkafa danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Ɗan Sululu
Labarin na GabaDabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.