Ciwon ƙaba (Hernia) Da Yadda Za’a Kare Kai Daga Hernia 

0
31

Ciwon ƙaba, wani ciwo ne da ke faruwa saboda gajiyawa ko raunin jikin naman da ya rufe ciki(wato naman da yake

karkashin fatar da ta taso tun daga kahon zuci har zuwa mara),wadda kan sa tsagewar wani bangare na naman,hakan ke sa halittun jikin dan adam na ciki, kamar hanji ya fito ta wannan’yar kafar.

Abubuwan Dakan Kawo (ƙaba)

Abubuwan da ke kawo ciwon ƙaba sun kasu kashi biyu kamar haka:

1 Gado (Congenital): Ana gadon ciwon tun a ciki, sai jariri ya fito da ita ƙabar.

2 Wanda ake samu daga baya (Acquired): Wannan nau’i ne da ake kamuwa bayan an girma saboda raunin naman jiki, sanadiyar ƙiba sosai ko kuma tsananin aikin da zai wahalar da jiki kamar daukar abu mai nauyi,duk lokacin da wani bangare na naman jikin mutun ya samu gajiyawa sakamakon daukar nauyi, ko tari na tsawon lokaci, ko ma tsananin yunkuri lokacin ba haya, duk sukan sa naman ya rabu biyu, ta yadda wani sashe na ’ya’yan hanji zai biyo hanyar.

Domin karanta cikekken bayani akan Gyambon Ƙoda [Pyelonephritis] Shiga nan

Shan taba sigari ma kan sa mutun ya kamu da cutar saboda tsananin tari sanadiyyar ciwon huhu da sigari ke sa wa.

Hanyar Magance Ciwon 

Hanyar magance ciwon: Hanya mafi inganci domin kawar da ciwon kaba shi ne fida, domin a gyara wannan wuri da yake rauni. Idan kuma aka ki zuwa a yi aikin, to ciwon ba ya mutuwa da kansa sai dai ya kara girma wani lokaci kuma ya rika zafi sosai, wanda hakan barazana ce ga rayuwar mutum.

Bayan aikin fida mutum zai ji rashin walwala da dan zafi na ’yan kwanaki, kafin ya fara jin sauki,hakan kan dauki sati daya zuwa shida kafin a ji garau,amma wadanda ke daukar nauyi ko aiki mai wahala, to za su dauki tsawon lokaci kafin su warke.

Domin karanta bayani akan Cututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i Danna nan

labarin da ya wuceCututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i
Labarin na GabaBayani Mai Mahimmanci Zuwa Ga Mata Akan {Ovulation}