Ummulkhair Sani Panisau
Tukunyar Ramadan tare da ni Ummulkhair Sani.
A yau za mu ga yadda ake haɗa Chinese Rice.
ABUBUWAN BUƘATA:-
Shinkafa.
Karas.
Peas.
Albasa.
Ƙwai.
Tattasai.
Butter.
Gishiri.
YADDA AKE HAƊAWA:-
Da farko za ki fasa ƙwanki a cikin ƙaramin kwano sai ki yanka masa albasa, ki saka gishiri kaɗan ki ajiye a gefe. Sai ki kawo tattasai, albasa, karas, ki yayyanƙa ki ajiye a gefe.
Ki ɗauko karas ɗinki ki samu abu mai kyau ki zuba masa ruwan zafi da baking powder ki rufe na wasu mintuna sai ki tace. Ki kawo peas ɗin ki, ki juye a kwano sai ki zuba masa ruwa sosai sannan ki tace. Bayan nan sai ki haɗa dukkanin kayan lambunki a wuri guda ki ajiye. Za ki samu non-stick pan ɗin ki ki ɗora a kan wuta ki samu butter ɗinki ki riƙa juyawa kamar dai yadda kike miyar ƙwai. Idan ya yi sai ki ɗauko kayan lambunki ki zuba a kai kina juyawa a hakali saboda kar ya kama. Sai ki kawo dafaffiyar shinkafarki ki zuba a ciki ki yi ta juyawa har sai ta soyu sai ki juye.
Ki samu plate mai kyau ki juye a ciki. Ana ci da miya.
Danna nan don karanta Yadda Ake Garin Kunun Aya
Edita:@rumasau-kallamu