Ba Kowane Ciwon Ƙirji Ba Ne Ulcer

1
279

Mutanen mu sun lamincewa kansu cewa; duk ciwon ƙirji kurum ulcer ce, shi yasa ciwon zuciya ya aika mutane da yawa lahira ta farat ɗaya da sunan ulcer, domin ba a son zuwa asibiti ai gwaje-gwajen da suka dace, asalin uwar hanji ba ma a kirji take ba, sai dai eh mun ji ana iya jin ciwon ƙirji sanadiyyar refer pain amma ba dole ulcer ba ko yaushe. 

Shi fa gwajin nan ba ka da buƙatar sai likita yace ma ga shi yi kaza. A ah in ka ga bai da niyyar ba ka matuƙar da hali roƙa za kai ka ce kana so ya ba ka gwaji iri kaza kayo don kurum ka ƙara sanin matsayin ka.

Ciwon ƙirji abin tsoro ne musamman in mutum na da hawan jini, matsalar zuciya, ballantana wasu sun gado matsalar da ba su san suna da ita ba a family, haka wasu suna da matsalolin hawan jini amma ba su sani ba, gani suke ciwo kaza sai a tsoffi ko masu aure, wa ya gaya ma haka? 

Idan kuna so ku karanta Bayani A kan Gyambon Baki {Canker Sore} Danna nan

Sai dai ina! Duk maimakon haka kun gwammace zama ku yi ta ɗibar maganin ulcer har sai ya kai ga fara sa ku gudawa, ga shi fa saboda wauta ana jin ana shan maganin amma ba canji, kuma ko da an ji relief zai dawo, amma mutum ya share duwawu ya zauna, ulcer ɗin nan fa ana warke ta. 

Ya kamata mu sani duniya ta wuce wannan zamanin, in dai ka iya neman kuɗi, toh dole kuma ka koyi neman lafiya tare da tattalin ta, dole ne kai wa rashin lafiya tanadi tun kan ta zo. 

A yanzu dai ba ka da buƙatar sai ka ji ciwo sannan ka je asibiti, masu dabara duk shekara sukan je sau 1 su nemi a ba su mahimman gwaji da suka dace da masu shekaru irin nasu saboda in ma jikin su ya fara shiga wani lokon to ai ƙoƙarin tsamo shi.

Domin karanta bayani a kan Samiha-Borin Jini {Hives,Urticaria,Neetle Rash} Danna nan

labarin da ya wuceLarurar Sarƙiwar Numfashi Da Ake Kira (Asthma)
Labarin na GabaSanƙaran Nono Wato {Breast Cancer}

SHARHI ƊAYA