Cutar Dundumi Ko Ganin Hazo-Hazo

0
101

Cutar dundumi ɗaya ce daga cikin larurorin da kan shafi idanu, wannan larura ce ta dakushewar kaifi/ƙarfin gani, yanda mutum shi a karan kansa ke tabbatarwa da kansa yana da larurar domin ba ya buƙatar zuwa wajen likita yin gwaji kafin gano ta.

Masu wannan larurar galibi in sun zo wajen likita sukan ce likita gani na bai da kyau, idona ina jin kamar an zuba min mai a cikin sa, dususu nake ganin abubuwa ba irin tar-tar ba kamar da ba wai duhu mutum yake gani ba a a yana ganin komai fes sai dai ba tar ba, abubuwa musamman manya kamar motoci, gini, ko wani symbol duk yana ganinsu normal, amma kuma bai iya ganin rubutun jikin symbol ɗin fes-fes musamman in ƙanana ne ba za su karantu da kyau ba, zai iya ganin sun harhaɗe musamman in akwai ‘yar tazara.

Wani lokacin sukan gani da kyau idan rana ta take,to amma in yamma ta yi musamman goshin magriba duhun nan na sa ganin nasu ya yi dususu sosai har sai daren ya taho an yi sallar magariba sai kyawun ganin nasu ya ƙaru, wanda ke da wannan larurar na san zai fi fahimtar me nake bayani da kyau.

Domin karanta Amfanin Ruwa Da Lafiya Danna nan 

Jiya nasa wasu hotuna inda nake tambayar tsakanin “A” da “B” wanne ya fi fita fes? Inda dukkan masu gaskiya ba tare da son raurawar zuciya ba suka tabbar da hoton “A” ya fi “B” fita, wanda tabbas hakan ne, ai ba ka buƙatar ma yin wani tunani abu ne a fili, kai da gani ka sani.

Don haka wanda suka zaɓi “B” ba mu san meke damun idonsu ba, ƙila ko don ni na ce “B” shi yasa suka zaɓi su bar gaskiya su ma su rufta rami

Na yi wannan tambayar a jiya ne kafin kawo wannan karatun don kowa ya fahimta. Sashin ‘A’ ɗin shi ne yadda mutane masu “Normal vision” wato kaifin gani ke kallon abubuwa, yayin da shi kuma “B” ɗin tamkar haka ne masu larurar dundumi ko gani hazo-hazo (blurry vision) ke ganin abubuwa, wato ga abin a haskake sai dai ba fes ba kamar dai hotunan jiya da kuma na ƙasa jikin hoton ƙasan post ɗin nan.

Ita Wannan Larura Ta Rarrabu Zuwa Muhimman Gidaje Guda Biyu:

(1) Mai ganin hazo-hazo, dundumi-dundumi ko garara-garara daga nesa, wato “short ko near sighted” a turance,ko ince MAYOFIYA a yaren likitanci (myopia)

(2) Mai ganin hazo-hazo,dundumi-dundumi ko garara-garara daga kusa,wato “long ko far sighted” a turance,ko a ce HAIFAROFIYA a yaren likitanci (Hyperopia).

Domin karanta matsala da maganin Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

Dukkan biyun nan abu iri guda idanunsu ke nuna musu, sai dai

MAYOFIYA: Masu wannan su suna iya ganin duk abinda yake kusa da su fes wanda nisan sa da shi bai wuce taku goma ba “10 feet” yana iya karatu da rubutu normal, inda matsalarsu take kurum in suka kallo abinda ke nesa sai su ga ba ya fita sosai, ko fuskar mutum ce ba sa iya ganinsa fes sai ya matso kusa, haka ko tv suke kallo sai dai su zauna a gaba kamar dai yadda hotunan nan suka nuna. Yayin da shi kuma me.

HAIFAROFIYA: Suna iya ganin duk abinda ke nesa fes-fes kamar wata daren 14, amma kuma in abun kusa-kusa da su yake dab ba sa iya gani da kyau, wato me wannan matsalar shi abinda ke nesa kurum yake iya gani da kyau, waɗannan sun fi shan wuya wajen karatu a littafi ko sarrafa wayoyin hannu domin baƙaƙen har haɗe musu suke, ka ga mutum na ta takure ido, har idanu suke zafi.

Shi yasa galibi za ku ga malamai da medicated glass, ko manyan ‘yan boko har a riƙa farar paper ta cinye musu ido, ba a gani sai an sa glass.

Wasu za su iya ma komai ba tare da glass ba to amma zarar sun ɗau littafi to sai sun nemo shi sun saka, shi yasa wasu sai za su yi karatu suke sakawa.

