Contraceptive Implants : Ana Kiranta Ashanar Fata Da Hausa Wannan Wata Hanya Ce Da Ake Dasa Wani Roba Ƙarami A Hanun Mace

0
64

Shi wannan roba zai rika fidda wani hormone da ake kira da suna progestin a cikin jini ne da zai hana mace daukan ciki,yana iya zama a jikin mace har na tsawon shekara 3,amma ana iya cire shi duk lokacin da ake bukata a asibiti. 

Ashanar fatan yana sake sinadarin Progestin a hankali,sinadarin zai sa kofar mahaifa (cervix) ta yi kauri da majinan gamsai domin hana maniyin namiji haduwa da kwan mace wannan sinadarin kuma na hana fitowar kwan mace.

Wadan Da Bai Kamata Suyi Amafani  Da Implants Ba:
  • Idan mace tana fuskantar ko fama da zubar da Jini daga farji ba tare da sanin dalilin sa ba.
  •  Idan mace tana da alamar cutar dajin nono ko kuma akwai tarihin masu cutar dajin nono a cikin zuriyar su.
  • Idan mace tana shan maganin farfadiya ko maganin TB kaman rifampicin,sabida maganin zai iya rage ingancin aikin implant.
  • Idan mace tana dauke da ciwon daskarewar jini.
  • Mata masu ciwon hanta mai tsanani.

Domin karanta cikakken bayani a kan Darasi Na Shida Game da Hukunce-Hukuncen Jinin Haila da na Biƙi danna nan.

Wasu Daga Cikin Matan Bayan An Saka Musu Implant Suna Fuskantar Wadannan Matsalolin:
  • Tashin zuciya
  • Ciwon Kai
  • Hajijiya
  • Ciwon ciki
  • Pimples 
  • Kumburin Mama
  • Fitar da ruwa a farji.
Idan Aka Ga Wadannan Alamomi Ayi Gaggawa A Koma Asibiti:
  • Rashin waikewar ko kumburi a gurin da aka saka implant din.
  • Alamar fitowar implant  daga hannu.
  • Idan ana son a cire ashanan fatar yayin da mace ta kara kiba,kada ayi gangancin cirewa a gida.
  •  Fuskantar rashin kuza’ri da koshin lafiya
  • Tunani kamar kina dauke da ciki.

Note:

Ingancen implant tana raguwa a jikin mata masu kiba da nauyin jiki,mata wanda weight nasu ya wuce 80 zuwa sama,irin wadannan mata ya dace su sake wani jadelle bayan shekaru 3 (kada a bari zuwa shekaru 5) implanon bayan shekaru 2 kada abari zuwa shekaru 3.

Domin karanta bayani akan Yin Tazarar Haihuwa Ba Tare Da Shan Ƙwayoyi Ba Danna nan

labarin da ya wuceMutane Da Yawa Sukan Yi Tambaya Akan Aa Yaya Za a Samu Hanya Mafi Sauki Ta Yin Tazarar Haihuwa Ba Tare Da Shan Ƙwayoyi Ba
Labarin na GabaWari Ko Hamanin Baki {Mouth Odour}