Me ke Haddasa Matsalar?

(1) Wannan matsala takan bi cikin family wato ya zamto gado ce aka yi daga iyaye da kakanni, shi yasa sau tari ko da a fina-finan turawa za ku ke ganin yara ƙanana sanye da tabaran ƙara ƙarfin gani wato medicated glass, haka muma a nan ba za ku rasa ganin yara masu sanya glass ba kullum, cikin manya kuwa wannan kusan kowa ya gani, akwai ‘yan mata da Maza ‘yan ƙwalisa ma kuwa amma duk suna sanya glass ko yaushe saboda ganin su, prescription glasses ne ballantana iyayen mu dattawa ko manyan malamai.

(2) Canzawar girman ƙwayar ido wato eyeball, ta yadda ta yi girma ta kuma tsuke ta kai ga ko ido ya kallo abu wannan abin bai tsirgawa har cikin retina sai dai ya yanke dab da tsayin da ya saba tunda ƙwayar idon ce ta matsa baya, shi kuma ƙarfin yadda ido ya ɗauko abin ba zai iya ƙetare yadda ya saba ya isa can ba, shi ne abin ke yankewa ka ga dususu.

(3) Akwai yawan zama cikin ɗaki musamman inda duhu yake kwana da kwanaki babu fita a ga rana sai dai kallon screen ko yaushe, wannan ma na taɓa ido, lokacin covid da aka yi lock down da yawa sun yi progressing zuwa myopia saboda zaman cikin ɗaki 24/7, kuma shi yasa galibi a wanda suka je prison ake cewa an sasu a ɗakin duhu za ku ga wasu in sun fito suna samun matsala da ganin su.

Karanta cikakken bayani game da Saurin Inzali (Premature Ejaculation) Danna nan

(4) Shekaru, eh mana daga sanda aka ba 40yrs baya karfin gani galibi kan canza, sai dai wani canjin ya fi bayyana sosai bayan an cimma 50yrs.

(5) Cuttukan da ke bin sassan jiki wanda aka yi wasarere da su, wato hawan jini da ciwon sugar infact a yanzu galibi in patient suka zo da korafin idanu ba sa gani sosai sai dususu musamman in sun shiga rana yin gwajin sugar wajibi ne, da yawa diabetic ce ta fara lalata musu idanu sun makaro ba su sani ba. Haka ma daɗaɗɗen hawan jini da ba a shan magani da kiyaye su gishiri da magi a abinci.

(6) Sai kuma hawan jinin ido wato glakoma, da kuma cin ruwan idanu wato fafiladema.

Wannan su ne muhimman dalilai a wasu kuma ba ka iya gano dalilin kai tsaye.

Maganin Matsalar Shi ne

Abu ne mai sauƙi, ana zuwa aka auna idon mutum da ƙarfin ganin nasa shi kenan sai a yanka masa glass daidai da shi, an warware matsalar an gama, domin kar ka ɗauka duk masu sanya medicated glass iri guda ne, a a ba haka ba ne, kowa ƙarfin ganinsa daban, wani ma ba ya buƙatar glass sai zai karatu ko tuƙi.

Haka karka ɗauka me sanya glass makaho ne kurum refractive error ne in ya sanya wannan glass ɗin ya fi ka gani da kyau kai wanda ba ka sa glass din, ko tsoho kar ka kuskura ka raina sa ganin yana sa glass ka ce za kai masa wayo kar yake kallonka, sai dai kai nasara ba akan baya gani ba, a a sai akan ƙwaƙwalwarsa ba ya iya tuna abubuwa saboda tsufa.

Wanda kuma ba sa son sanya glass akwai contact lenses shima kamar glass sai an auna idon, wanda da yawa har celebrities sun fi ga contact lenses tunda shi acikin idon za a manna shikenan, har me kala da zai canza kalar idon zuwa blue ko gray duk akwai.

Domin karanta Dalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace Shiga nan 

Haka nan akwai LASER SURGERY in ba ka son sanya komai, sai dai shi yana da tsada, duk ido ɗaya yakan kai dubu ɗari shida zuwa milyan da ɗaya, shi kenan sai a gyara, sai dai kowa da yadda yake iya ganin results din, galibi an fi yi wa wanda ba su kai shekara 35 ba.

Glass dai shi ne mafi sauƙi da arha, ku dubi hoton ƙasa yadda ta cikin glass komi yake kar-kar amma ta gefe inda ba tabaran ba dususu ba ma ka iya gane wasu abubuwan.

Masu ciwon sugar da hawan jini, bayan an yi control ɗinsu wasu ganin su na dawowa ya gyaru.

Illar Ƙin Daukar Mataki Ga Masu Larurar

Idan ka sami kanka da larurar kar ka bar idanunka haka kai ta wahala kana takure su har su riƙa zafi da ƙaiƙayi, lallai kai ƙoƙari ka je ka ga likita kuma ka bi duk abinda ya ba ka zaɓi, ƙin sanya glass da cigaba da zama haka shi ke haddasa wasu hatsarurrukan a titi saboda direba ba ya gani sosai.

Haka nan a kwana a tashi za ka haɗu da strabismus wato jijiyoyin idonka za su saki saboda halin matsin da ka riƙa sa su, don za a ga ƙwayar idon mutum ta waskace abinda ake kira harar garke, ka ga ga inda mutum ke nuna ma amma in kana kallon ƙwayar indonsa inda take kallo daban, wanda matsala ce hakan, ai ba za ka so a rashin sanya glass ko contact ka zamo haka ba.

Ko kuma illa mafi muni hawan jinin ido wato Glaucoma wace za ta faru a kwana a tashi saboda matsin da ka riƙa da idon, wannan matsalar ita ke mai da mutum makaho na dindindin har abada, kuma sai an riƙa tura ma allura a cikin ido jefi-jefi tare da bincikar idon, kullum sai kasa magani, kuma kazo kasa glass ko ba ka so, don haka ba wanda muke masa fatan haka, shi yasa gara ai abinda ya dace tun farko.

Ina mai tabbatar muku kafin ma a yanka glass sai an yi gwajin glaucoma dole ne don kar a zo ko ta fara samun mutum ƙila bai zo neman glass da wuri ba, sai da ya ga ba dama, ganinsa ya ɓaci da yawa.

Domin karanta bayani akan Hyperstimulated Nervous System Danna nan 

Shi yasa wasu wanda a kai wa glass ba tare da screening me kyau ba na glaucoma daga baya kan dawo su koka cewa ganinsu ya ƙara raguwa, bisa tunanin ko glass ne amma a zahiri glaucoma gare su.

Shin Glass Na Ƙara Lalata Idanu:

Magana ta gaskiya karya ne,ba inda don kana sanya glass za’a ce ganinka na kara lalacewa, na gaya muku hawan jinin ido ake tsoratar wa ma wanda suka zauna haka. Kuma babu wasu shekaru da sai ankai za’a sa matukar kwai buƙata, wasu tun suna yan shekaru biyu haka suka taso suka ga kansu, kuma har mutuwar su wasu ahaka suke rayuwa da glass, wanka da bacci ne kurum basa yi dashi.

Kun ga glaucoma ɗin nan in kai wasa yadda ka ga ana ɗauke wutar nepa duhu ya wanzu kai tsaye haka wataran mutum zai iya neman ganinsa ya rasa, ya makance, kuma ba wata alama kafin faruwar hakan, kana iya kasancewa da ita ba ka sani ba, musamman in ka san akwai tarihin matsalolin idanu a family ɗinku ko makanta a yi hattara.

Medicated glass muddin ka je ga kwararren likitan idanu (Ophthalmologist) sai yai ma screening ma zai yanka ma daidai da ganinka. Illa iyaka tunda dai kullum ƙara girma muke, shi ma prescription ɗin glass ɗin zai dinga canzawa tunda ba natural ƙwayar idon ba ce, shi ne za ku ga a hankali a hankali wani yana canza glasses gwargwadon saurin canzawar idon. Ƙila wannan ake ganin kamar ko ganin ke canzawa.

Ku sani ba a glass ɗaya permanent galibi, duk da wasu in aka yi musu guda shi kenan har ƙarshen rayuwa, wani sai zai karatu ma yake buƙata don normal vision gare shi, kurum refractive yake fuskanta, wani na iya shekara 5 zuwa sama da glass ɗaya.

Idan kuma mutum na da halin biyan surgery kamar su PRK bayan an gwada an ga candidates ne ya cancanci aikin shi kenan.

Shin Duk Me Sanya Glass Wannan Matsalar Ce Kenan?

A a akwai sauran larurori masu jawo a sanya glass amma de kaso 95% cikin ɗari wannan matsalar ce da na tattauna

Fatan bayanin ya ankarar, ya kuma fa’idantar duk da ya yi tsayi da yawa.

Karanta cikakken bayani a kan HIV/AIDS 

labarin da ya wuceAmfanin Ruwa Da Lafiya
Labarin na GabaGyanbon Ciki Wato Ulcer Disease